Sashe 87
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 40 Wayar na kan kunnenta hawaye na tsiyayowa daga kan fuskarta, tana son yin magana amma bata iya furta ko da kalma guda, to me zata ce ma wai? Tana jin rishin kukansa a kan kunnenta yana cewa, "Jiddah kin tafi kin bar Ni cike da kewarki, na rasa ya zan yi na rasa me ke min da i, don Allah ki dawo gareni Jiddah tun kafin cutar aunarki ta nakasar da rayuwata." Ba wai kukansa yasa ta kuka ba, a'a kuka take na jin cewar saboda ita wani ke kuka, ashe har akwai wanda zai mata irin wannan soyayyar da zai zubar da hawayensa saboda ita? Ashe har ta kai matsayin da kamar Mustapha mai aji da kyau da ta ama zai zubawar da hawaye saboda sonta? Tabbas wannan abin kuka ne na farin ciki gareta, dole ta gode wa Allah da wannan matsayi da ya kaita wanda bata ta a tsintar kanta a cikinsa ba. Mustapha da gaske kuka yake sosai kamar wani aramin yaro, kuka yake har yana jan majina kuma ba don yana son kukan ba kawai ji ya yi kukan ya zo mai da arfin gaske lokacin daya kira ta a waya. arya son ta yake sosai son da ko a tarihi bai ta a yi wa wata yarinya irinshi ba. Jiddah ta zama wata katangar saka shi farin ciki a rayuwarsa yanzu gani yake tamkar zai rasa ne nisan da tai mai, yana ji a jikinsa rasa Jiddah wani babban alubale ne a rayuwarsa kuma ba zai ta a cika burinsa ba samun irin rayuwar da yake fata da mafarkin samu na zaman aure ba. Ya ja ajiyar zuciya ya ce, "Jiddah don Allah ki taimaka ki amsa min ko da sau aya ne cewa kina so na don Allah! Na rantse da Allah na rasa farin cikina da annurin zuciyata tun da na ganki za ki tafi har zuwa yanzu ban cikin farin ciki Jiddah. Shin Jiddah ko da sau aya baki ta a jin cewar na cancanci na so ki bane ba ko me? Na san cewa Jiddah mutane da dama ba za su so wannan ha in ba, amma don Allah ki taimaka ki da e kunnuwanki daga duk wasu surutu da za ai maki ki taimake Ni ki so Ni Jiddah don Allah! Magana yake cikin kuka sosai don wani abin ma bata san me yake cewa ba. Ita kuma sai kukanta ya tsananta ji take kamar bata kai ba, kamar bata da matsayin kamar bata da ajin da namiji kamar Mustapha zai zauna ya dinga mata kuka ba. Tabbas Allah abin godiya ne ya za e ta a cikin dubbun mata ya dasa ma maza uku sonta wa anda ko a mafarki bata ta a tsammanin hakan ba. Tabbas bata shirya soyayya ba, idan ma soyayya za tai to ba zai soyayya da Mustapha ba, haka ba zatai soyayya da Dr Faisal ba shi ma Kawu Mansur ba zata iya aurensa ba, a takaice dai su duka babu za in zuciyarta a cikinsu. Ita tana ta tunani yayin da shi kuma yake ta kuka kamar wani aramin yaro yana ambatar sunanta. yar ta samu ta daina kukan ta gyara muryarta tace, "Ni ban ce ban sonka ba, amma dai ba yanzu zan yi aure ba, saboda yarana nike kula da su don haka ban zaci zan iya aure ba duk don wa annan shekarun ba." Mustapha ya ja majina ya ce, "Na yarda da ba yanzu za ki aure ba amma ina son don Allah ki min al awarin za ki aure Ni duk lokacin da kika tashi auren don Allah Princess." Ta rasa ya zatai mai, akan me zai wautar fa awa mai mata har uku? Gaskiyar magana abin ba zai mata kyau bata san tai aure inda damuwa zata cigaba da bibiyarta tafi son tai aure inda zata zauna cike da farin ciki da aminci. Idan haka ne kuwa to karda ta kai kanta gidan kishiya don haka ha in nan ba zai yiyu ba gaskiyar magana. Mustapha jin ta yi shiru ya ce, "Ina son don Allah ki amince min Jiddah nayi maki al awarin zan kula da ke zan baki duk wata kulawa zan tabbatar da cewa kina cikin jerin mata masu farin ciki da rayuwar aurensu nayi maki wannan al awarin Princess." Kamar yana gabanta haka take girgiza kanta, akan me zata amince da soyayyar mai mata? Me ta tsinta a rayuwarta da har zata kai kanta cikin mata kawai ta saka kanta a uku da ranta da lafiyarta a lokacin da take da madafan ikon gina rayuwarta da rayuwa mai inganci a inda take so yai mata kuma? Tabbas gidan Mustapha yafi arfinta ba zata iya zaman kishi da matansa ba sai dai ya yi ha uri. Don haka tace cikin sanyin murya, "Kai ha uri amma ba zan iya zama cikin matanka ba gaskiya." Ta kashe wayar kafin ma ya sake cewa wani abu. Mustapha yabi wayar da kallo yana jin zuciyarsa na zafi kamar