← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 133

Sashe 82

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 38 Daddy ya nisa ya kalle su duka ya ce, "Lokacin da na tabbatar da cewar Iyami ta sace min yarinya ta gudu da ita, sai najS tsani dangina na tsani ahalina tsanar gasken-gaske. Hakan yasa na tattara kayana baki aya cikin dare na rubuta takarda na ajiye ma Yayana da mu ka je Lagos tare a lokacin. Ban ji ina son sake rayuwa da kowa ba sai da iyata Alawiyya don haka na tafi tashar mota kai tsaye na shiga motar Bauchi, ko a cikin motar ban da hawaye da takaici babu abin da nake yi, ace wai danginka sun yi maka tsakani da iyalinka? Wannan wace irin rayuwa ce mai wahalar gaske da babu imani babu tausayi balle zumunci? Haka na saka kaina cikin cinya na kama matse hawayen ba in ciki. Har muka isa Bauchi ban daina kukan ba in ciki ba, haka kowa ya sauka ya kama gabansa aka barni zaune ina tunanin ta ina zan fara? Ga shi ba ku i gare Ni sosai ba, balle na samu gidan haya ko shago na bincika na kama. A tasha na zauna tsawon lokaci sai ga wani dattijo ya yi min sallama, bayan mun gaisa ya ce min, "Yaro ba o ne kai ko?" Na girgiza mai kai alamar e, na kuma bu e bakina na gaya mai cewa, "Daga Lagos nake ina neman yarinyata da wata mata mai saida abinci inyamura mai suna Iyami ta gudo da ita, to matsalar ban san a wane gari take ba, na dai za i zuwa nan ne don raina ya ban zan iya ganinta." Mutumin ya kalle Ni ya nisa sosai ya ce, "To Yaro lamarinka akwai ban tausayi ka rasa yarinyarka kuma kana da tabbacin tana da rai kuma a hannun wadda babu hasken musulunci a tare da ita tabbas akwai matsala mai tare da tashin hankali. Don haka zan taimaka maka na kai ka gidana a kwai shago sai ka zauna a ciki har Allah Ya yi nashi ikon. Sai ka zauna a nan Insha Allah zaka dace indai kana raye tana raye to tabbas zaku ha u wata rana." Wannan bawan Allah shi ne ya auke Ni ya kaini gidanshi ya ajiye Ni shagon gidan na ajiye kayana. Kasancewar ba wasu ku i a hannuna kuma ina don in fara sana'a ko da ba wata babba bace ba, kuma maigidan ya auke min nauyin abin da zan ci insha yasa na nemi yaban shawarar sana'ar da zan fara yi a garin. Muka zauna muka tattauna yaban shawarar na fara saida kayan gwanjo. Ba a auki lokaci ba kuwa na fara saro kayan gwanjo ina kaiwa kasuwa abu kamar wasa sai ga kasuwar gwanjo ta amshe ni sosai har ta kai ko ba ranar kasuwa ba ina ajiye kayana a ofar shagona ina ciniki sosai kuma. Haka Allah Ya aukaka Ni sosai a kan sana'ata . Malam Lado shi ne mutumin da ya sauke Ni a gidansa, yana da mata guda da yara manya duk sun yi aure wasu maza wasu mata, akwai mata guda biyu dake zawarci a gidan da Safiya da Asma'u, Ni dai iyaka ta da su gaisuwa, sai idan sun ga kayan da suke so, su yi min magana Ni kuma zan ba su ba tare da na amshi ku in su ba, saboda mahaifinsu ya gama min komai tunda ya ban wajen zama yake ci da Ni kuma. Sai dai duk da haka Ni ma ranar kasuwa nakan yo cefane mai kyau na aika cikin gidan da su. Ashe wai Safiya da Asma'u suna ta cacar bakin kowace sona take aure na za ta yi, Ni kuma babu wadda na ta a nuna ina so ko da wasa a cikinsu, to Ni wace soyayya ko aure zan bayan an raba Ni da macen warai macen kirki Fatima? Sannan ga tunanin iyata Alawiyya da kowace rana da shi nake kwana da shi nake tashi? Hakan yasa ko da na fara jiyo amshin maganar sai na sake kame kaina sosai ban sakar masu fuska ko fitowa su kai ba ruwana da su, ba ko da yaushe nake amsar gaisuwar su ba. Haka rayuwa tai ta juyawa a Bauchi ban da wata matsala sai ta abin da ya fito da Ni daga gida. Ranar wata Laraba tun da safe na jiyo makoki daga cikin gidan Malam Lado, ina shiga na samu labarin rasuwar shi da asubar fari. Nayi matu ar ba in ciki sosai naji babu da i, haka akai zaman makoki har na kwana bakwai, sai na fara ha a kayana da zummar barin garin na koma wata Jahar ko Allah Ya ci da Ni da ganin Alawiyya. Sai dai lokacin da na shiga gidan don nayi masu bankwana suka fasa kuka suka ce don Allah kar da nayi masu haka, Ni suke gani suna ebe kewar maigidan don Allah na cigaba da zamana inda nake har mai rabawa ta raba. Ba don na amince da cewar zan rayu da su har mutuwa ba na amince na fasa tafiya sai don kar su ji babu da i a