← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 133

Sashe 102

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

su biyo NI daga baya amma ba zan iya ha urin kina can ina nan ba Princess saboda ance idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi to haka ne kam na yadda saboda yadda nake ara jin sonki a raina tamkar zai lahanta Ni, gaskiya Princess ki gode wa Allah don ya saka min aunarki sosai a zuciya da ruhina." Lamo tai kan gado tana zuba mai shagwa a shi kuma yana biye mata yana bata ha uri ta daina kuka yana tare da ita kowane lokaci. Ita kam idan akwai abin da ke birgeta shi ne ta dinga shagwa a ana bata ha uri ana lallashinta abin na matu ar tsumata taji tafi kowa farin ciki haka zalika tafi kowace mace dace da samun mai kulawa da ita. Ta sake narkewa sosai tace, "Prince kasan wani abu kuwa?" Ya ce cikin kulawa da natsuwar gaske, "Princess sai kin fa a zan sani dai." an yi jim sannan tai ajiyar zuciya tace, "Wallahi na rasa yadda akai nake masifar sonka sosai nake jin aunarka tana yawo a cikin ga an jikina ban iya kwashe tsawon yini guda ba tare da naji muryarka ba mai sakani nisha i da walwala ba, ana yawan cewa soyayya da mai mata jidali ne amma Ni kam mantawa nake da kana da mata, ko da yaushe kai ne kawai a gabana kai ne muradina kaine abin tunawa ta don haka ta kai nake bata matanka ba. Ta ja ajiyar zuciya tace "Wallahi Prince ban jin akwai wata barazana ko maganar da za ai kanka wadda zata saka naji cewar ba zan iya aurenka ba, domin so ne nake maka daga asalin cikin zuciyata ya fito zuwa cikin sassan jikina har ya tumbatsa ya bayyanawa halshena shi kuma ya yi jagora zuwa ga fuskata har jama'a suka shaida cewa lallai Jiddah na son Mustapha so bana wasa ba, so irin wanda idanuwa ke rufewa kunnuwa su toshe ba ji ba gani sai zallar aunarka kawai nake iya ji da gani haka zalika nake iya ganewa." Sai kawai taji shi yana cewa, "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah na gode maka daka azurtani da samun wannan kyakkyawar mace natsattsiya son kowa hassada ga wanda bai samu ba. Don Allah Princess mu cigaba da aunar juna, mu zama haka har abada kar da mu ba wasu mutane damar raba mu ko shiga tsakaninmu domin nasan hakan duk mai sau i ne saboda nasan ina da tarin ma iya na oye dana bayyane wa anda ban isa na hana su aikata abin da suke yi ba a kaina. Princess ba wai don ki soni ba zan fa a maki ne kawai don ki sani ina cikin wani hali wanda Allah ne kawai shaidata kan komai ke faruwa a cikin gidana, don haka ina so ko anyi maki maganata don Allah ki dasa adalci kafin ki yanke min hukunci, saboda nasan cewa yanzu duk wata hanya da za a bi don aga an rabani dake ita za a bi, za a gaya maki abubuwa da dama masu nauyi kaina wanda za ki ji cewar ban kamata na zama miji gareki ba, amma ina so ki sani Ni nake sonki kuma nake burin aurenki don haka nayi maki al awarin zan zauna dake da zuciya guda kuma zan yi duk wani arin ganin kin rayu cikin aminci da farin ciki har mutane su yi mamakin abubuwan da ake fa a kaina nasan a kanki ne za a gane cewar ba laifina bane ba Princess laifin matan da nake aure ne don Allah Princess ki yi min wannan alfarmar... Kuka ya ci arfinsa ya kasa ida maganar da yake yi. Jikinta ya yi sanyi sosai, tabbas mutane na ba shi laifi kan damuwar gidansa mafi yawan mutane cewa suke shi ne mai babbar matsalar bai da mutunci haka zalika bai ganin matansa da gashi duk ya raina su ga shi da masifar fa a ga disgin masifa tare da buyagin tsiya , wasu ma cewa su ke har dukan mace yake da zaginta, duk ta ji labarin ne zuwan da tai suka fara soyayya ake gaya mata hakan, jikinta kan sanyi taji zuciyarta na rawa kan shi da farko amma daga baya data jima tare da shi kuma ta fahimci wasu abubuwan daga awarta ma wabciyar Prince in wadda awa ce ga matarsa Maryam, ita kanta Bilkisu tana gaya mata cewar bai da laifi yana da kirki kuma tsaye yake kan gidansa babu rashin ci haka babu rashin sha balle sutura asalima bai da aramar ci ma don an gayu ne shi ko da yaushe cikin son rayuwar hutu yake kawai halin matan ne sai a hankali kuma sai su dinga tsine mai don kawai ace suna da ha uri shi ne bai da kirki bata san miye amfanin hakan ba kuma da suke. Jin ya kasa daina kukan ta sausauta murya sosai tace mai, "Haba Prince kamance da cewa kowane mutum yana tare da kalar