zata kama da wuta. Me yake son faruwa da shi ne? Me ye aibunsa don kawai bai dacen mata ba sai a auka laifinsa ne ba laifinsu ba? Me yasa Jiddah zata kasa fahimtar shi? Me yasa mutane suke kasa yi mai uzuri ne? Kuka yake sosai yana fyacewa ji yake tamkar ya mutu ma kowa ya huta tun da babu mai masa uzuri babu mai fahimtar sa balle ya fahimci halin da yake ciki. Haka ya jima a yanayin tamkar ba shi ba, duk wata jimammiyar damuwarsa sai da ta dawo masa sabuwa, ya dinga tuna yadda Salim ke kwatanta mai wata rana sai labari to wai yaushe ne zai zama labarin? Yaushe ne ma komai zai wuce a gunshi to? Hawaye yake yana arawa, tabbas Jiddah ita ce maganin matsalarsa idan ya tasa ta zai ara shiga cikin matsalar da tafi ta baya ne nesa ba kusa ba. Amma ba zai asa a gwiwa ba, zai dage iyakar dagewa zai jure iyakar jurewa ba zai gaza ba har sai ya samu cikar burinsa watau auren Jiddah. Deeni Yana zaune kamar an dasa shi, yana tuna ranar da abin ya faru ranar da ba zai manta ba, ranar da kunya da nadama tare da takaicin abin da ya aikata suka sa ya kasa ko da aga halshensa balle ya furta ko da kalma guda ce. A hankali ya dinga hasko yadda abin ya faru a idanunsa. Yana zaune a akin da aka ware mai bayan ya warke daga ciwon damuwar da ya so ya maida shi mahaukacin arfi da yaji sai ga Likitan ya shigo da sallamarsa ya ce, "Yawwa ga wadda tai ma magani ta zo kamar yadda ka bu ata tana son ku gana." Cike da fara'a ya amsa da cewa "To Likita na gode sosai mu je na ganta." Suka tashi Likitan na gaba yana bayansa suka fice daga akin zuwa office in Likitan. Tana zaune fuskarsa auke da tabarau ta ora afarta aya kan aya tana duban wasu hotuna dake hannunta. Fuskarta auke take da murmushi ga amshin turaren ta daya kama office in baki aya. Da sallama suka shiga su duka har Likitan, bayan shigarsu ne Likitan ya nemi ya fice amma sai ta dakatar da shi tace, "No Dr zauna ai komai a gabanka ai ba wani abu bane sabo, abin da aka saba ne dai kawai." Hakan yasa Likitan zama kan kujerarsa ya gyara tabaran fuskarsa ya yi shiru. Kujerar dake kallon kujerarta ta nuna mai ya zauna, bayan ya zauna ta dube shi sosai fuska cike da fara'a tace, "Malam Deeni kenan, kana lafiya? Ina fatan ba abin da ke damunka a halin yanzu? Nufina baka da wani oyayyen ciwo a cikin jikinka?" Cike da jin da i ya amsa mata da cewar, "Ai gaskiya jiki alhamdulillah komai ya yi min lafiya ban da wata damuwa ko matsala Hajiya, sai dai ince Allah Ya saka maki da mafi alheri kan abin da kikai min na gode sosai da sosai Hajiya." Dariya tai irinta manyan nan ta mi a mai hotunan wajenta, tana cewa, "Ko zaka iya gane min su waye a cikin wa annan hotunan Malam Deeni?" Amsar hotunan ya yi yana dubawa, zumbar ya mi e tsaye yana arewa hotunan kallo yana sake zaro idanuwa alamar mamaki sosai ya ce, "Ina kika samu wa annan hotunan, ai wannan matata ce, wa annan kuma yar ana ne don Allah suna ina domin nemansu nake na maida matata da yarana guna mu cigaba da zama kamar baya." in ciki da takaicin kalaman sa yasa Alawiyya auke shi da mari tana cewa. "Wannan da kake gani ita ce Jiddah yarinya mai ha uri da natsuwa mai cike da tsoron Allah macen da bata auki rayuwar duniya da zafi ba, ta zauna da kai duk da bakai ne za in ta ba, tai maka ladabi duk da azabtar da ita da kai, ta zame maka macen rufin asiri duk da tona mata nata asirin da kai, tai maka sutura duk da sace mata nata da kake, ta ci da kai duk da azabtar da ita da yunwa da kai, arshe ta kare maka mutunci duk da watsar mata da nata mutuncin da kai. Deeni ina son ka sani Jiddah yanzu tafi arfin ka tafi arfin duk wani wanda ya shafe ka don haka kai shirin amsar tukuicin abin da kai mata a yanzu ba sai gaba ba. Deeni ka sani tun da nake da Jiddah ban ta a ganin tayi farin ciki ba saboda kai ne wanda ya kamata ka zame mata farin cikin amma sai ka zame mata ba in ciki wanda hakan yasa take jin tsanar kowane namiji a zuciyarta har ma bata maraba da aure a rayuwarta. Deeni ka sani ka yi wa kanka asarar mace mai mutunci da kamala mai ri e sirrinka mai ha uri da babunka mai farin ciki da samunka mai neman hanyar zamanka mutumin kirki a rayuwarka. Shin Deeni wane irin tukuici ka samu na bin matan da kake