Sashe 49
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zage na gyara akin na kunna turaren wuta. Hajiya Turai ta zabga min mari tace, "Allah idan Alh ya dawo gidan nan ki ka gaya mai wani abu daya shafi abin da ya faru sai na lahira yafi ki jin da i, wai tsabar neman abin duniya ma wai namiji kika haifa, kan uban can namiji fa ke? Allah na tuba ko mace baki isa ki haifa ba balle namiji ba a gidan nan." Haka dai suka dinga min kashedi da barazana son ransu suka gaji suka fice suna ara jaddada min da kar na yi masu ba daidai ba gun maigidan. aramar takurawa su ke min ba, cikin lokacin sai da Allah Ya maido Alh sannan suka shiga tattalina suna nuna mugun tausayina gabansa, hakan yasa ya ji da i har ya yi mana kyautar zinari mai tsadar gaske. Ban san me suka tsara ba amma dai naga yanzu idan yana gida to tare muke cin abinci suna ta fira don Ni ban saka baki, saboda nasan duk shiri ne, yana fita suke shigowa akina su yi mun tas, har dukana su ke kamar iyarsu haka suke maida ni bayan idon maigidan. Sai da ya yi wata guda da dawowa sannan yake gayamin ai ya je gidan Inna amma bata nan, amma an gaya mai ta bar Alawiyya wajen wata Iyami mai saida abinci, ya je can ma ya iske Iyami ta bi dare ta gudu asarsu da yaran ba wanda yasan inda take . Na yi kuka sosai na shiga damuwa domin na fahimci cewa Alawiyya da Inna sun rabu kenan rayuwar Alawiyya ta shiga cikin gararanba da ha'ula'i kenan. Sai da Alh ya yi da gaske na daina nuna damuwata a gaban idonsa sai ya tafi nake cin kukana iyakar son raina su Hajiya Turai na mun dariya. Wata rana kamar ance na duba inda nake ajiye ku e da sar in da Alh ke saimana sai naga babu komai gun, abin ya tabbatar min da cewa an sace su kenan. Duk da ance zargi bai da kyau amma Ni dai su Hajiya Turai na zarga domin ban da kowa sai su, haka zalika ban da awa ko abokan arzi in dake shigowa gidan da sunan waje na suka zo tunda nake a gidan ban da kowa, to ta ya za a shigo ai min sata? Kamar na gayama Alh sai kuma na fasa na barsu da Allah nasan shi ne kawai zai iya sakamun. BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR. Komi ya sauya min baki aya ga ciki ga Alh ya tsane Ni wai an gaya mai duk arin da nayi a baya nice ke zubar da cikin don ban aunar haihuwa da shi, ban san jininsa. Hakan yasa baki aya ya fita sabgata ya daina min magana sannan ya daina shiga sashena ya ce shima cikin na jikina bai so na zubar . Ga wannan karon wani irin azanabben ciki na samu mai shegen laulayi da kwa ai amma ban da ikon cin ko da cinyar kaza ce a gidan, sai abin da suka ban kawai don mugunta sun san ban san wake da shinkafa sai suka dinga ban ita kullum safe rana dare, duk sanda na ci sai nayi amai na galabaita na fita hayyacina amma ko a jikinsu, ga shi cikin ya yi wani uban girma afafuna duk sun yi kumburi sosai Ni kaina tsoron girman cikin nake idan ina tsaye gaban madubi. Haka na sha ba ar wahala har Allah Yasa cikin ya kai wata tara cif, wata rana da rana ina zaune naji alamar haihuwa, kuma na ji motsin maigan a falo don haka na rarrafa na isa inda yake zaune ina kuka na ri e mai afa nace ya taimaka ya kaini asibiti haihuwa zan yi. Kamar ba zai kalleni ba, kuma sai ya yi sauri ya auki makullin mota dake aje gefensa ya kama Ni muka fice zuwa asibiti. Da yake haihuwar ta zo gadan-gadan yasa bai nufi asalin asibitin da muke zuwa ba ya kaini mafi kusa kar da na haihu a mota. Ban jima ba na haifi yarana biyu duk maza cikin oshin lafiya. Matu ar murna tasa ya manta da laifin da yake kallona da shi ya rungume ni yana kukan farin ciki yana ta saka mun albarka. Tun a kan hanya yake fa awa mutane gidansa an haifi yara biyu duk maza yanzu, ina ga murna ta sa ya manta da gayama su Hajiya Turai haihuwar, sai da mu ka je gida suka ganmu auke da yara a hannu suka zaburo kamar kamun hauka suna tambayar yaran waye kuma mata ne ko maza? Ni dai da yake ya kira wata tsohuwa ya ce ta dinga ma yaran wanka tana dafa mana ruwan wanka sai na shige aki ina godiya ga Allah da baiwar yaran da ya ban lokaci guda ba tare da na zata ba. Tamkar hauka haka Alh ya dinga kwaso kaya yana labta min a aki na yara da nawa ne kawai, su kuma su Hajiya ya basu Naira miliyan