tashi addarar ne? Ko ka manta da cewa mutane ba su ne za suyi maka hisabi ba idan anje lahira? Don Allah ka daina damuwa ka natsu ka kwantar da hankalinka insha Allah ba za kai nadamar aurena ba kamar yadda nima ba zan nadamar aurenka ba insha Allah. Wallahi a da ne nake jin ar kan aurenka amma yanzu na shirya zan iya aurenka ko da kuwa da gaske ake maka kana tare da wa ancan halayen insha Allah zan ari naga na sauya ka zuwa magidanci mai adalci da tausayi ga iyalinsa. Wallahi Prince ina tausan kaina amma kaima ina matu ar tausanka sosai hakan yasa ko da yaushe nake ara sonka nake ara jin na agara na aureka saboda gaskiya tai halinta a fahimci cewar fahimtar baibai akai ma baka da wani laifi a rayuwar gidanka. Amma duk da haka ina so na ara shaida maka cewar na yadda da kai na amince da kai nasan cewar ba zaka ta a juya min baya ba balle ka aikata min ko da rabin abin da ake kiran halinka ne Prince. Ina kuma baka shawara suma matan naka ka sake samo hanyar da zaka daidaita tsakaninka da su ku zauna lafiya kai da su saboda zaman lafiya shi ne ke arawa maigida yalwar arzi i Prince." Ajiyar zuciya yai ko bai fa a ba tasan ya samu sau in abin da yake ji a asan ransa, sai ta kauda maganar tace, "Prince kasan kuwa idan ka tashi ba da sadakina ko nawa zan ce ka ban?" Kamar tana gabansa haka ya girgiza mata kai sai kuma ya amsa mata da a'a Princess nawa zan ba da ne?" Ta kwashe da dariya sosai tace "Kasan dai ai ba wani sau i zan maka ba, saboda kasan zan yi matu ar tsada ta ban mamaki wadda sai kowa ya yi Allah san barka ance lallai Jiddah tayi wuta." Ya fashe da dariya ya ce, "Too ashe kice na tashi tsaye na nemi ku i auren mace mai kyau daman sai mai ku i." Ta murmusa don daman burinta ta sashi ya manta ba in cikin da yake ci kuma ga alama ta auki hanyar don hata ta sake ce mai, "Prince Ni fa gaskiya sai naga kamar ka fini kyau don haka ba zan amince ba da gayun da kake ko ranar auren ban yadda kai kwalliya ba kar da ace angon ya fi amaryar kyau ma." Ta idasa maganar da alamar shagwa a a muryarta. Ji ya yi komai ya yaye mai tamkar ba abin da ke damunsa ya dinga dariya yana jin nisha i yana jin yadda ta dage tana lissafin ku en da ko a gwamnati sai an yi wata ba a nemo inda suke ba tana cewa a hakan ma duk don saboda so da auna tare da wani munafin tausanshi ne yasa ta lissafa ku en ka an amma ba don haka ba tsab zata lissafa manyan ku e masu tsoka saboda ta ci su ai. Shi dai ya samu abin yi don haka ya dinga zolayarta yana dariya har da dafe cikinsa tsabar farin cikin halin da yake ciki. Maryam ce ta banko ofar ta shigo akin ta auka da Hafsat yake nisha i don sun auke ta sakarya ranar aikinta za su shige aki suna wata banzar shewa ? Sai dai ganinsa manne da waya a kunne ya wani lumshe idonsa sai dariya yake ta fahimci cewar da Jiddah yake wayar sai ta samu kanta da fisge wayar ta jefar gefe guda ta ci amara tana huci tana kallonsa burinta yai magana ta are mai tanadi tsab, sai dai yana ganinta ya tashi ya auki wayarsa yai mata kallo guda yabar akin. Sai kawai ta zauna ta ci-gaba da zubar da ruwan tujara da zagi tana cewa zata ga inda za ai auren nan sai dai inbata nan, amma babu mai kawo mata karuwa cikin gida. Yana fita ya ga kiran bai katse ba, Jiddah kuwa ba abin da bata ji ba na maganar Maryam in sai kawai ta saka dariya tace "Gaskiya na taya ka murna matanka na sonka budurwarka na sonka so na gaskiya mai matu ar girma." Sai kawai ya ji ya washe daman tunanin me zai ce mata yake don haka jin maganarta yasa ya samu sau i ya ji komai ya wuce ma sai kawai suka cigaba da hirarsu gwanin sha'awa ya zauna ofar gidan yana wasa da tsinke suna zuba soyayya abin da ruhi da jikinsa ke so kenan a rayuwarsa. Sai da katin wayarsu baki aya ya are daga shi har ita sannan suka ha ura ba don ransu ya so ba. Ranar da zata tafi Kano tun da safe ta shirya ba da yara zata tafi ba saboda karatunsu don haka su kai bankwana ta auki hanya zuciyarta cike da nisha i a hankali take tu in har ta isa gida kamar yadda ya shaida mata kuwa yana zaune yana jiranta ya ci gayu sai amshi ke tashi na turarensa mai saukar mata da nisha Da hanzari ya bu e mata mota yana cewa, "Oyoyo Princess sannu da zuwa." Tamkar su rungume juna haka suke ji su duka amma ba dama don haka sai kawai suka zuba ma juna ido kowa fuska
Chapter 102 · 0% Book details