Sashe 67
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aka kafa gidan nan shekaru da dama da suka wuce muke ayyukanmu cikin sirri bamu ta a samun wanda ya shigo gidan nan ba sai dai idan mu ne muka shigo da mutum amma ga shi Yau ka karya mana wannan tarihi ka shigo cikin gidan nan ba wani tsoro ko tashin hankali har ka yi fito-na-fito da mu. Ina maka albishir da cewa idan ta amarka hatsabibi to muma iyayen hatsabiban ne ko ma ince Kakansa. Shawarar da zan baka shi ne ka mi a wuya kawai, daman a Yau ne za mu ba Dodo kyautar jinin tagwaye tabbas zai murna ya samu da naka jinin ko shakka babu sai mun samu alheri mai gwa i daga albarkar dodo." Barista Alawiyya ta nufi ramin gadan-gadan ba tare da wani tsoro ko fargaba ba, domin ta yadda Ubangiji ba zai ta a basu dama kanta ba, balle su samu nasara kanta ba. Sai ga shi tana shiga gun ya koma ba komai ramin ya ace wajen ya koma yadda yake. Sai ga wasu irin attin maza sun fito daga wani aki auke da muggan makamai sun durfafi inda take tsaye. Gyara tsayuwa tai ta ja tunga tana jiran zuwan nasu, cike da jarumta da aukar wa rai. Nan da nan wajen ya kacame da fa an gaske tamkar a filin ya i amma abin mamaki su duka an kasa samun wanda ko sau aya ya ta a jikin Alawiyya da makamin hannunsa. Ita kam duk ta ji masu rauni babu wanda jini bai fita daga jikinsa ba. Kafin kace me? Alawiyya ta zubar da su tas, ta ja tunga tana are wa mutanen kallo, zuwa yanzu ranta baki aya a ace yake domin ta agara ta gama da su ta nemo inda yaran suke don bata ga alamar su a gidan ba. Ganin haka yasa wasu da dama su ka ace at! Sai ga shi an bar su Hajiya Turai kawai, suka dubi Alawiyya cikin tafasar zuciya suka kece da dariya lokaci guda, sai kuma suka ha e rai. Hajiya Turai ta dubi Alawiyya tace cikin aga murya, "Nasan ko baki gaya mana ba,kece Alawiyya ko ince Barista dake kare Fatima, to ina so ki sani babu wanda muka ta a raya za mu yi wani abu da shi muka fasa, don haka dole ne rayuwar Mahaifiyarki data annenki ta salwanta kamar yadda mu ma muka ha ura da rayuwar mijinmu data yaranmu da muka ba dodon tsafi ya cinye. Bari na baki wani labari wanda nasan ba dole bane idan Uwar taki ta baki shi ba, mu ne nan muka kashe Alhaji! Haka mu ne nan muka salwantar wa uwarki da idanunta muka asirce su yadda ba zata sake gani ba har sai ranar da dodon tsafinmu ya halaka, abin tausayi abin dariya shi ne ba zai ta a halaka ba duk don shekaru ari masu zuwa, domin muma a haka muka shigo ungiyar muka ganshi kuma har gobe yana a yadda yake. Sannan idan ta amarki kice za ki maka mu a shari'arki kan wannan harka ta tsafi to ruwa kike domin akwai manya-manyan usoshin gwamnati dake cikin wannan harka dumu-dumu." Ta dubi Hajiya Tani tai mata inkiya sai kuwa ita ma tace, "Yarinya ina so ki sani annenki na cikin gidan nan amma a inda baki isa ki je gun ba, domin suna akin dodo wanda ko mu da kike gani ba duka bane kowa ya ta a shiga akin ba, nasan zuwa yanzu sun riga da sun zama gawa annenki don haka ki shirya binsu domin labarin zuwanki ya iske dodo ko shakka babu yana tafe gunki. Da wannan muke maki ta'aziyya domin dai ba za ki sake ganinmu ba duk inda za ki bincika mun riga mun maki nisan da ba za ki iya kamo mu ba. Ku ki ri e a ranki za ki sha mamaki a kotu domin mun yi kyakkyawan tanadi a can ma wanda muka tura mutanen mu don tabbatar da cewa an yanke ma Fatima hukuncin kisa kamar yadda muke bu ata a bainar nasi." Kawai gani tai sun ace su ma ba kowa gun sai attin data kwantar asa ke ta nishi. KOTU Kotu ta cika ta batse, da mutane kowa son ganin matar data kashe mijinta yake, miji kuma babbar Soja kamar Captain Aliyu Masani wanda yanzu ya jima da yin ritaya, ya amshi manyan ayyuka sosai ya ji da su, gwamnati na matu ar ji da shi, amma matarsa ta kashe shi. Al ali ya shigo, don haka kowa ya nabba'a ya natsu ya yi shiru tamkar ba mutane sai arar fanka da takardun da baristoci ke bu ewa kawai ake ji. Magatakarda ya tashi ya fara karanto shari'ar da za a fara. Magatakarda, "Kotu na bu atar a matso da Fatima Aliyu Masani." Sai ga