← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 133

Sashe 119

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai masu gadi su biyu ban sha wahala ba gun shiga saboda guda ya sanni sosai ta silar wata shari'a da nayi mai kan wani yaro da aka sace mai nabi mai ha insa don haka cikin natsuwa suka bu e min ko'ina na shiga nayi bincike na samo sunayen duk masu hannu a cikin lamarin. Sannan a cikin ofishin dai naga hoton A'isha da shi an majalisar na auki hoton na tafi da shi kai tsaye gidan shi na sha atawa yana ciki kuwa na iske shi na zauna na fito da hoton A'isha da sauran gan in su na an kwangilar waya na fara da kora mai bayanin laifinsu da ara mai da cewar shi ne babban mai laifi wanda ke taimakawa ana fitar da wayar daga asar nan zuwa asashen waje don haka sunansa ne a farko kafin nasu, sannan na nuna mai hoton A'isha da Abubakar da hoton yaronsu na gaya mai yana bin matar aure matsayinsa na babban an siyasa a asar nan wanda idan wannan maganar ta fita zai rasa abubuwa da dama, irinsu siyasarsa, mutuncinsa, ba mamaki har da iyalansa ma. Hakan yasa ya ru e yake ce min wallahi bai sani ba, ya auka bata da aure sai a satin nan ne yake ganin abin da ke faruwa tana Shari'a da mijinta wai ya kashe mata ar aikinta bayan ya yi mata ciki, to da yake kin san mu an siyasa bamu da yadda tun ha uwarmu bada jimawa ba na sai mata wata sar ar zinari mai tsadar gaske na saka mata Camera a cikinta na saka mata nace kada ta sake ta cire ta sai zan sake mata wata, tunawa da hakan yasa na kunna Camerar don ganin meke faruwa a nan ne naga wannan abin da ya tada min hankali watau kisan da tai ma ar aikinta da kiran da taima mahaifiyarta. Ya ban aukar na kalla, na ri e na yi mai godiya nace sai mun ha u a kotu, duk da ya so na cire shi a lamarin nace ba zai yiyu ba saboda ya jima cikin manyan siyasar dake gur ata asar nan. To kin ji yadda akai na samu shaidun dana gabatar a wajen Al ali Yau." Abubakar ya sake yin godiya ya tafi cike da jin nauyin abin da yai ma Jiddah a baya Yau ga shi ita ce ta cece shi ta watar mai ha insa a lokacin da kowa ya yale shi ya juya mai baya. Prince ya dubi Princess insa ya ce, "Zan je gun Baba mu yi maganar zuwa kai ku in aurenmu don wallahi na gaji da wannan ja min ran da kike ko da yaushe so nake na ganki kusa da Ni ga Ni gaki." Alawiyya ta goya mai baya tace zata kira Baffa ta gaya mai yanzu kuwa gwara ayi hidimar a wuce gun haka nan. Da dare Jiddah ta gayama Hajjo ita ma ta kira Maman Jiddah ta gaya mata, tai ta addu'a tana arawa domin ta gane yaron da akace yana son Jiddah tabbas bai da kwaramniya da gani yana da hankali yasan me yake yi kuma don ba laifi yafi Deeni shekaru. Alawiyya ma ta kira Baffa ya ce sai ya ji daga bakin Jiddah sannan zai yadda don ba auren dole zai mata ba kuma ya zatai da karatun da take yi? Ya kira ta ya tambayeta ta amsa mai da cewa Mustapha ya amince ta cigaba da karatunta ba zai dakatar da ita ba ko bayan sun yi aure hakan yasa Baffan jin da i ya amince kuma sai dai ya ce ya tura can Jalingo shima zai je can su ha u da yayyen mahaifinta su amshi ku in auren. Ba haka ta so ba, so tai shi ya amsa ya zama waliyinta kawai a yale su tunda ba wanda yasan da zaman ta a duniyar daga su har mahaifin nata amma tunda ya ce haka sai ta amince sai dai umarnin arshe ne ya sosa mata rai da ya ce ta shirya ita da Alawiyya suje Jalingo ta gaida iyayenta kafin ai auren don ba lokaci za a saka ba mai tsawo. Ba yadda zatai haka ta amsa da to duk ba da i a asan zuciyarta. Ta shaidawa Prince da Hajjo da Alawiyya yadda su kai da Baffa su duka sun goyi bayan hakan don haka ita ka ai ce abin baima da i ba suka saka ranar tafiya Jalingo nan da kwanaki biyar. Sai kuma wata sabuwar fitina ta fita na yadda mata da dama ke sallama har gida suna gaya mata cewar karda ta sake ta auri Mustapha yadda take haka idan ta aure shi ta ci baya kuma sai tayi nadama tayi danasanin aurensa kowace mace tana kafa mata hujja da tarin auren da yayi a baya da yadda yanzu gidansa yake ba zaman lafiya wai bai kula da mata kashe mace yake komin diri da kyanta idan ya aureta aryar daga waje ne kawai tana shiga gidan ta zama sorry. Ita kuma duk lokacin da aka kawo mata