Sashe 127
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 44 *Don Allah ku yi min uzuri, abubuwa ne sun yi min yawa, ga karatu ga sauran hidimomi, don Allah ku dinga saka mu a addu'arku ma saboda muna gab da fara Exam.* Ya dubi Hafsat da muryar ban tausayi ya ce, "Wai me yasa ke baki san a baki ha uri sau aya bane ba Hafsat? Tun jiya nake abu guda amma kin i saurarata shin ya kike so nayi maki ne? Komai nawa ya tsaya kanki, na rasa me ke damuna na kasa natsuwa na kasa fahimtar kowa da komai amma kin kasa min adalci ki fahimceni duk da na gaya maki ban yi mata kayan aki ba Ni, asalima ban da ku in da zan yi wannan hidimar ma ni a zahirance, Jiddah nada sana'arta kuma aiki take yi ga iyayenta tsaye kanta don haka bata da matsalar kayan aki wallahi don Allah ki daina kama maganar mutane wadda bata da amfani sai ha a fa a kawai." Ta dube shi ta ta e bakinta bata ce komai ba, don ba abin da zata ce mai in. Sai wajen arfe biyun rana ta bar shi ya fice gidan, cikin sauri ya nufi gidan Maryam don yasan itama tana can ta cika fam, don ma bata da tabi'ai kira da yanzu ta kira shi tunda yasan ba kayan cefane a gidan. Yana zuwa akinta ya shiga tana kwance ko ago kanta batai ba balle ta amsa sallamar da ya yi. Kai tsaye wajen gadon ya nufa ya ra a ya zauna yana tambayarta "Baki lafiya ne na ganki a kwance?" Kamar jira take yai mata tambayar tace, "Ni dai nasan mutum bai isa ya kashe Ni ba idan ajalina bai zo ba, don haka duk wani mugunta da rashin adalcin mutum ba inda zai kai Ni kuma ban yafe ba indai da ha ina wallahi." Shi dai baice komai ba, ya gode wa Allah da abin ya tsaya iyakar nan ma, don haka cikin sauri ya fita ya yo cefane mai kyau ya kawo har da an canji duk dan ya samu ya wanke mata zuciya daga fushin da take ta yi. Ko da ya yi sallah nan ya dawo ya ci abincin zai tafi gidan Jiddah kenan Hafsat ta kira shi tace tana son ganinshi, don haka sai kawai ya nufi can kai tsaye bai waiwayi gidan Jiddar ba. Ta jima cikin yanayin, wanda ko bata tambaya ba tasan alamar hawan jininta ne ya tashi, hakan yasa ta dinga jero addu'o'i kala-kala daga kwancen har dai ta samu ta dawo hayyacinta. Zuwa yanzu hawayenta ya afe sai ajiyar zuciya da take yi akai-akai. Ta yi fayau da ita ta rame kamar wadda tai ciwon wata guda. A hankali ta tashi tana dafa bango ta samu ta isa akinta tai alwala tai sallah daga zaune tana gamawa ta ora da karatun Alqur'ani mai girma na tsawon lokaci, sannan ta samu ta haye gadonta ta kwanta tana nishi don wani azabebben ciwon kai ne ke damunta ga gidan taji ana bugawa, kamar kar ta tashi ta samu ta kwanta sai kuma ta tuna da ko maigidan ne ya dawo, don haka ta samu da yar ta tashi tana dafe da kanta ta fice zuwa ofar ta bu anwarsa ta zo suka shigo tare suna gaisawa, da kanta ta fahimci Jiddah bata lafiya don haka tai mata sannu tace bari ta le a ta samo mata magani, tunda ba kowa gidan. Bayan ta fita Jiddah tai murmushi tana hasko lokacin da take gidan Deeni Maman khairat ce ke bata magani idan bata lafiya ta kai ta asibiti Yau kuma ga anwar Mustapha ce ta zo ta iske bata lafiya ta tafi neman mata magani ko ina maigidan yake Allahu a'alamu. Har ta dawo Jiddah na inda ta barta , haka nan ta sha maganin ba don tasan zai mata komai ba sai don ta nunawa Asma'u taji da in taimakon siyo mata maganin da tai. Ance mutum rahama ne sai ga shi zuwan Asma'u da yaranta biyu yasa Jiddah ta ji dama-dama amma babu kalma guda ta fita daga kunnenta wadda Prince ya gaya mata. Asma'u nan ta yini har bayan la'asar sosai sannan ta tafi tana addu'ar Allah Ya baya lafiya. Asma'u na tafiya sai damuwa ta sake dawo mata sabuwa dal a leda, tunda Prince ya fice arfe shidan safe bai sake dawowa ba har yanzu da za ai magriba, haka bai kira ta ba,bai turo mata sa o ba, ita ta tura sa on ba amsa ta kira ya ce bai son kiran nata. Wayarta ce tai ara ta wajen aiki, sai taji sanyi a ranta don haka ta auka don jin abin da akai, duk da ta auki hutun amarci. Bayan sun gaisa ne ake gaya mata wata mata ce ta zo tace dole ita take son gani kuma sai kuka take ta i magana da kowa. Hakan yasa tace a ba matar wayar . Tana jin kukan matar sai nata hawayen suka dawo mata ita ma, ta daure taima