Sashe 101
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ga ko Prince ya kira ta ko ya turo mata sa Ilai kuwa kira goma sha biyar na shi sai kira biyu na Alawiyya sai kira aya na Mama kira biyu na Maryam awarta ta Kano ma wabciyar Prince ko tace awa ga matar Prince. Tai mamakin kiran Maryam don sun jima ba su yi waya ba, amma sai ta fara kiran Prince don kiransa duk yafi na sauran yawa. Yana auka kamar ya fashe da kuka ya ce, "Haba Princess don Allah ki dinga jin tausayina mana, don Allah ki daina azabtar da Ni haka nan wallahi ji nake tamkar na mutu idan na kira ki baki auka ba sai na ji tamkar wani ne ya zo ki ka je kika manta da Ni." Murmushi tai, don ta saba yanzu duk lokacin da wani ya kira ta a waya ko ya tsaida ta ya yi mata maganar yana sonta sai Prince ya yi mata orafi ya ce mata ya ji alamar wani na sonta. Don haka sai ta share tace mai, "No Prince wallahi ba haka bane ba, ina can gun Alawiyya zata tafi gida,muna bankwana shi ne fa sai yanzu suka tafi na dawo cikin gida na shigo aki na iske miss call in." Tana jin ajiyar zuciyarsa alamar ya samu kwanciyar hankali jin kalamanta, don haka sai ya ce, "Kwantar da Ni kawai za ki yi Princess ai nasan daman ba za ki ta a bari na kama ki da laifi ba, amma ke kin iya kama mutane da laifi." Cikin dariyar samun nasara kanshi tace, "Amma dai Prince kasan cewa kafin na kwantar da kai, ai kai ka jima da halakar da Ni ko?" Shima cikin shagwa ar ya ce, "Princess shike nan naji amma dai ki sani nafi ki kulawa da aunar nan tamu, don nasan da za a fiddo su duka a auna to tabbas tawa sai ta fi taki yawa nesa ba kusa ba." Har tana diddira afa gun magana alamar shagwa ar tai nisa tace, "Ni... Ni... Ni...ba zan yadda da wannan maganar ba, ta ya ma za ai kace wai ka fini bayan ko da yaushe nice mai magana kan baka min waya akan lokaci baka turamin sa o a kan lokaci to shi ne za ka ce wani taka ta tafi tawa yawa?" Cike da nisha i yake sauraren muryarta ji yake tamkar ya fito da ita daga wayar tsabar son ganinta da yake, muryarta na saukar ma shi da kasala jin barcin nisha i yake duk lokacin da take mai irin wannan shagwa Anya kuwa akwai mazan da su kai dacen da ya yi ma samun mata kamar Jiddah? Gata da natsuwa gata da hankali sannan tasan abin da take, mafi yawan lokuta ita ke ba shi shawara idan wani abu ya faru haka zalika tana matu ar son cigabansa ko da yaushe tunaninta idan kai kaza kai kaza Prince za a aru don Allah ka jaraba yi man. Duk acin ran da yake fuskanta mantawa yake yanzu daya tuna da yana da yana da Jiddah sai ya ji komai za ai mai ba komai ya manta ma sam. Haka yanzu ya kawo idanu ya zubama matansa duk abin da suke bai tanka masu ko kallo basu ishe shi ba, shi dai yasan yana fita duk wani ha insu don haka duk abin da suke yanzu bai ata mai rai, ko ranshi ya aci ma yana kiranta a waya sai ta saka shi cikin farin ciki don haka shi yanzu ta auren su kawai yake bata haukan da suke zuba mai ba a cikin gida. Duk yana sane da yadda suke zuwa suna mai arya gun mutane suna zubar mai da mutunci duk yana sane amma yasan dai cewa Allah shi ne shaida kan abin da ke faruwa a gidansa don haka duk masu zaginsa da masu cewa bai ri on aure duk ya barsu da Allah , saboda shi ne kawai wanda zai saka mai kan ananan maganganun da ake binshi da su, duk da yasan hada laifin matan nasa amma ai mutane ya kamata su yi mai adalci su dinga tunawa da cewa duk macen da take zaune gidan mijinta kuma tana i irarin yana zaluntar ta arya take tunda ba aure ta ya yi ba, haka zalika ai babu yadda za ai ace namiji ne kawai mai laifi ban da mace a zaman aure. Jin ya tafi duniyar tunanin da tasan ba makawa na iyalanshi ne yasa ta sauya firar zuwa ta tsokana tace, "Yawwa Prince ba jiya kaban labarin yarinyar da tace tana sonka ba? To har zuwa yanzu ban gama tsinewa idanunta albarka ba da suka hango mata kai, don da ace zan ganta ba shakka sai naji dalilin da yasa take sonka ana zaman lafiya kawai." Magana take ba alamar wasa da jin muryar yasan bata fara'a take maganar sai ya ji ya ru e baki aya don haka ya sake gyara kwanciyarsa bai damu da Hafsat dake tsaye kansa ba tana ta jan tsaki ba, tana cewa wane dare ne Jemage bai gani ba." Cikin lallashinta ya