biyar-biyar ya ce kowacce ta sai kayan suna. Ranar suna aka raba atamfa da takalma har da dardumar sallah ga duk wanda ya zo taron sunan. Ni dai da yake ban san kowa ba sai ya kasance duk mutanensu ne cike da gidan da jama'ar Alh. Bayan suna da sati guda ne suka tare tsohuwar dake zuwa saka mana ruwan wanka sukai mata kashedi suka ce kada ta sake zuwa gidan an kore ta. Ta shigo ta gayamin nace ta gayama maigidan ya yi masu magana don tana taimaka min sosai duk lokacin da take nan nake samun damar aiwatar da ayyukana yadda ya kamata saboda ban manta kashedin da sukai min ba na cewar sune ajalin yarana duk daren da ewa sai sun kashe su sun kashe ni idan ta kama har maigidan sai sun ha a sun kashe ba uwar da za ai. To sai na dinga rufe sashenina idan Alh bai nan ko tsohuwar ta zo sai na saka makulli na barshi a jikin ofar saboda kar su shigo don na tsorata da su sosai na shaida rashin imaninsu gabana suka kashe jaririn wata bakwai. Cikin nasara tsohuwar ta samu ganin maigidan ta gaya mai ya bata ha uri ya ce ta dinga zuwa har su girma ita ce mai kula da su shi ya kawo ta ba su ba. Su ma a ranar sunga ruwan masifa har ya yi i irarin duk wadda bata yadda da abin da yake so ba to ofar gidan a bu e take ba wadda ya ri e a cikinsu zata iya tafiyarta. Tun daga lokacin sai wasu manyan abubuwa suka fara faruwa a gidan na bayyanar wasu halittu duk sanda aka kwantar da yaran sai su bayyana su kama yagin yaran kamar mage ta yakushe su su dinga kuka, da an zo kuma sai su ace. Tun bai yarda ba har dai wata rana shi ma ya gani da idonsa, hankalinsa ya tashi sosai yana tambata "Daga ina suke Fatima? Waye ya turo su? Kashe min yara za su yi ne?" Ni dai na gode wa Allah da Yasa ya gani da idonsa , hakan yasa ya ce min na shirya zai auke Ni daga gidan ya sauya min gida saboda rayuwar yaransa. Ranar da ya tara su Hajiya Turai ya gaya masu abin dake faruwa da abin da ya yanke shawara daya yanke sai su kai tsalle suka dire suka ce ba su yarda ba babu inda zai kai mu. Shi kuma ya ce basu isa ba ya gama shawara dole yabar gidan nan da yaransa kada wani abu ya same su a banza su ne kawai yaransa duk duniyar nan. Daren ranar da ya ce washegari za mu tafi wani gidan ina kwance ina barci kawai naga wata mata ta tsago bango ta fito kafin in motsa ta huro min iskar bakinta cikin idanuna kawai sai naji wani irin zafi ya ratsa fuskata kamar wasa na dinga jin zogi a idanuna shike nan sai naga ban gani. Saboda makantar da ta sameni yasa Alh yabar maganar tashina daga gidan don dole tunda ban gani ga yara kuma. Sai ya nemi alfarmar tsohuwar nan ta dawo wajena da zama baki aya tunda ga lalurin daya same Ni kuma babu irin neman maganin da ba ai ba amma ba wani alamar zan samu waraka duk asibitin da aka je sai su ce basu ga komai ba su don haka ba abin da za su iya yi min su. Wata rana muna zaune da tsohuwar nan mai suna Baraka sai ga wasu attin maza sun shigo su Hajiya Turai na biye da su a bayansu, Ni dai ban gani ba amma naji tsohuwar nan na basu ha uri amma haka suka kwashe yarana suka fice bayan sun yi ma tsohuwar duka guda wanda yasa ta sume. Ni ma haka ba tausayi suka buga min bakin bingida ban sake sanin abin da ke faruwa ba. Kawai na farka na jini a kan gadon asibiti Alh na zaune ri e da hannuna yana kuka. Sai da na kwana biyu sannan aka sallame Ni domin naji rauni a kaina sosai don har aske gashin wajen su kai suka saka min magani. Lokacin da muka koma gida ashe Alh bincike ya fara na sanin inda aka kai mai yara da su waye suka turo aka kwashe mai yara. Ban sani ba ko zargi ne yake koko me ya faru oho ashe wai ya saka Camera ko'ina a cikin gidan duk abin da ke faruwa yana kallo a cikin akinsa duk motsin kowa yana gani. Bayan sati biyu da saka Camerar sai ya zauna ya bu e don yaga me ya faru da bai nan don ya yi tafiya kwana biyu. aramin tashin hankali ya shiga ba ganin abin da ke faruwa ba, Hajiya Turai da Hajiya Tani ne a zaune sai ga wasu atti su hu u duk sun rufe fuskarsu ba a gane ko su waye su suna zaune. Hajiya Turai ce ta fara magana, "Yawwa Dauda yanzu aikinku ya kammala yadda muke so saura abu guda ya rage ku ida mana shi ne ku kawo mana bidiyon kashe yaran da za ku yi mu gani don mu