← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 133

Sashe 80

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

daga yi mata aikin akai aurena da Faisal lokacin na kama aikina na lauya sosai babu garin da ban zuwa kan aikina, a haka Allah Ya azurta Ni da yara uku maza biyu mace guda an biyu duk maza na fara haifa aka saka masu sunan Daddy da Kakana amma ana kiransu da Affan da Aiman sai macen da na saka wa sunanki Hawwa'u nake kiranta da Jiddah. Wannan shi ne labarina bayan rabuwarmu dake Jiddah." Cewar Alawiyya tana kallon Jiddah dake ta kuka. Wayar Alawiyya ce tai ara tana agawa aka gaya mata cewa tai ba uwa daga nesa tana son ganinta. Bata ji komai ba ta bada umarnin a kawo ta gidan da take yanzu tana jiranta. Ba da jimawa ba sai ga tsohuwa an kawo ta kamar ba ita ba,madadin tai rame ko ta yamutse sai ma kyau da tayi. Su duka suka fasa ihu suka rungume ta suna ihun tsohuwa ta dawo ga tsohuwa. Kasancewar mutanen gun kowa yasan labarin tsohuwa shi Daddy shi ne ma yafi kowa sanin ta domin ita ce ya auri Fatima gunta kamar ya fi su murna ma. Bayan an gama murna ne tsohuwa ta fashe da kuka tace, "Na samu labarin abin da ya faru ne ta hanyar sauraren rediyo da jikana ya zo kuma ya sake bayyana min abin da ya gani a jarida, tabbas a nan na amince da cewar Alawiyya ce da Fatima, hakan yasa na matsa ma jikana sai ya kawo Ni Kaduna domin Ni ina zaune ne a auyen Sokoto wani auye da ake kira FANGWA to da can muke zaune sai kuma jikan nawa ya samu aukaka ta hanyar samun aiki mai kyau a cikin garin Abuja a wata ma'aikata har suka ba shi gida da mota, hakan yasa ya auke Ni kuma koma can da zama cikin kwanciyar hankali." Jiddah ta dubi tsohuwa tace, "Amma me ya hanaki komawa Lagos bayan kin bar Alawiyya gidanmu tsohuwa?" Hawaye suka zubo ma tsohuwa tace, "Bayan na koma garinmu ne da nufin nayi wata guda na dawo sai hakan bai samu ba, domin daren ranar da zan dawo ne aka fara fa an siyasa, wanda aka kashe mutane da dama na garinmu wasu aka raunata su sosai. Ni da Yarona muna zaune yana fama da Ni kan na ha ura na zauna nan yanzu yana samu ba kamar da ba tunda har ya yi aure matarsa ta haihu ma yaron ya girma sosai, ya ce zai iya ri e Ni nace mai sai idan ya amince zan je na dawo da Alawiyya nan wajena na ba shi labarin kaf rayuwata da Fatima har zuwa kan Alawiyya, ya yi jim sai kuma ya ce, amma Inna ai da kin sani da ita kika dawo, da baki baro ta gun arniya ba, tunda ke iyayenta suka ba amanarta don haka ki bari a gama wannan guguwar siyasar sai na raka ki mu je tare ki amso ta, idan ya so sai mu bar sa on idan iyayenta sun zo neman ta su zo nan su amshe ta." Har dare ya yi muna ta fira da shi ya tafi, washegari sai dai na ji kururuwa daga cikin gidansa wai wasu sun shigo sun kashe shi har da matarsa an sa kuwa sun ji mai rauni sosai. Wannan tashin hankalin yasa na manta labarin komawa Lagos har sai da jikana ya samu lafiya lokacin komai namu ya are ban da komai hatta gidanshi na saida sai gidana kawai inda muke rayuwa nida jikana. A haka mu kaita rayuwa cikin ba in talauci na tsawon lokaci har Allah ya kawo wani bawan Allah ya taimaka ya auki jikana yana mai aikin lissafin ku e daga nan ne ya zama silar samar mai aiki a wani banki dake Abuja muka koma can rayuwa tai mana da i, bayan mun koma ne na matsa mai muka shirya muka je Lagos nemanki amma aka ce mai ai ba a san inda kuke ba ke da Jiddah an neme ku an rasa haka ma an nemi Iyami an sara kuma Babanki ya je nemanki bayan guduwar Iyami. Tun daga lokacin nake neman ki ta hanyar addu'ar Allah Ya bayyana min inda kuke shiru. Sai jiya ne naji a labarai an kira sunanki dana Jiddah sai na amince da cewa ke ce, da jikana ya dawo nai mai magana sai ya ce ai kowa yasan ki yana ma da hotonku shi ne ya nuna min nace tabbas kuwa ke ce, hakan yasa na shirya nace Yau ban kwana sai na zo Kaduna tun da akwai kotun da kuke shari'ar nasan zan ganku." Su duka sukai mata jajen anta da ta'aziyya,sannan ta dubi Baban Alawiyya tace, "Bello me ya faru bayan danginka sun tafi da kai baka dawo ba, bayan kai min al awari zaka dawo?", Daddy ya nisa ya ce. Mu ha u a page na gaba don jin labarin Daddy bayan ya shiga duniya naman iyarsa Alawiyya. Taku a kullum Haupha [9/14, 6:39 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa
Chapter 80 · 0% Book details