← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 133

Sashe 108

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da miji aki guda." Sakin baki ya yi galala yana kallonta, wai da ita a tunaninta da gaske yake mata wannan maganar? Cab ijam! Sai kace dai wanda ya yi auren dole ba auren so da auna ba? Janye bargon jikinta ya yi ya ce, "Af, na manta fa, amma bari na duba nagani ko kin isa kwana da miji ko har yanzu sai na yi rainonki." Tai saurin janyo bargon ta rufe jikinta, bayan ya riga yaga komai. Cikin muryar shagwa a tace, "Kai Prince, kai ne fa kace zaka barni sai bayan shekara biyu sannan na zama ar duma-duma." Dafe bakinsa ya yi ya ce, "Kai wannan baki baka kyauta ba da ka fa a wa Princess abin da bai yiyuwa, amma dai bari mu gani." Ya sake arin cire bargon daga jikinta. Ta kuwa ri e bargon ta fara yin kukan shagwa a, bai san lokacin daya ida hayewa ba ya janyo ta jikinsa yana bubbuga bayanta tana cewa, "Sorry Princess ba zan sake ba, kin ji, ban san kina damuwa ji nake kamar zuciyata ta fashe don tsabar tashin hankali." Lub tai jikinsa amshin turarensu na ara masu nisha i a zukatansu. ago kanta tai ta kalle shi ta zum ura bakinta ta sake fashewa da kukan shagwa Baki aya ta rikita shi ya rasa me zai mata sai kawai ya rungume ta ya fashe da kuka yana cewa, "Na gode! Na gode ! Na gode sosai Princess Allah Ya ban ikon ri e ki kan amana da gaskiya, Ya azurtani da yi maki duk wata bu ata taki Yasa na zama abin alfahari a gareki ." Jikinta yai sanyi ganin yana kuka yana magana wadda tasan da gaske daga can asan zuciyarsa take fitowa sai itama ta kama hawaye ta shige cikin jikinsa sosai tana cewa, "Don Allah ka daina kuka kana tada hankalinka a wannan rana mai daraja, a wannan rana mai alfarma, a wannan dare mai cike da farin ciki da nisha i tare da cikar dukkan burikanmu Prince. Insha Allah za mu rayu cike da farin ciki tare da walwala mai orewa har arshen rayuwarmu. Ina maka kyakkyawan zato wanda ya inga dukkan tunanina yasa na amince da kai ya tunzura zuciyata da jikina ara arfin sonka da aunarka da son aurenka. Shin Prince ka ta a tunanin zuwan wannan ranar a shekaru biyar zuwa goma da suka wuce ne?" Kanshi ya girgiza mata don kuka bai barinsa fa in ko da kalma guda. Ta cigaba da shafa sumar kansa tana magana cikin zubar hawaye, "Ka sani Prince ba kai ya kamata kai kuka ba, ba kai kuka ya kama ba, sannan ba kai fargaba ya kamata ta kama ba Prince nice, saboda kafin auren nan an fa a min maganganu da dama akan ka da halayenka wanda na runtse ido na toshe idanuna nayi kunnen uwar shegu da su na kafe sai kai duk da tarin masoya da Allah Ya azurtani da su kaine kawai ka zauna min a raina ka mamaye min duk wata jijiya da tsokar dake jikina. Prince ka zama jajirtacce mai kauda kai daga dukkan abin i mai aikata abin da za a yaba mai, wanda kowa zai dinga Allah san barka da halayensa." ara shigar da ita ya yi jikinsa sosai yana cewa, "Nayi maki al awarin hakan Princess don Allah kema ki dinga saka Ni a hanya idan kinga na kauce da in zaman kenan Princess kin ji?" Ya ago mata kai yana kallon idanunta. Itama cikin kukan take share mai hawaye yana cewa, "Nai maka wannan al awarin Prince nima idan kaga ina ba daidai ba ka zaunar dani cikin natsuwa da lumana ka gayamin abin da nayi ban daidai ba zan baka ha uri kuma na gyara kuskuren ba zan sake aikatawa ba." Sun jima suna yi ma juna al awarin zama da lafiya da taimakon juna da kulawa da juna har arshen rayuwarsu. Sannan labarin ya sha bambam domin Prince ya rikice mata shi ala dole bai san wane lokaci ya ce mata zai raine ta saboda shi idan tana gabansa manta wane hali ma yake ciki yake sam. Sanin cewar daman ranar suke jira, kuma shi ne matafin farko na samun nisha i a rayuwar aurensu da nuna godiya ga Allah Yasa ta saki jiki ta taimaka mai ta ba shi kulawa iyakar kulawa sai ga Prince na fa in "Princess nayi maki kyautar kaina, na baki komai nawa ke ce ma mai Ni ke Princess Allah ke ce kika aureni." Ita dai ba baka sai kunne domin abin ya girmi kunnenta don haka sai ta yi tsit kawai tana amsar sa on da kowace jijiya ke amsa daga gun Prince inta. Sai da taga yana neman yi mata rauni sannan ta dinga ture shi amma ina shi bai ma san me yake faruwa ba don zuwa yanzu ko magana ya kasa sai tashin nishinsa kawai da kalmar Princess kawai yake iya ambata. Sai da tai da gaske sannan ta ture