Sashe 46
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
gun furta kalmar Warrrr kamar wasu zararru. Kallona ya yi, "Fatima waccan ita ce Hajiya Turai, ita ce ta fara shigowa sai wannan ita ce Hajiya Tani, su ne matana da na gaya maki guda biyu, Allah bai bamu haihuwa ba, har zuwa yanzu muna saka rai dai." Ya nuna min wata ofa waccan ita ce hanyar sashen ki, nan ne angarenki, ina son Allah kada ki biye masu ki ci-gaba da nuna min kyawawan halayenki masu kyau don Allah hakan zai sa na rage damuwar wasu abubuwan ban san rigima ban san tashin hankali ko da wasa." Yana gama maganar ya mi e tsaye ya nufi wata ofar ya bar mu a zaune a gun, su kam kowacce sai cika take tana batsewa. Hajiya Turai ta kalli Hajiya Tani ta kwashe da dariya tace, "Hajiya wannan fa ita ce kishiyarki, don haka sai ki tashi tsaye Ni kam yanzu na aje makamai na kan wani banzan kishi sai na abin duniya, don haka Allah Ya bada sa'a Yasa a fara zuba ruwan kishi da kyau cikin lokaci kuma, domin irin wa annan masu siffar munafukan Larabawan Makkah basu jin kira balle aiken dare sai kin tashi tsaye kin yi kamar kina yi sannan za ki samu galaba kan su." Hajiya Tani ta maka min harara tace, "Ni wallahi kyanta ma ke ban tsoro, munafukar kamar haihuwar indiya ta tsakiya kin san ance sun fi kyau, ko a cikin indiyawan. Amma maganarki na kan hanya wallahi ba zan kwance ba daga kuka sai gari ba tai min yanka baya ba, kin san ance an Lagos Mayun gaske ne idan suka kama kurwar namiji sai sun kai shi kushewa suke samun sa'ida a ransu." Ni dai tamkar an dasa ni haka nake zaune ina sauraren su ina kuma are masu kallo don tabbatar da cewa daga bakunansu maganganun ke fitowa ko ko ya akai ? Hajiya Turai ta zabga min harara tace, "Naji Alh na kiranki da Hajiya shi ya biya maki ku in Makkah ko?" Murmushi nayi domin ta tuno min da cewa nima naje Makkah tun ina budurwa ma. Sai dai bakina ya yi nauyin da ban iya bata amsar tambayar ta. Ganin ban da lokacin zama ina sauraren ba en maganganun da suke gaya min masu kama da barazana yasa na tashi na nufi ofar da aka tabbatar min da nan ne angarena. Sai dai tare muka tashi da su, ban ankara ba naga sun sha gabana, kafin nace me sun rufe Ni da duka. Sai da suka gaji sannan suka yale Ni, da jan jiki na shige angarena ina hawaye. Dare nayi aka aiko na fita cin abinci, kamar ince na oshi sai kuma naga rashin dacewar hakan tunda Alh ne da kanshi ya aiko kirana. ara gyara jikina don kar a raina Ni tunda naga matan gidan gasar kwalliya suke na fice ina duk addu'ar da ta zo bakina. Su duka suka zubomin ido kowacce fuska auke da tsana da kishi. Da sallamata na isa gun, kamar yadda na zata hakan ya faru, Alh ne kawai ya amsa sallamar da nayi. Shi na fara gaidawa sannan na bisu duka na gaida, amma babu wadda ta amsa min, shi ne kawai ya amsa gaisuwata yana ta murmushi. Kular gabana na jawo na bu amshin abincin ya daki hancina sai kawai na ji cikina baki aya ya shiga hautsinawa, kafin kace me, amai ya wanke jikina. Su duka suka ora hannu a kai suka furta, "Kambura'uban can kayyasa! Ba dai ciki ne da ke ba?" Mu ha u a page na gaba don jin koma miye gare ta. Taku a kullum Haupha [8/14, 9:28 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa