← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 133

Sashe 24

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *Ina matu ar godiya ga dukkan mutanen da suka kirani don yi mun gaisuwar rashin da mu kai, da masu yi ma Mamana addu'ar samun lafiya, duk na gode sosai da sosai Allah Ya bar zumunci*. Hauphanku ce Page 19 "Jiddah kuka ba abin da zai maki, don haka ki share hawayenki ki natsu ki koma ga Allah ki dage da addu'a shi ne mai maganin kowace irin damuwa. Wallahi Jiddah a wannan lokacin babu macen da bata da matsala a gidanta sai dai ta wata tafi ta wata, amma duk wadda zata dube ki tace bata da matsala a gidanta to arya take, yanzu lokaci ne muke wanda babu babba babu yaro kowane gida sai kin samu matsala ko dai ga maigidan ko ga matar gidan. Sai dai kawai mu cika fili da addu'a Jiddah amma don Allah ki daina saka damuwa a ranki ki daina takura ma zuci yarki da tunani saboda kinga kina da hawan jini kuma mai hawan jini ba a son shi cikin damuwa." Tunda Mamar Khairat ta fara min nasiha nayi shiru ina kallonta domin dai Ni damuwata guda, ina na samo aljanu? Ni dai a sanina ban da aljanu sam, kuma wane irin duka ne nayi wa Safiya? Duk da daman naji a lokacin tamkar na kamata na yi mata dukan tsiya lokacin da take gayamin maganganun sai kuma na dake na share ta har kaina ya fara sarawa ban ce mata ala ba, don ba zan iya cewa ga abin da ya faru ba Ni a tsakaninmu ba sam. Sai yamma lis sannan an kawo min tuwon dare daga gidan Maman Khairat, ita kuma ta bi yaran da suka kawo min tuwon suka tafi tana min Allah Ya sawa e, har ofar gida na raka ta tana ta ara min nasiha kan nayi ha uri watarana sai labari. Bayan Maman Khairat ta tafi ne nayi alwala na zauna ina jiran kiran sallar magrib naji shigowar mutun ko ban tambaya ba nasan maigidan ne don shi ka ai ne yake shigowa bai sallama. Haidar ya nufe shi yana kiran Abba amma ko waigen shi bai ba ya shige aki. Ba aramin fa uwa gabana ya yi ba amma sai na dake na mi e a hankali na nufi akin, har ya kwanta kan gado yana shafa wayarsa, ga dukkan alama abin da yake yi da wayar nayi ma shi da i don sai murmushi yake. Da sallama na shiga akin, da yake akwai wutar NEPA don haka ina ganin yadda nan take murmushin fuskarsa ya kauce ya gayyato acin rai ya shimfi a akan fuskarsa. Ban damu ba nasan zan ga fiye da hakan, na isa na zauna gefen gadon nace, "Sannu da zuwa Abban Haidar." Kamar yadda na zata hakan ya faru ko ala bai ce ba, na sake maimaita wa sai ma ya saki uban tsaki ya dube ni a fusace yace, "Wai miye daga zuwana za ki isheni da magana?" Kaina na asa nace, "Sannu da zuwa nake maka fa." Ya an tsura min ido sai kuma ya tashi zaune yace, "Da gaske kina da aljanu? Kuma sun bugi Safiya azun?" Girgiza kaina nayi alamar a'a, an tsaki ya sake ja yace, "To wallahi kin ji na gaya maki daga Yau sai Yau kowa ya yi rayuwarsa a gidan nan kar ki sake shiga rayuwata kamar yadda Ni ma ba abin da ya shafe Ni da taki rayuwar." Ban ce ala ba ya koma ya kwanta yana tsaki akai-akai. Haka na dawo falo na gyarama Haidar kwanciyarsa, can cikin barci na ji shi yana kirana, kamar na share sai kuma naga ba kyau, don haka na tashi naje, ba wata magana ya jani jikinsa, ya biya bu atar sa ya juya ya kama barci. Ba abin da na tsana irin na ha a jiki da Deeni Allah Ya zuba min tsanar mazinaci na tsani zina don haka na koma falo nayi kukana na gode wa Allah na tashi nayi wankan tsarki na kwanta. Washegari tunda safe ya bar gidan, ba tare da ya ban ko sisi ba, ga Haidar bai da ha urin yunwa sai ya tasani gaba ya yi ta kuka, idan yana jin yunwa, hakan yasa na bishi da sauri na ina kiran sunansa, har ya an yi nisa ya juyo fuska murtuk yana kallona baice ala ba, cike da warin gwiwa nace, "Ka manta baka ban ku in kalaci ba, kuma naga idan rana tayi arewa yake." Idan bango ya tanka min shi ma ya tanka min, haka ya are min kallo ya juya ya yi tafiyarsa ya barni tsaye ofar gidan ina bin bayansa da kallo. Ko da na dawo gida na auki tsintsiya ina shara kamar wasa naji amai ya taso min, cikin lokaci ka an nayi amai sosai har ya kai idan nayi aman sai dai nayi aman yalon ruwa mai aci, ga Haidar na bina yana kukan yunwa, duk na rasa yadda zan yi saboda na fara galabaita sosai da aman. Kafin kace me zazza i ya rufe Ni na lalla a na shige falo na kwanta ina jan Haidar jikina shi ma ya kwanta don ban da sanyi ba abin da nake ji, shi kuma kuka yake tamkar ana tsunkulinsa. A haka Maman Khairat tai sallama, ina jinta amma ban da ikon amsa mata sallamar amma har ga Allah naji da in zuwanta, ko ba komai zata kama min Haidar na samu na natsu na ji da kaina. Ai kuwa har da kofin kununta da fanke ta zo, ta zuba ma shi a kofi ta ba shi sannan ya bar kukan ya kama sha yana gwarancinsa na yara. "Jiddah ba dai tun jiya baki lafiya ba? Ki ka kasa aikawa a gayamin kuma? Ta ya za ki zauna da ciwo ke ka ai a cikin gida Jiddah?" Ni dai zuwa lokacin ban da kyarma babu abin da nake yi, Saboda baki aya zazza in ya gama rufe Ni jikina ya auki zafi sosai da sosai . Ina jinta sama-sama ta fice bata jima ba ta dawo, ashe magani ne ta siyo min, ta ebo ruwa tace, "Jiddah nasan baki iya shan kunun nan don haka tashi ki sha ruwan shayi ga shi sai ki sha magani kwanciyar ba magani ba abinci ai bata yiyuwa." Ban san magani ko alama don haka nayi kamar ban ji ba, amma ganin ta matsa da magana dole na tashi na amshi maganin nasha da ruwan shayin na koma na kwanta. Sai dai ko gama kwanciya ban ba amai ya wace min ta baka ta hanci, sai da nayi mai yawan da yafi ruwan shayin dana sha sannan ya lafa na koma na kwanta. Ita ta gyara gun tas, ta fice ta ida sharar dana fara ta tattara kayan wanke-wanke tayi duk ina kwance ina jin jikina na ciwo kamar ana daddaka min shi haka nake ji don haka nake ta juye-juye ga shi ban iya ko aga kaina saboda shi ma ciwo yake sosai. Haka na wuni don haka ta tafi zuwa can ta dawo da mutanen gidansu aka sakamun arin ruwa, suna zaune Deeni ya shigo kamar yadda ya saba ba sallama ya ra a su ya wuce bai ce ma kowa komai ba, sai su ne suka dinga gaida shi suna tambayar ya mai jikin, ba tare daya kalleni ba yace da sau i ya shige aki abinsa. an jima kana ya fito ya sauya kaya ya fice bai ce ala ba. Maman Khairat ta dube ni, "Yaushe maigidan ya dawo ne Jiddah?" Cikin yanayin maganar marar lafiya nace "Jiya ya dawo bayan kin tafi gida." Ta sake kallona "Kuma yasan baki lafiya kafin ya fita?" Kaina na girgiza alamar a'a bai sani ba. "Allah Ya kyauta! Abin da tace kenan tabar maganar. Wasa-wasa sai da na share kwanaki ina fama da ciwo daga wancan sai wancan a lokacin ne Maman Khairat ta dube ni tace, "Anya kuwa Jiddah ba ciki ne da ke ba? Na lura duk wasu alamomin ciki sun bayyana gare ki fa." Cike da mamaki na waro idanuwa ina kallonta, wane irin ciki kuma? Ni da rabo na da Deeni har na manta inba ranar da ya dawo ba, kuma shi ma a ranar shi ka ai ya yi ki i da rawarsa? Anya kuwa ana samun ciki daga ha uwa aya? Itama marar da i irin wannan ha uwar... "Ya daga tambayarki kin fara sana'ar taki Jiddah? Yaushe za ki daina tunani ne wai? To ki sani masu ciki ba a san ko da damuwa suna saka kansu a cikin matsala, dama kin ture komai kin natsu kin zauna lafiya." Cikin sanyin jiki na dubeta nace, "Ba shakka cikin ma zai iya yiyuwa domin Ni dama ba wani ganin jinin al'ada nake ba duk wata ina shafe watanni ban ganshi ba, yanzu haka rabona da shi tun kafin na yaye Haidar Maman Khairat, amma ban da tabbas gaskiya." "Idan kau haka ne ki tambaye shi gobe sai na raka ki asibiti ai maki awon cikin don mu samu tabbas." Cewar Maman Khairat. Sai da dare da Abban Haidar ya dawo na iske shi da maganar zuwana asibiti, ban oye mai ba na gaya mai zan je ai min awon ciki ne don ciwon da nake ya yi yawa. Banza yai da Ni tamkar bai akin, na gaji da jiran ko zai tanka bai tanka ba na tashi na koma falo don tuni mun raba aki yana urya ina falo. Washegari Maman Khairat ta zo mu je asibiti na gaya mata yadda mu kai tace "Ai ciwo ne mu je kawai." Ai kuwa muna zuwa awon farko aka tabbatar da ina da yaron ciki. Sam ban murna ba, sai naji wani bala'in tausayin kaina, ko yanzu daya nake ri e da Haidar kawai balle ga wani cikin? Sai nafi sati guda ban kama Naira ari in Abban Haidar ba. Ko da yaushe daga gun Mamana sai gun Maman Khairat kawai nake samun auki, sai kuwa Binta wani sa'in takan kawo min abinci har gida ba kamar idan
Chapter 24 · 0% Book details