lokacin yasa na ajiye a raina zan ara zaman shekara guda sai ka ara gaba abina neman Alawiyya. Bayan wata uku da mutuwar Malam Lado wata rana da dare arayi suka zo shagona suka kwashe min komai su ka sassare Ni sosai sukai tafiyarsu. To a nan fa na fara gane da suwa nake zaune. Domin kwata-kwata aka daina ban abinci daga gidan aka daina min duk wani abu na kyautatawa da aka saba yi min a gidan. arshe ma sai suka kira Ni suka ce idan ina son zama a shagon to na fara biyan ku in hayar shagon. Nayi matu ar mamaki sosai kan yadda lamarina da matan gidan ya juye, saboda ba wata mu'amala ta kirki dake wanzuwa a tsakaninmu da su sai gori da habaicin da suke fitowa ofar gidan suna sakarmin wai na zauna ba kunya ba tsoro ina cin abincin marayu ina zaune gidan marayu ban iya ta uka abin sisi a cikin gidan. Ni kuma ga Ni kwance sai jinyar raunuka nake dake jikina haka nake kwana na wuni ban ci komai ba sai fa idan wani ya zo ganina cikin abokan sana'ata ya ban wani abu nake amfani da su nake siyen abinci nake siyen magani. Haka na samu da yar manyan raunikan dake jikina suka warke na auki surutuna manya na kai kasuwa na saida na ha a ku in na je gidan nayi masu bankwana da godiya na basu makullin shagon na ara gaba, ban tsaya ko'ina ba sai garin Zamfara. A Zamfara ma nayi rayuwa mai wahalar gaske domin na isa ban da ku i kuma ban san kowa ba, kuma ban samu wanda ya taimake Ni ba, don haka a kasuwa na cigaba da rayuwa ta ina kwana cikin masallacin kasuwa nan nake rayuwa ina sana'ar dako da aikin gini da wanke mota ko mashin, sannu a hankali na fara ha a kayan gyara kasancewar na iya gyara sosai na kama gyaran mota da mashin a cikin tashar, cikin ikon Allah na samu mutanen da suke kawo min gyara sosai sai ga Ni na maida ku en da akai min fashi a garin Bauchi har da riba. Sai ga Ni har da yarana wa anda suke tayani aikin gyara a cikin tashar abun gwanin ban sha'awa, sai dai nakan shiga cikin gari na yi yawo sosai ina neman Alawiyya duk inda naga mai saida abinci inyamura sai na tambaye ta ko ta san wata mace mai saida abinci da tai zama a Lagos mai suna Iyami? Ban ta a dacewa ba har Allah Ya kawo wata addarar ta afka min, ta wata motar baban Soja daya kawo gyara yaban makullin cikin dare ban ankara ba yarana ashe sun ha a baki suka kwashe kayan motar masu muhimmanci suka gudu, daman ga shi Ni da su duk aya ne, basu da kowa a garin ka zo Na zo ne Ni da su baki aya a garin. Ai kuwa sojan ya ce bai yadda ba, ya turomin yaransa suka tafi da Ni barikin su babu wata irin azabar da basu yi min ba, ya wace duk wata dukiyata ya kuma yi min azaba ta tsawon wata guda sannan ya sake Ni, lokacin ko tafiya ban iya yi tsabar wahala da na sha gun sojan nan yasa na fita hayyacina na koma kamar mahaukaci. Haka na bar garin Zamfara wutsiya zage ba arzi i ga Ni ban da komai ban da abin komai. A haka na samu na ji jinyar jikina na wahalar dana sha, na nemi taimakon ku in mota a masallacin da nake zaune a tashar na shiga motar Kaduna saboda naji ana cewa garin ya tara kowane irin yare musulmi da arna don haka sai na tafi can ko Allah zai sa na ga Alawiyya tunda Iyami arniya ce ba mamaki tana can tana cigaba da saida abincin tare da Alawiyya. Zamana garin Kaduna da farko na sha wahala saboda rashin ku i da rashin sabo da garin yadda ya ha a manyan hatsabibai manya da yara bariki iya bariki babu wanda ba a yi a garin Kaduna. Sai kawai na dage da neman na kaina ta hanyar shiga aikin sauke siminti da nake duk rana ba fashi har na samu ku i masu yawa ba laifi na kama shagon da na dinga kwana tunda da a tasha nake kwana asan motoci. Sannu a hankali na cigaba da keman ku i kuma na dage da zuwa duk inda naji ance ana saida abinci kuma arna ke saida abincin ko da akwai nisa mai yawa sai na je na duba ko zan ga Alawiyya ko Iyami amma ko mai kama da su ban ta a gani ba. Cikin taimakon Allah na sake samun jarin gyaran motoci da mashina a ofar shagon dana kama haya nake gyarana. Sai ga Ni na fara sayen mataccin motoci ina gyara su ina saidawa da farashi mai tsada, kafin ka ce me? Har na samu ku in da na sayi gidana arami a Kaduna na kuma siyi mota mai kyau ba laifi ina yawon neman iyata Alawiyya. Na jima a Kaduna har Allah Ya ha a Ni da wani
Chapter 82 · 0% Book details