← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 133

Sashe 57

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 31 Cak ta tsaya tana kallonsa, domin jin dalilin kiranta da ya yi, har kira biyu. Rasa abin da zai ce mata ya yi domin baki aya sai yaga tai mai kwarjini bakinsa ya fasa furta gaskiyar abin da ke asan ransa, don haka sai ya ce mata, "Ki kira wayarta mana ki ji ko tana ina tunda bata nan gidan." Kamar ha in baki tsaki kowace ta ja ta koma inda take zaune tana ta e bakinta. Jiddah ta an yi murmushin da bai barin fuskarta tace, "Tunanin da ban yi ba kenan, ko da yake ban ma fito da wayar ba, amma bari na koma sai na je na kira ta a wayar." Ba tare da ya kasa auke ido daga fuskarta ba ya ce, "Bari na kira maki ita mu ji ko tana kusa, ya saka baki ya kwa a wa Maryam kira domin ita ce awarta. Yi tai kamar bata ji shi ba sai da ya kira ta kusan sau hu u sannan ta aga labulen akinta tana yamutsa fuska tace, "Lafiya kake ta kirana kamar mai bina bashi?" Shi ma dai cikin fuskar rashin walwala ya ce mata, "Number awarta Bilkisu za ki ba da a kira wa wannan taji ko tana ina." Kamar ba zata ba da ba, don bata ce komai ba, ta koma saki labulanta ta koma aki. Jiddah har ta saduda zata tafi sai kawai ta ji muryar Maryam in na karanta ma Mustapha number don haka ta saurara ka Ta sowa ya yi har gabanta, yana kiran wayar har ta aga ya gaya mata Jiddah ce ke neman ta gata nan gidansa. Bayan ya kashe wayar ya dube ta fuska fal farin ciki ya ce, "Kin ji ta koma gidanma yanzu haka wai daman marka en kayan miya ta amso." Jiddah cikin murmushinta tace, "Na gode bari na je to." Ta juya ta fice ya bita da kallo har ta rufe ofar gidan idonsa na kan ofar. Maryam dake kallon komai ta tagar akinta ta ja tsaki tace, "Sai shegen son matan tsiya ba kirki. Wa ya sani ma ko jawararsa ce? Aikin banza." Jiddah na shiga gidan Bilkisu ta ja ajiyar zuciya tace, "Kai Yau naga ikon Allah! Su kuma haka tsarin su yake ? Tabdijam kowa dai da halinsa." Bilkisu tai dariya don tasan an yi wani abin ne gaban idonta tun da lambar maigidan ce ya kira ta da ita to ba shakka tasan cewa an tabka wani abin gabanta wanda gidan ne kawai ake irinsa a unguwar. "Hala fa a su kai sababbun?" Cewar Bilkisu tana dariya. "Uhmm! Ban iske ko aya ba a tsakar gidan sai maigidan da yaran kawai yadda naga gidan ne bai min ba, shi kanshi maigidan a dame yake ko mai yasa oho! Dariya Bilkisu ta sake kashewa da ita tace, "Ai wallahi ka an ki ka gani indai gidan Mustapha ne, bawan Allah yana amsar wuta gidan nan ai, ko da yake ai maganin masu auren mata barkatai kenan, ka tara yara ka tara mata ai ta fitina kullum cikin rabon fa a kake, ko da yaushe cikin tashin hankali kake na rashin zaman lafiyar gidanka. Amma wallahi yana ban tausai domin yana bakin arinsa kawai dace ne bai yi ba, a zahiri kowa auka yake laifinsa ne matsalar gidansa amma mu da muke tare da su mun san cewa laifin matan ne." "Ke ji mata sai wani kare shi kike, nifa duk abin da aka ce namiji zai yi wallahi ban cewa bai iyawa, komai aka ce namiji na yi wa mace yadda nake da gudun gaske ma, domin maza basu da tabbas ko da wasa namiji bai tausan mace yadda take tausansa, ke a takaice ma dai Ni nan da kike gani babu abun da na tsana irin aure da soyayya." Bilkinsu ta dubi Jiddah sosai tace, " awata bari ki ji na gaya maki gaskiyar magana, Mustapha an gayu ne, ga tsabta sannan irin mazan nan ne masu son rayuwar kulawa da nuna soyayya sai dai bai dace da samun irin haka ba daga kowace daga cikin matan nasa. Amma wallahi nasan da zai samu wadda zata kula da shi ta tarairaye shi tayi mai duk abin da yake so wallahi sai an yi mamakin yadda zata rayu da Mustapha cikin farin ciki Jiddah, domin nasan Mustapha yafi mijina kyawawan halaye nesa ba kusa ba wallahi har addu'a nake Allah Yasa nawa mijin ya koyi irin halayen Mustapha." Jiddah ta ta e bakinta tace, "Ke Ni ba gulmar wani gida ta kawo Ni ba, zuwa nayi na ji idan an kawo kayan yaran da kika ce na saidawa na gani idan akwai daidai na yarana amma kin tasani da maganar wani can da ba ruwana da shi." Bilkisu tace, "Ke fa awata na lura Deeni ya cire maki duk wani so da yardar maza a ranki, kuma ba haka bane ba akwai tarin maza masu kula da tarairaya irin wadda kowace mace ke mafarkin