Sashe 68
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 34 Rayuwa kenan, komai na shi ya are, bai da ko sisi bai da abin sisin, shi ka ai ke rayuwa cike da unci da takura mai ta a zuciya. Ya rasa abin da yasa har gobe yake jin tamkar ya yi babbar asara ta wani jigo na rayuwarsa, amma ya kasa gane wace asara ce ya yi. Sau tari ji yake tamkar ya zauna ya bi diddu in rayuwarsa ko zai gane inda ya rasa wani gurbi amma ya kasa zaman da zai gane ina damuwarsa take. Shi da kanshi mamaki yake idan ya ji hawaye na zubowa daga idonsa, kamar shi wai yana kuka kan yanayin rayuwa! Tabbas abin yana da matu ar mamaki da aure kai kamar shi ace yana kuka da rana tsaka ba wani laifin da wani ya yi mai ko da wasa. To wa ma ya damu da shi da rayuwarsa a wannan lokacin? Ina ne yake da matsala ne wai? Ina ne yake neman ciko a rayuwarsa? Sam bai cikin farin ciki a rayuwarsa. Jin damuwa yake sosai a ransa, ji yake yafi kowa damuwa a wannan rayuwar. Hawaye suka zubo mai masu zafi da ciwon gaske bai damu ba daya goge kawai so yake ya ji fili a cikin zuciyarsa amma abin ya ci tura. Wahala yake sha ta ko'ina ba sau i, wuta yake amsa tamkar wanda ke gidan Yari da hukunci mai tsauri haka yake jinsa. Dama haka rayuwa take wai ga wanda yake cikin damuwa? Dama haka mutum ke jin tsananin tashin hankali da damuwa wa anda babu musabbabinsu sai dai ka wayi gari ka jika a cikinsu kawai baka san ya zakai ka fita ba kuma. Kamar ba shi ne Deenin nan ba mai nuna isa da ta ama ba. Kamar na shi ne wanda kullum sai ya saka Jiddah a cikin damuwa ba, Yau ga shi a damuwar da tafi wadda yake saka ta. Amma duk da haka bai ta a jin damuwa ba kan abin da ya yi mata, kawai auka yake wani yanayi ya same shi na rashin ku i wanda zai kauce, yana kaucewa kuma zai koma Deenin da wanda ke yadda yaga dama, mai neman duk yarinyar da ya so, mai shiga gidansa cike da izza da gadara, mai juya matarsa yadda ya so, mai nuna mata isa da iko, tai yadda yake so ko da bata so. Duk sanda ya yi wannan tunanin sai ya ji damuwar ta an ragu, ya ji tamkar komai zai dawo mai yadda yake so yake tsarawa kuma. BAYAN KWANA BIYU Duk abin duniya ya ishe shi, ji yake tamkar ya ora hannu akai ya kwarma ihu. Yaushe ne wai ya shiga cikin wannan rubibin rayuwar bai ankara ba? Yaushe ne ya fa a mummunan yanayin nan wai? Gaskiya akwai sake, bai ta a tunanin akwai irin wannan ranar ba a rayuwarsa. "Jiddah! Ya ambaci sunan cike da jan numfashi mai auke da damuwar gaske. Tun da ya saki Jiddah yake jin tamkar ya rabu da aya ba kamar da ya ha a mata da gayyar yaranta, sai yake jin damar walawarsa ce ta zo, sai yake jin tamkar shi in dama wauta da kasada ce suka tunzura shi har ya auri Jiddah ya saki jiki har ya haihu da ita. Sai dai kuma ko bayan rabuwarsu sai ya fahimci cewar Jiddah na matu ar taimaka masa wajen sutura, abinci, ku in kashewa, saboda bayan rabuwarsu ne da shekara mahaifiyarsa ta rasu, sai ya sake gane cewa duniya budurwar Wawa ce, domin sai wani munafikin talauci ya addabe shi ya kanainaye shi ya hanashi rawar gaban hantsi. Lokaci guda duk an matan da yake ta ama dasu suka guje shi, domin bai da abin basu, ita kanta Safiya wata uku kenan idan lissafi bai wace ma shi ba da mijinta ya iske su tare cikin akinta suna abin da suka saba, ya tara mai mutane sukai tai masu tofin alatsine ya saki Safiya a gaban jama'a ya kira Mamanta ya gaya mata abin da ya faru, nan take ita ma tace ba dai gidanta ba Safiya hakan yasa ta shirya kayanta tai tafiyarta bai san inda take ba yanzu. Aure yake so amma ya faskara gare shi, duk inda ya je neman aure ba a ba shi, kai tsaye ake gaya mai ba mai iya ba shi yarinyarsa don bai ri on aure. Sosai abin duniya ke damunsa yadda bai oyuwa daga idanun mutane,duk wanda ya ganshi tabbas yasan yana amsar wuta a rayuwarsa. "Jiddah ka ai ce zata iya zama da Ni, t bbas mutane sun fa i gaskiya ke ka aice za ki iya jure rayuwa da Ni Jiddah kina ina ne?" Hawaye suka zubo mai "Ban ta a tunanin za ki iya samun matsayin da zan tuna da ke ba, bayan na rabu dake ba Jiddah. Yau na yarda da cewa duk abin da ya baka tsoro wata rana shi ne zai baka tausayi, domin hakan yake faruwa a tsakanina da ke