matar sallama. Matar ta amsa ba tare da ta daina kukan ba, zuwa can tace don Allah son ganinki nake ki taimaka min don Allah kamar yadda Allah Ya taimaka maki don Allah Jiddah." Hakan yasa zuciyarta hasaso mata inda tasan mai wannan muryar, tamkar ta jima da sanin muryar ji take ma kamar tayi rayuwa da mai wannan muryar don haka cikin sanyin jiki tace, "Ba shi wayar zan mai magana." Matar ta mi awa wanda aka ce ta ba wayar hannunta na kyarma. Jiddah tai ajiyar zuciya tace "Kasa a kawo ta gidana zan turo maka address in, kasan hutu nake kuma ban fara fita ba." Ya amsa da "To Ranki ya da Ta tura mai sa on adireshin gidan ta aje wayar tana aniyar zuciya. Yana zuwa ya iske Hafsat ta shirya ta ci kwalliyar gaske abin da bai saba gani ba a gidansa tayi ba, ta dube shi fuska ba walwala tace " orayj zaka kaini gun buki yanzu, daga can sai mu biya ta Kurna babban layi ina da suna." To kawai ya ce mata suka kama hanyar zuwa, sai da ya kaita duk inda tace yana jiranta a ofar gida sannan ya maidata gidansu ya nufi gidan Jiddah. Tana kwance kan kujera ga alama barci take, gidan baki aya sai amshi yake, komai tsab sai karatun Alkur'ani dake tashi a hankali mai da in saurare. Tayi nisa a cikin tunaninta don haka bata ma san ya shigo gidan ba balle akin duk da taji amshin turarensa amma sai ta i amincewa da shi ne ya shigo in domin aikin da ta yini yi kenan bayan tafiyar Asma'u na jin kamar shi ne ya shigo sai ta samu da yar ta tashi sai taga ba shi ne ba kawai sa ma ranta ne. Bai jima da shiga ba, sai taji sallamar wadda take zargi wadda bata ta a tunanin za su sake ha uwa ba, wadda take jin ba zata iya yafe mata abin da tai mata ba a rayuwarta . Jin mace ta shigo tana kuka yasa Mustapha fitowa daga akinsa ya tsaya bayan labule don ya auka ma Jiddar ce ke kukan. Jiddah ta tashi zaune da yar ta dubi Safiya duk da sauyawar da tai hakan baisa ta kasa ganeta ba, sai dai ta kasa furta mata ko da kalma guda sai kallonta kawai da take. Safiya ta zo gaban Jiddah ta tsugunna ta kama afarta tana cewa, "Don Allah don Annabi Jiddah kar da ki tuna baya ki yafe min ki taimake Ni don Allah Jiddah domin nasan ke in ta dabance kina da yafiya, kina da tausayi sannan baki da ri on abu don Allah Jiddah ki yafe min duk abin da nayi maki a gidan Deeni don Allah. Ko dan darajar sauyin rayuwar da kika samu Jiddah, ji bi gidan aurenki kin yi auren soyayya mijinki na sonki bai san abin da zai ta a ki, bai iya nisa dake komai kike yana damarki shin Jiddah ko wannan sakayyar ba zata sa ki yafe min ba? Nasan cewa nayi matu ar tasiri gun hanaki zaman lafiya a gidan Deeni kuma na zama muguwar Aminiya na zama butulun awa na zama mai ha'incin abokantaka amma ban girbi komai ba Jiddah sai tashin hankali da rashin natsuwa da ba in talauci auren sunna ya gagareni balle an sunna sai shegu na kan titi marassa Uba marassa dangi su ka ai na tara gabana ga rashin daraja kowa zai iya takani ya wuce ba a komai ji yadda na koma na lalace na nakasa saura jiran lokaci kawai nake sai ga wani bala'in ya sake dimfaro Ni Yau in nan aramar iyata ta kashe Yayarta saboda saurayinta ya kwanta da Yayar tata... Kuka ya hanata cigaba da maganarta. Jikin Mustapha ya yi sanyi jin kalaman matar na cewa Jiddah ta samu sauyin yanayi ta samu mijin dake sonta bai son gusawa daga inda take sai a lokacin ya arewa Jiddar kallo, ba aramin fa uwa ba gabanshi ya yi ba, ganin yadda ta koma daga jiya zuwa Yau kawai ta rame ta fice daga hayyacinta k amar ma shasshekar ciwo take yi. Kansa ya dafe anya kuwa yana da adalci? Jiddah ta ja ajiyar zuciya tace, "Tabbas na gode wa Allah a duk yanayin dana samu kaina a gidan aurena, ban damuwa saboda za ina ne haka nasan ba komai bane dawwamamme ba tunda har zaman gidan Deeni bai dawwama a gareni ba to ba in ciki ba zai dawwama a gareni ba kowane iri ne kuwa. Ina so ki sani ba zan iya yafe maki ba, saboda kin cutar da Ni kin saka Ni a ba in ciki madadin ki taimaka min matsayinki na Aminiya ta wadda na yadda da ita na za e ta a cikin tarin mata dan ki maye min gurbin Alawiyya sai kika kasa ki kai amfani da damar kika dinga cutar da Ni wanda ban san iya adadin kukan da nayi ba dare da rana ba kika taimaka