ce, "Princess don Allah ki manta da wancan shirmen yarinyar na rantse maki da Allah ban bari ma an jima ba a nan gun nace mata ta nemi daidai da ita ba bai niba." Ta wani zaburo cikin wayar tace, "Na shiga uku ni Jiddah an fasa aurena ! Yanzu don Allah har wannan muryar taka sai da taji bayan ta gama kallemin kai sai kuma ka bata tukuicin muryarka?" Sai ta fashe da kukan shagwa Zaune ya tashi a ru e yana cewa, "Dakata Princess, dakata, kin san dai ba zan maki arya ba ko? To billahizzali ban yi mata magana cikin sakin fuska ba, to wai Ni da nake da kamar ki ke zan da wata mace kuma Princess?" Ai sai Hafsat ta ora hannu bisa kai, kome ta tuna kuma sai ta sauke hannun daga kanta ta fice tana maganar da ba shakka yasan zagin Jiddah take bai mamaki ma idan har da shi ta ha a ta zagen. Jin abin da ya ce yasa Jiddah fashewa da dariyar farin ciki, sai shima ya samu kansa da sakin dariyar ya ce, "Oh ! Watau har kin ji da i nace ban gane mata idan ba ke na gani ba ko?" Cike da farin ciki tace, "Sosai kuwa don tsabar da i har ora afa aya nayi kan aya ma yanzu haka Prince." yale da dariyar jin da in abin da tace ya ce cikin zolaya, "Yanzu nan ke murna kike ba ce wa za ki min ba, a'a Prince ai duk aya ne Ni da su ba komai ka yi yadda kaga dama kai da kowa ce ma." Yana jin ta sauke wani gauron numfashi sannan tace, "Nabi su da gudu su duka matan da kake magana kan su to." Ko bai tambaya ba yasan harara take yayin da take maganar don yasan halin an kayansa tsab. "Ki ka bisu da gudu har ina kenan Princess?" Cike da takaici tace mai, "Na bisu da gudu har ofar gidanka nace." Ya ce "A'uzubillahi ya za ki ainufin biyo matan mutane da gudu ainufin har ofar gidana Princess?" Sai kawai ta kama cewa, "Hello. Hello. Hello." Wai ita bata ma jin me yake cewa. Dariya yake har yana ri e cikinsa, Princess da kishi sai addu'a kawai, ita duk wata araka bata sonta indai ta shafe shi. Tana jin shi yana dariya abin da take so kenan don haka ita ma sai ta cigaba da taya shi dariyar su duka suka shiga yin dariyar. Wannan na aya daga abin da yasa duk yadda ranshi yake a ace yake saurin kiranta domin yasan ba su gama wayar ba tare da tasa shi ya manta acin ranshi ba ya ji shi a cikin farin ciki ba kamar dai yanzu. an saurara da dariyar tace mai, "Prince azun muke magana da Alawiyya zamu shiga wani zubin adashe duk wata dubu ari me zai hana kaima ka shiga cikin adashen nasan ku in sun yi maka rana?" Ya daina dariyar shima jin tai magana mai ma'ana ya ce, "Kuma kinga wallahi dana ji da in hakan amma fa sai idan ta arshe za a ban saboda ban san aukar wuri." Baka da matsala sai Ni da kai mu zama na biyun arshe da arshe kenan." Sun jima suna wayar wadda daman haka take duk lokacin da za su yi waya sai su annata katin dubu biyar ba tare da sun ankara ba. Sai da katin ya are su kai bankwana mai tsayawa kowa a rai a tsakaninsu watau ya ce mata, "Sai anjima love you." Ya ja kalmar You in sosai itama sai tace mai, "Love You too. Sai sui ma juna kiss kowa ya kashe kiran, yabi wayar da kallon farin ciki. Sai tana cikin yanayin farin cikin ne taga sa onshi kamar haka. "Princess nace wai da ace babu waya ya za mu samu kanmu a ciki kenan? Ni dai ko awa nayi ban ji muryarki ba zaucewa nake na shiga cikin tararrabin rayuwa ke fa?" Tai murmushi bayan ta gama karantawa ta maida mai da amsar. "Prince don Allah daina jawo mana abin da ba alheri bane, kasan Allah? Duk wani motsi nawa sai na kunna recording in wayarmu na saurari muryarka naji da i, haka zalika duk lokacin da sakan zai buga ban jin da i idan ba tare da kiran wayarka ya buga ba. Prince kai in na asalin daban ne a rayuwata, addu'a nake dai na ga ranar da zan wamushe ka a kirani da matarka a kira ka da mijina." Sai da ya harba afa don farin cikin amsar data ba shi, don haka ya maida mata da amsar. "A ranar za a ga yadda za mu dinga shiga muna fita cikin shigar alfarma tare da nuna tsantsar godiya ga Allah ta hanyar bu e duk wasu ofofin alheri dake manne da mu Princess. Allah ban san ya zan kasance ba, amma dai nasan idan acan Jalingo za a aura maki aure to zan bi ki ne tun ranar da za ki tafi har a aura auren mu taho tare, saboda ba zan iya nesa dake ba, sai dai aurin auren