Jiddah. Tabbas Ni ne abin tausayi a wannan karon yayin da kece abar tsoron." wabcinsa ya iske shi zaune ofar gidan duk ya gwaguye daman kowa yasan cewa Jiddah ita ke gyara gidan idan ya samu matsala, ita ce ke komai na gidan, tun barinta gidan ya fice hayyacinsa kamar yadda maigidan shima ya fita hayyacinsa. Cike da zolaya ya dubi Deeni ya ce, "Malam Deeni ya garin ne naga ka zauna a nan kayi tagumi kamar mai damuwa, na shiga gida na fito na sake iske ka a nan zaune a yanayin dai, ko dai bikin ya matso ne don naji kamar ana maganar aurenka ya matso ko?" Cike da takaici Deeni ya dubi ma wabcinsa ya ce, "Ai wannan karon ma auren ba zai samu ba, an sake samun munafukai sun shiga sun fita sun raba auren." Cike da nuna alhini ya ce, "Ashsha! Ashsha! Magana ba tai da i ba kau, to me zai hana ka maido matarka mai ha uri da sanin ya kamata ne Deeni?" Wani irin takaici ya ziyarci zuciyarsa ji yake tamkar ya maido baya yanzu, tabbas da babu abin da zai sa ya saki Jiddah ko da kuwa ita ce ta nemi sakin daga gare shi. Ganin ya yi shiru ba mamaki yana hasko wautar da ya yi ne a baya yasa ma wabcin ya wuce yana ara yabon halayen tsohuwar matarsa Jiddah. "Na shiga uku ni Deeni! Ya zan yi ne wai? Ina kike Jiddah? Tabbas zan maida ki akin mijinki ko da hakan na nufin ke baki aminta ba, nasan tabbas wa anda suka ban ke da farko a wannan karon ma za su sake ban ke Jiddah." Sai yanzu murmushi ya wace mai, har ya samu warin gwiwar tashi ya koma cikin gidan ya sauya kaya ya nufi gidan Kakannin Jiddah. Ko da ya isa gidan kamar yadda ya zata ba kowa sai Kakarta dake zaune tana sa ar hannu, ya gaidata ta amsa kamar bata so, ya sadda kan shi asa ya ce, "Dama na zo ne in gaya maku cewar na maida aurena da Jiddah, zan sake biyan sadaki ta koma akinta ta cigaba da kulawa da yaranta." Kaka ta dube shi she e ta watsar ta ta e bakinta ta cigaba da abin da take yi, dukkan alama bata da lokacinsa. Ya sake maimaita mata abin da ya ce da farko, sai a lokacin ta kalle shi cike da takaici tace, "Amma kai baka da hankali ko? Gidan uban wa naga wata Jiddah balle ka gaya min wai zaka maida aurenka? To daman can Ni nace ka sake ta ne? To tun wuri ka tashi ka ban waje domin Jiddar da ka sani ba ita bace yanzu. Wannan ta girma tasan ciwon kanta ko Ni shakkar yi mata wani abin nake yanzu balle kai da ko takalmanta bata ba umarnin taka ka ba. Don Allah maza ka tashi kaban waje ai duk naji abin da kai mata da tana gidanka, don haka ban da ta cewa Ni kan aurenka da ita, tana ma Kano bata garin nan sai ka bita can ka gaya mata zaka maida ta akinta." Daram! Gabansa ya fa i, bai za ci zai samu damuwa da tsohuwar ba, saboda lokacin da ya zo da maganar auren Jiddah tana ta saka albarka tana cewa ko iyayenta na wajen uwa basu yadda ba ita ta amince don haka aure ba zai fasu ba. Amma ji yanzu yadda tai mirsisi ta nuna bata ma san shi ba, wai bata ma iya lan wasa Jiddah take nuna mai! Jiddah da ya sani da gudun fa a da taka-tsan-tsan da abin da zai ja mata matsala da mutum ce take nufin yanzu bata juyowa? Yarinyar da bata da ra'ayin kanta sai wanda aka bata umarnin bi? Tabbas zai jira ta dawo ya tunkare ta kan shi ya gaya mata ya maida ta akinta yasan ba zata mu sa maganarsa ba, tunda daman can bata iya yi masa ko da musu ne balle ya ce mata umarni ne da gudu take aikatawa. Kaka ta sake dubansa fuska ba walwala tace, "Kai Ni don Allah maza ka tashi ka ban waje na gaji da ganinka ma, sai har ewa nake a sa ar na kasa daidaita zarena." Jiki sanyi alau ya tashi ya fito, amma zuciyarsa na gaya ma shi ya jira Jiddah kawai, ita ce kawai wadda zai sake ma maganar maida aurenta ba wasu ba. Don haka sai ya aje maganar gefe yana jiran dawowar Jiddah daga Kano kamar yadda ya ji ance tana Kanon. Sai dai duk lokacin da yake zaune ko tsaye ko yana tafiya sai kawai idonsa ya dinga hasko mai rayuwar Jiddah a gidansa. Ya dinga hasko yadda take kallonsa idonta cike da hawaye idan ta iske shi da wata a gidan. Ya rasa yadda zai ya daina hasko fuskarta cikin damuwa ko hawaye. Wasa-wasa Deeni ya tsinci kansa cikin wata irin zazzafar aunar Jiddah mai zafin gaske. Duk sanda ya zauna ya hasko ta tana kuka shi ma sai ya