zugarshi sai taji ya bata tausai amma dai Hausawa na cewa ana tauna tsakuwa ko dan aya taji tsoro sai ta kira shi a waya taita fushi tana cewa ta gaji da surutun mutane kada fa ace da gaske ne. Bawan Allah zai ta lallashinta yana rantse mata kan idan ya ci amanarta Allah ya saka mata kawai hassada ce ake mai don zai aure ta. Ni da Bilkisu awata sai komai ya lalace domin na fahimci munafuka ce tana son samun magana daga bakina don ta gayama matarsa Maryam sai kawai na rufe ta na fice daga sabgarta amma sai ta dinga biyoni har gidan Hajjo tana son bugar cikina don taji yadda muke ciki da Prince, Ni kuma sai na i gaya mata komai sai ta koma yi min bincike a waya tana duba sa onni da hotunan da mukai da shi, hakan yasa na fito na gaya mata cewar mun ata da Mustapha yanzu har na fitar da wanda zan aura a Kaduna bu ar bakinta sai cewa tai, ai wallahi daman nasan kin fi arfinsa yo me za ki yi da Mustapha Allah na tuba? Ai ba ajinki bane ba ya je ya ji da kansa ma da hayaniyar gidansa ina shi ina ke ban da neman magana? Ai daman nasan yaudararsa kawai kike don ki yagi abin da kika yaga ki kama gabanki don bai da wayau kashe ma mata ku i kawai yake suna mai wayau don ba mai iya aurenshi ta kawo kanta gidanshi duk masifa da azanta ta kashe ta." Tun da naji haka daga bakin Bilkisu sai nayi mata dogon layi mai kyau na saka ta ciki kawai na rufe. A farko tana gaba wajen cemin nayi dacen miji domin bai da matsala har cewa tai yafi mijinta kula kawai mata ne bai dace ba amma mutum ne har da ari Yau kuma ga abin da tace min saboda ta ha e kai da matarsa bata son na shiga gidansa da sunan aure. Sai na sauya mata ko a fuska na daina ko doguwar magana da ita kawai na kame kaina na daina bata ko wayata duk da cewar tana tambayata . Sai kuma suka tsiri turo min yara su gani ko Mustapha na gidan Hajjo sai ina zaune naga yara na le e duk na tarkata su na watsar kawai nasa a raina aurene dai nice mai yinsa don haka zan auri Mustapha ko da ace munanan halaye n da ake ambata yana da su to tabbas ina da tabbacin zan iya sauya shi indai da gaske yana sona nima ina sonsa to sauya shi ba wani abin ku zo ku gani bane ba. Tunda nayi rayuwa da Deeni wane namiji ne ban iya rayuwa da shi? Ban ganshi ba zan iya rayuwa da kowane irin namiji a yanzu Ni. JALINGO Tafiya mai da i a gunsu Alawiyya da Prince Ni kam murna aya nake zan je na ga Mamana ban da wannan ba wata murna da nake sai kawai kallon titi, lura da hakan da sukai ma yasa sai fira su ke su ka ai basu saka Ni don hankalina ba kansu yake ba ya koma a can shekarun baya na koma tunano rayuwar da nayi a baya mai cike da alubale kala-kala ko ince iri-iri a cikin garin Jalingon. Har muka isa fuskata ba walwala gidan Mamana muka fara sauka da yake tasan da zuwanmu ta shirya mana abinci mai rai da lafiya naji da in yadda na ganta cikin aminci da natsuwa bata tare da damuwa ko takaici hakan yasa na sake sakin fuskata na ji da i ya ziyarci zuciyata baki aya har ma na ware ana ta fira da ni kamar ba nice mai ha e ran nan ba sam ba fara'a kan fuskata ba. Daga nan gidajen dangin Mamata muka je suka ga wanda zan aura sunata addu'a suna nuna jin da in su kan auren da zan yi kuma ga alama duk sun yaba da za in nawa. Sai daga arshe muka nufi gidan Babana tun daga nesa naga gidan duk ya sauya kamar ba shi ba, haka mu kai fakin muka sauka. Yana zaune yana jan casbaha a hannunsa duk ya rame ya koma kamar ba shi ba, ga alama ma bai da wadatar lafiya, a hankali muka isa inda yake muka gaida shi amma abin takaici abin mamaki Alawiyya kawai ya gane ya zabura yana ro onta ta kaishi inda zai ga Jiddah don Allah. Kaina na asa ina kukan takaici aka nuna mai Ni matsayin iyarsa wadda ya manta da ita wadda bai sonta wadda bai damu da ita ba ita ce gabanshi tsugunne bai gane ta ba. Ya kama Ni ya ri e yana kuka yana neman afuwata sai kuma tari ya taso mai kamar zai sume hakan yasa zargina ya tabbata bai da lafiya ganin mutane sun fara taruwa yasa muka shiga cikin gidan baki aya. Komai na yadda yake yadda na sanshi yadda na barshi sai dai tsufa kawai da gidan ya yi na rashin fenti . Mutanen gidan suma kowa na nan sai ara manyan ta da sukai ba kunya ba tsoron Allah
Chapter 119 · 0% Book details