shi ta mirgina gefen gadon ita ka ai tasan me take ji a jikinta. Shima sai ya yi lamo kawai yana hangen taurari na yawo a sararin samaniya yana ganin furanni na kai da kawowa ga network ta ko'ina na yawo duk a idanunsa. Sun jima kowa jiki ba arfi sannan a hankali ta tashi ta nufi toilet ta ha a ruwan zafi ta shiga kenan sai ga shi ya shigo, kunnenta ya kama ya an ja, tai ara ya ce, "Me yasa kika taho baki jira na auki ki ba? Kin manta da aikina ne aukarki nayi maki wanka na shafe ki ko'ina na kwantar da ke jikina ki yi barci ina baki labarai masu da i da saka barci cikin nisha i ba?" "Afuwan Prince, na tuba ba zan sake ba, sai dai kar ka manta nima wannan shi ne burina naga nayi maka komai na tsare maka komai na saka barci cikin nisha Rungume ta ya yi bai damu da kayan jikinsa ba yana cewa kenan wayau kike so ki yi min kenan komai kice ke ce za ki yi Ni kuma ba zan komai ba kenan? Gaskiya ba zan yadda ba Princess nima ina son naga ina taimaka maki gun ayyukan gidan nan dama kin gane komai tare zamu dinga yi." Zuwa yanzu su duka sun afka babin wankan tana yi mai yana yi mata, suna tsokanar juna ta hanyar watsawa juna ruwa. Sun auki lokaci suna wankan sannan suka fito ko wajen fitowar ma sai da suka saida halin don Jiddah cewa tai sai dai ya goya ta, shi kuma ya ce idan ya goya ta to zai sake mata garambawul don ya lura a zabure take sosai. Kan gado ya ora ta ya auki towel yana tsane mata jiki itama tana tsane mai nashi jikin, turare kawai ta fesa masu suka sake kwanciya ta shige cikin jikinshi sukai shiru kowa na tunanin yadda rayuwarsa ta juya Yau shi ne kwance cikin yanayin da yake gani a mafarki. Jiddah ta an bugi irjinsa tace, "Prince ka kwanta kai barci saboda gobe nasan jama'a za su zo da wuri kada barci ya hanaka amsa taya murnar aure gobe." Shafa ananan kitson kanta ya yi ya ce, "Ke dai Princess ki fa i gaskiya kada gobe na fita ace lallai na auri jaruma kwana guda har ta gama mai aiki ya ara tsawo." Sunne kanta tai cikin irjinsa tace, "Kai Prince ban da sharri dai, Ni ban ma san komai ba, don haka ba ruwana." Murmushi ya yi ya ce, "Ni kam kinga na sani domin Yau naga network kala-kala naga kuma sararin samaniya haka naga furanni na yawo a saman akin nan." Dariya tai, don tasan me yake nufi, don haka sai tace, "Ni sai ba ruwana don Malama ce kowa yasani." Shima ya yi dariya ya ce, "Kai ai Ni zan bada wannan labarin don tunda nake ban ta a amsar irin wannan darasin ba sai Yau gaskiya Malama kullum zan dinga amsar darasi daga gareki ba dare ba rana balle safiya." Dariya tai mai an sauti tace, "Duk ban san wannan ba, amma dai nasan an ban manyan kyauta kala-kala kuma gobe zan auki kyautuka na saboda na baka ta rabani da abuna." ago inda ta nufa don haka sai ya yi murmushi kawai yana sake jin wani sabon nisha i na zagaye ilahirin jikinsa ya ce, "Ai Ni da sau i tunda har nayi kyauta ke fa? Ai tsabar amsar sa on da nake baki ko kalma guda kasa furta wa ki kai sai santin kurma kawai ki ke wanda kowa yasan yafi kowane santi." Sun kai wajen arfe biyun dare ba su yi barci ba, haka ba firar kowa suke ba, firar kansu suke da kansu, sai tsabar tsokanar juna kawai. Washegari tunda asuba suka tashi ya yi alwala ya fito ta auka masallaci zai je sai kuma ta ga ya zauna ga alama ita yake jira. Ta dube shi da alamar neman arin bayani sai kuma tai murmushi ta isa inda yake ta kama hannunsa tace, "Mu je na raka ka ofa Prince yanzu an tada salla kar da ka makara." Wata ar harara-harara ya jefa mata ya ce, "Tab ina ango ina zuwa Masallaci ranar farko na angonci?" Dariya ta saka ta dube shi sosai tace, "Ai na manta ai Malam ango ashe fa bakai ba fita sai bayan kwanaki hu u ko?" "Ai da ina dake saurin fahimta don haka maza ki yo alwala mu yi sallah domin so nake na ara aukar darasi ya Malamata mai unbin ilimi da tarin hadisai." Sanin idan ta biye mai har gari ya ida waye wa basu yi sallar ba haka basu daina tsokanar juna ba yasa ta fa a toilet in tana murmushi. Suna gama sallar ta jashi suka koma barci duk da idan zata biye mai to darasin zai sake auka amma sai tai mirsisi tace barci ya kamata su yi tunda akwai gajiyar biki jikinsu. Ba don yana so ba, sai don bai san takura mata, kuma yasan tai namijin ari a jiya da ta auke duk bu atarsa ba tare da raki ba duk da abin ya koma mata sabo, don shi da ace bai san yaranta ba
Chapter 108 · 0% Book details