samu a gidanta." "Allah Ya kyauta! Ni da aure sai idan ana yi a lahira na yi amma a duniyar nan ban ce na rantse ba amma kam babu Ni babu wani aure Bilkisu." Babu yadda Bilkisu ba tai ba, amma Jiddah ta kasa fahimtar ta, don haka suka bar maganar suka koma kan kayan da za a kawo na yara Jiddah zata siya." Tunda ta fice daga gidan ya koma akinsa yana jin wani abu na yi mai yawo a cikin jikinsa da zuciyarsa. "Wane irin so ne wannan mai arfi ke yawo a cikin jikina na yarinyar ne? Wace irin soyayya ce wannan nake mata? Na tsani auren amma gani da kaina nake hasaso rayuwar aurena da yarinyar me hakan ke nufi?" Ya sake zuyawa yana ajiyar zuciya ya ce a bayyane, "Ina cikin matu ar damuwa amma kuma nake jin ki a raina, cike nake da damuwa amma nake jin ke ce za ki cire min damuwar, na kasa natsuwa domin ban da ita amma dana ganki sai na manta tashin hankalina, don Allah Jiddah ki tausaya wa rayuwata ki zama cikon mafarkina kamar yadda nake gani a mafarkina na aureki muna rayuwa mai cike da tsabta da farin ciki muna rayuwa tamkar ko da yaushe sauyo mu ake saboda rashin damuwa. Idan bai manta ba, Salim na yawan gaya mai cewa, ya ara ha uri akwai lokacin da komai zai wuce a wajensa kamar yadda zai wuce a wajen Jiddah, bai ta a tambayar wane irin hali yarinyar take ba, har Salim ya rasu, domin a tunaninsa ba huruminsa bane ba tunda gidan wani take, amma a yanzu ji yake so yake ya ji wane irin hali ne wanda yarinyar tai a gidan aurenta? Amma gun wa zai ji? Hajjo ce amma ya zai ya tunkari Hajjo da maganar? Yana cikin halin da ya kamata ya tarkata babin mata ya rufe a rayuwarsa hakan shi ne daidai amma me yasa Jiddah ke kai da kawowa a ransa da zuciyarsa? Tana matu ar birgeshi yarinyar ko da yaushe cikin fara'a take, baka ta a ganinta da fuskar damuwa alamar tana tare da godiyar Ubangiji kenan tunda tana da yakana a tattare da ita. Asma'u ce ta fa akin ba sallama ta wurga mai harara da jakar kayanta a hannu tace, "Na lura komai na gidan nan nice a banza ce nice wadda bata da ancin kanta balle na anta don haka zan koma gidanmu na gaji da wannan ba in zaman mai cike da takaici da mugun son kai." Mustapha ya dube ta ya kasa tanka mata, domin mafi yawan lokuta idan suna mai irin wannan shirmen kasa magana yake su kuma sai su auki hakan matsayin wula anci ne da son kai daga gare shi. Ta sake aga murya sosai tace, "Daman ai nasan ba zaka tanka ba, tunda ba nice nace ma matarka na satar abinci tana saidawa da kaiwa gidansu ba." Sai a lokacin ya bu e baki cikin takaici ya ce,"Ke wai wanda ku kai bai ishe ki bane sai kin biyo nan kin sake min wata fitinar ne? Wai me yasa baki san zaman lafiya ne? Wuce ki ban waje kada ki sake ata min rai, ba dai abin da kika ga yayi maki ba kenan, to ki je kiyi ta yi." Ya juya ya gyara kwanciyarsa ya lumshe idonsa kamar mai barci. Tai ta ananan maganganun ta son ranta tana kiran shi azzalumi mugu da bai san adalci ba, shi dai bai sake tanka mata ba, kamar yadda ba zai hanata zuwa gidansu idan yajin nata ya motsa ba. Maryam kuwa sai abin ya yi mata ciwo ganin Fatima ta shige akin Mustapha ta yi shiru kuma bata jiyo hayaniyar su sai ta auka ya sata aki ne yana lallashinta ita kuma ko oho tunda ba aunarta yake ba yanzu. Sai zuciyarta ta dinga tafasa har tana jin ma ta je akin ta ha a su duka ta ci masu mutunci kawai ko zata ji sau in zuciyarta dake una. Tana tsaye gun tagar akinta ta ga Fatimar ta fito fuskarta ba wata damuwa ta shige akinta, bayan da farko tasan yaji ne tai niyyar yi, amma da yake munafuki ne shi ne ya lallashe ta waya sani ma ko har zagina ya yi gabanta don ya faranta mata rai?" Ai sai ta kwasa ita ma cike da fushi ta nufi akinsa, kamar dai yadda suka saba ba sallama ta ambaci sunansa kai tsaye cike da rashin kunya tace, "Mustapha ka ji tsoron Allah wallahi ba zan ta a yafe munafurta ta da kake ba da zalunta ta ba a cikin gidan ba, sai Allah Ya saka mun wallahi." Kallonta yake ita ma kamar Fatimar, ba wata kwalliya balle amshi kayan jikinta duk sun yi datti kamar wata tsohuwa haka take cikin kayan ba mai cewa yarinyar mace ce ita. Wani takaici ya sake kama shi, sam bai dace ba ta kowane angare, yana son yaga mace cikin kwalliya yaga mace nata amshi uwa uba ya ganta cikin ananan kaya
Chapter 57 · 0% Book details