Fatima wasu matan an sanda sun rako ta, sun kai ta har inda zata tsaya. Magatakarda, "Kotu na tuhumar Fatima da kashe mijinta marigayi Captain Aliyu Masani ta hanyar yanka ma shi wuya da caccaka mai wu a a cikinsa." ali, "Malama Fatima kin ji abin da kotu ke tuhumar ki da aikatawa na kashe mijinki ta hanyar yanka wuyansa da caka mai wu a a cikinsa." Fatima ta fashe da kuka ta sadda kanta asa ta kasa furta ko da kalma guda. Mutane duk suka zuba mata ido, wasu tausayinta suke yayin da wasu ke mata kallon munafuka kawai, ta kashe mijinta tana kukan munafurci. ali ya sake maimaita tambayarsa amma Fatima ban da kuka babu abin da take yi, don haka Al ali ya bu aci da lauyan wadda ake tuhuma ya fito tare da Lauyan mai ara. Sai dai abin mamaki Lauyan mai ara ne kawai ya fito,babu Lauyan wadda ake tuhuma. Sai kotu ta hartsine da magana, kowa da abin da yake cewa, sai da Al ali ya yi tsawatar sannan akai shiru. ali ya gama rubuce-rubucensa ya ce, "Kotu ta ba, Fatima kwana biyu ta bayyana gaskiyar lamari tunda bata da Lauya... "Assalamu alaikum, a gafarce ni ya mai girma Al ali. Ha a Fatima na da Lauya har guda biyu, ko don ko da aiki ya yi wa guda yawa insha Allah za a samu guda kamar dai yanzu. Ina ara neman afuwar Al ali saboda rashin zuwana da wuri, hakan ya faru ne saboda doguwar tafiyar da nayo. Sunana Barista Hawwa'u Bello Dawa, Ni ce Lauyar dake kare wadda ake tuhuma watau Fatima Aliyu Masani." Sai kallo ya koma sama, Shaho ya auki Giwa! Mustapha mamaki kamar ya kashe shi, wai dama Jiddah Lauya ce? Dama tana aikin Lauya bai sani ba? To yaushe ta fara aikin bai da masaniya! ali ya yi murmushi domin jawabin Lauyar ya birge shi, tabbas tasan aikinta ga alama, don haka ya amshi uzurinta ya ce a fara Shari'a. Barista Jiddah ta arasa gaban Maman Alawiyya tace, "Kotu na bu atar jin sunanki tare da jin ka an daga ala ar ki da mijinki." Fatima, "Kuka kawai take har zuwa yanzu bata furta ko da kalma guda ba, sai dai a cikin zuciyarta tana tambayar kanta ina Alawiyya take? Wacece wannan to? Kar dai ace Jiddah ce ta Iyami? Sosai take son yin magana amma bakinta ya kasa furta ko da kalma guda. Lauyan mai ara ya tashi ya ce, "Ina son kotu taban damar tambayar mai laifi ba mamaki nadamar abin da ta aikata ne yasa ta kuka har ta kasa magana." Barista Jiddah, "Ya mai girma mai Shari'a ina son kotu ta tsawatar wa da Lauyan mai tuhuma domin yana razana wadda ake zargi ta hanyar jingina mata laifin da babu tabbacin ta aikata shi, hakan kuwa bai kamata ba ya mai girma mai Shari'a." ali, "Kotu ta kar i uzurinki, Lauyan mai ara ka gyara kalaminka." Barista Jiddah, "Na gode sosai Ya mai girma mai Shari'a." Lauyan mai ara, "Fatima ina son ki gaya min auren dole ki kai da magariyi mijinki shi yasa kika kashe shi, ko ko saboda ku i ki ka kashe shi?" Fatima, "Kuka kawai take fiye dana farko, domin ta lura bakinta ba zai ta a furta ko da kalma guda ba. Barista Jiddah, "Cike da sanin daraja da kimar wannan kotu nake son ta aga wannan zama zuwa gaba, domin bincikar lafiyar wadda ake zargi." ali, "Kotu ta amince, ta age zaman sai zuwa 25/8/2022." Magatakarda ya sake karanta arar gaba. Jiddah ta nufi office in da ta shiga ta amso aron kayan Lauya gun wata ar classmate in ta da su kai karatu tare. Tana mata godiya kenan Mustapha ya shigo har zuwa yanzu akwai umbin mamaki akan fuskarsa. "Dama ke Lauya ce Jiddah?" Cewarsa yana kallonta. Murmushi tai, "Tabbas haka ne sai dai Ni Lauya ce mai zaman kanta wadda bata ta aukar aikin da zuciyar zata iya ba, saboda rashin katangu guda biyu dana rasa, amma Yau ina zuwa nan sai naji Ni a cikakkiyar Lauya mai ji da kanta ta kowane fanni. Sannan zan bi kowace hanya don ganin na ci nasara akan wannan shari'ar ko da Alawiyya bata bayyana ba, tabbas sai na binciko gaskiyar lamarin nan." Sai a lokacin ya samu natsuwa, har yake hango tarin nasara a gabanta ya ara ji a ransa cewa tabbas ita ce cikar burinsa. To masu karatu kun ji dai ana wata ga wata. Taku a kullum Haupha [9/7, 11:05 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa