Sashe 103
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fal farin ciki. Sun jima a hakan sannan ta rufe motar ya ja mata akwatinta suka shiga gidan tamkar wasu sabbin amare satin farko da aure. Hajjo ta kalle su ta kauda kai, don tana jin maganganu marassa da i dake kai kawo daga cikin gidan Mustapha in wanda ita ba zata jure su ba sam. Har aki ya kai mata kayanta ya fito suka gaisa da Hajjo fuskarsa cike da farin cikin ganin masoyiyarsa ta zo. Hajjo ta ta e baki tace, "Kai gafara can tun da Jiddah tabar garin nan ban sake ganinka ba sai Yau data dawo to ban maraba da kai Ni." Ya sha kansa yana sunne kai ya ce, "Afuwan Hajjo wallahi ban zaune nima yanzu haka Yau na iso garin afuwa nake nema dai bamu haka dake ai." Shiru tai don maganar da matarsa ta saki a cikin akinta jiya ba aramin shiga kunnenta tayi ba duk da ba da ita suke maganar ba amma dai ai taji. Tana jin Maryam na cema Bilkisu Yau kwana biyu kenan yaranta basu lafiya amma tayi mai maganar duniya ya i kai su asibiti ko ya bada ku i ta kaisu ita kanta bata lafiya amma ba tasu yake ba, idan ta matsa da magana kuma ya dinga masifa yana turaja shi bai san haka, to ina zata bari Jiddah ta kai kanta gidansa ? Sai ta ara tsuke fuska tai banza da shi kawai ta tashi ta shige akinta tana cema Jiddah ga kayan abinci can idan zata ci ta iba. Tana shiga ya langa ar da kansa abin tausai ya ce, "Princess me nayi ma Hajjo take fushi da Ni kuma? Allah Yasa ba hanani aurenki zatai ba Princess." Ita kanta sai da gabanta ya fa i jin abin da ya ce, kuma ta lura da sauyin Hajjon Yau itama wanda bata san ko na miye ba, amma dai zata ji ko na miye tunda suna tare ai. Sai ta kwantar mai da hankali sosai tace mai zatai magana da ita karya damu Hajjo nada fahimta kuma ai da tana son shi yanzu ma dole akwai dalilinta na yin hakan. Shi dai cike da sanyin jiki yabar gidan yana jin damuwa fal a ransa na sauyin Hajjon. Yana shiga cikin gidan ya iske su suna halin nasu ko kallo basu ishe shi ba ya wuce su kowacce na zagin ar'uwarta kan yara shi dai ba tasu yake ba abin da ke ranshi yafi arfin fa an nasu ya samu ya kwanta yana jin sautin bugawar zuciyarsa. Kasa jurewa ya yi ya kira wayar Princess in don ya ji abin da ke faruwa wanda yasa Hajjo sauya mai fuska. Jiddah ta auka tasan cewa daman yana can cikin damuwa don haka ta fara da cewa, "Zaka iya fa a min gaskiyar magana idan na tambaye ka Prince?" Kamar tana gabansa haka ya girgiza mata kai sai kuma ya ce, "Wallahi zan fa a maki koma miye Princess in dai na sani wallahi tambaye ni." Ta ja ajiyar zuciya tace mai, "Prince yaranka su waye basu lafiya ne yanzu haka?" Ya yi jim sai kuma ya ce, "Lafiyarsu lau amma dai jiya na saima Hanan maganin zazza i dake damunta." Tace to, "Maganar gaskiya jama'a ne suka tabbatar ma da Hajjo cewar yaranka basu lafiya kuma matarka ma bata lafiya amma kace kai ba tasu kake ba." Ya yi ajiyar zuciya irin ta takaici ya ce, "Princess wallahi ba haka bane ba, na sai mata magani kuma a cikin matan ba wadda tace min bata lafiya duk suna ta harkar gabansu." Hajjo dake gefe guda tana ji ta sauke ajiyar zuciya don dama ta auka da gaske ne duk da tasan yana da tausai ba komai take yadda ba idan aka ce ya yi ba. Jiddah tace, "Na gane Prince na kuma fahimci inda maganar ta dosa, anyi amfani da Hajjo ne matsayinta na wadda nake da kusanci da ita aka ata ka gunta saboda taji tsoro tace ba zan aure ka ba. To ba komai ai Ni zan zauna da kai ba wata ba don haka ka kwantar da hankalinka kai dai ka zama mai tsare gaskiyarka ka zama mai adalci ka kiyaye duk wasu ha i nasu dake kanka zaka zauna lafiya." Godiya ya yi mata ya ce "Insha Allah Princess za ki same Ni mai kwatanta adalci mai yin duk abin da ya kamata na kuma bar ko waye ya yi min wannan sharrin da Allah." Hajjo ta saki ranta don ta gamsu da maganar Jiddah sai yanzu ma ta fahimci daman sa o ne aka na o har cikin gidanta aka bata saboda kawai a rusa auren to Allah Ya kyauta. Ta jima tana kwantar mai da hankali sai da taji ya fara dariya sannan sukai sallama ta kira lambar Abubakar dake ta kiranta tana waya. "Ranki ya da e kin iso ne?" Cewarsa. "E na iso yanzu haka na gama shiryawa zan fito anjima zuwa can kotun da za ai shari'ar don gabatar da kaina." Godiya yake yana arawa cikin alamar kuka ita dai ta kashe wayar kawai don tare za su fita da Prince sai taga dacewar ta shiga gidan awarta Bilkisu su gaisa an da e basu ha u ba. Tana shiga ta iske ta zaune su ka gaisa kamar yadda suka saba, sai Bilkisu ta kalli Jiddah tace, "Kin ban mamaki awata ban ta a tunanin za ki yi min haka ba sai ga shi kin yi min." Jiddah ta dube ta da kallon rashin fahimta tace, "Bilkisu ban gane ba me kike nufi da hakan?" Tai dariya tace, "Yanzu ace kina soyayya da ma wabcina amma ko da wasa baki ta a gayamin ba?" Bilkisu tai murmushi don ta fahimci inda maganar ta nufa yanzu don haka sai tace cikin murmushinta "Au don zan soyayya sai kuma na gaya maki ashe? Na auka kin bari ai sai anyi bikin ban kawo maki kayan auren ba sai ki yi min mitar nayi aure ban gayyace ki ba." Ko da taji amsar Jiddah sai ta wayance tace, "Abin ne yaban mamaki Jiddah da Mustapha na soyayya wai." Jiddah tai dariya tace, "Bamu dace da juna bane ko yafi arfina Bilkisu?" Tana ya e tace, "Kai haba Ni na isa nace haka? Ai nasan idan ke baki ce kin fi arfinsa ba shi ba za a ce yafi arfin ki ba." Jiddah ta sake duban fuskar wayarta tana kallon hotonsu ita da Prince in tace, "Kin san shi aure HA IN ALLAH ne don haka Ni da shi HA IN ALLAH ne kawai ko Ni ba zan ce maki ga rana ko lokacin da na kamu da sonshi ba." Sai ta yamutsa fuska tace, "Amma dai kin yi dace don kun dace sosai ya huta da ba azanta da rashin godiyar matansa ma ai." Jiddah ta murmusa tace, "Wannan kuma daban kowa kansa ya sani Ni ban san komai ba sai soyayyata da shi kawai mantawa nake da wasu matansa ko wani hali na gidansa." Ta mi e ta gyara gyalenta tace "Zan tafi akwai inda zan je dama shigowa nayi mu gaisa kwana biyu ba a ha u ba." Tana maganar tana tafiya don haka bata damu da kiran da Bilkisun ke yi mata ba kawai tafiya take abinta tana murmushi. Yana zaune ya sauya kaya sai amshin nan nashi yake ya cika ko'ina da amshi suka dubi juna suka saki murmushi. "Wow! Prince kaga yadda kai kyau kuwa?" Tai maganar tana kallonsa ta ri e bakinta. Sai ya yi murmushi ya ce, "Ban yadda ba Princess domin ke ce kikai kyau har ma naji kishi ya kamani kada ki wuce wani ya ganki ya ji yana sonki." Sai gardama ta kaure a tsakaninsu kowa na cewa kowa yafi shi kyau har suka auki lokaci mai tsawo suna gardamar har Bilkisu ta fito ta kalle su ta shige gidan Mustapha in ba a jima ba sai ga yaran gidan suna le owa aya bayan aya. Ganin haka yasa Jiddah cewa su tafi time na urewa don za su je yawon soyayya daga can. Suna tafiya suna firar duniya suna ta nisha i gwanin da i, har suka isa inda za su. aramin mamaki mutanen gun su kai ba ganin Barista Hawwa'u Bishir (Dawa)ce zata kara da Barista Alawiyya Bello Gareji ba , nan da nan sai ga an jarida sun rufe su wai ya take ganin wannan shari'ar zata kaya a tsakaninsu kuwa, ko sun manta su in Aminan juna ne wasu ma cewa suke gidansu guda amma zasu yi shari'a tare matsayin kowa da wanda yake karewa?" Dariya tai tace, "Ku dai ku zuba ido ku sha mamaki amma tabbas gobe zamu bayyana don karawa." Daga can suka wuce wajen sha atawa suka dinga yawo kawai cikin gari haka kawai sai wajen goman dare suka koma gida. Da uwar siyayyarsa da ya yi mata, tana kula komai ya sai mata zai siyi wani daban, taji da in hakan don tasan na gidansa ne ya siya ko bai fa a mata ba. Ko da suka dawo sun jima suna fira sannan su kai bankwana tana jaddada mai ya dinga cin abinci don ta gaji da ganinsa a rame ko da yaushe sai ba i yake alamar bai da natsuwa da kwanciyar hankali. Washegari tunda safe ta kira Alawiyya tace ta zo ta auke ta idan zata Kotun. Haka kuwa akai sai ga Alawiyya cikin shirinta itama daman ta shirya suka auki hanyar Kotun suna ma juna dariyar kowa zai nasara? Suna isa suka iske Kotun cike da mutane kowa ya zo don ganin wannan Shari'a ta Aminan juna kuma abokan juna sannan an'uwan juna. Nan da nan an jarida su ka yi masu caaa! Kowa da abin da yake son ji daga bakinsu amma su kai tsit sai murmushi kawai da suke saki. Abubakar ganinsu tare sai da gabansa ya fa i ya tabbatar da cewa ya yi wauta na zuwa gun wadda ya yaudara ya yi ma butulci neman taimako. Bai san cewa bakinsu guda ba ai da bai je ba sam, amma ya mi a komai ga Allah shi ne kawai zai bayyana gaskiyar lamari, sannan ko da ace an yanke mai hukuncin kisa ba zai damu sosai