Sashe 59
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ce ta za i wanda take so a shuka mata kuma ya shuka mata su. Baki aya ta sakankance Abubakar shi ne mijinta idan ta kammala karatunta domin shi a shekarar arshe yake yanzu. Wajen aikin su na polio aka ce an sake masu sabon S.T.P wanda bai da wasa don haka yanzu bata alular zuwa gun aiki saboda kar ya je bata je ba ta samu matsala saboda tasan komai ta zama ta zama ne silar aikin polio don haka bata wasa da shi sam. Ranar aikin tana zuwa bata jima da fara aikin ba sai ga S.T.P in ya je gun su, kallo guda tai mai taga kamar tasan shi amma ta kasa tuna ina inda ta san shi don haka ta share kawai bayan sun gaisa ta cigaba da aikinta. Sai dai kiran da yasa akai mata ne yasa ta fara tunanin shima ba mamaki ya san ta, bayan sun gaisa ya kalle ta ya ce "Wai ba Jiddah bace ta gidan Hajjo ba?" Kanta ta aga alamar ita ce, ya ce yana dariya, "Yanzu nan kin manta Ni? Ai ko muna yawan ha uwa gidan awarki Bilkisu domin ni anin mijinta ne." Tabbas an yi hakan yanzu ta tuna da hakan. Gaisawa suka sake yi tana dariya ta ji kunyar yadda akai ta manta shi. Bayan kwana biyu su kai waya da Bilkisu take gaya mata an turo anin mijinta aiki garinsu shi ne Bilkisun ke ce mata don Allah ta taimaka tai mai magana ya sa ta aikin polio ita ma tun da yana da hanyar hakan ita kam kunya take ji. Tace to ta tura mata lambar shi za tai mai magana insha Allah tun da ba lallai bane ba a sake maido shi garinsu aiki ba. Sai kuwa ga lambar Bilkisu ta turo mata, kamar ta kira shi a lokacin sai kuma ta katse kiran ta bari sai anjima. Da yake tana da application in nan mai suna Trucoller sai taga sunan Mustapha madadin taga sunan Mubarak don haka sai abin ya aure mata kai, sai kawai ta fasa kiran kawai ta cigaba da lamurranta kawai ta manta da lambar ma baki aya a wayarta. Bayan wani lokaci sai Jiddah ta sake komawa Kano domin dubo Hajjo da bata lafiya, bayan ta je gidan Bilkisu ne ta tuna da lambar da ta tura mata ta Mustapha kamar ta gaya mata lambar waye ta bata sai kuma ta share domin dai idan da arzi i bai kamata ba ace yadda yake da Uncle Salim ba ta watsar da shi ba, kamata yai ace tana daraja shi tana kiransa suna gaisawa ko dan darajar abokinsa kuma an'uwansa Uncle Salim in ta. Hakan yasa ta bar maganar kawai, musamman ita kuma Bilkisu da yake ta samu aikin sai batai mata maganar ba ita ma. Bayan ta dawo gidan Hajjo ne ta gama komai ta kira Abubakar suka sha firar soyayarsu sai ta latsa lambar Mustapha da zummar kiransa ta gaida shi kawai. Sai dai ta ji wayar a rufe don haka ta aje wayarta ta gyara kwanciyarta tana gode wa Allah yadda ya juya mata lamurranta daga zafafa zuwa sau a daga ita har mahaifiyarta suna cikin rufin asiri ba su rasa komai ba, Mamarta na sana'ar saida robobi ita kuma tana tata sana'ar ga yaranta ta kaisu makaranta mai kyau hakan yasa take cikin kwanciyar hankali. Har ta tafi basu ha u da Mustapha ba, duk da cewar ta so su ha u su gaisa domin hakan zai ebe mata kewar Uncle Salim sosai, amma basu ha u ba kuma ta kasa sake kiran lambar wayarsa tun kiran farko da tai mai. angaren Mustapha kuwa tun ranar da ta zo ya ganta sai dai a ranar aka tura shi Abuja gun wani aiki ba don ya so ba haka ya tafi yana jin tamkar zai rasa ta idan bai gaya mata abin da ke ranshi ba game da ita ba. Ko da yake yanzu ya samu sau in lamurran sa tunda ya cire damuwar gidansa ya aje gefe guda sai dai idan su kai mai ya ji ciwon abin a ransa nan take da ya bar gidan ya manta, hakan yasa ya zama shahararre gun yawo a yanzu idan yabar gidansa da safe bai dawowa sai yamma idan zai wanka daga nan sai wajen sha biyu na dare yake dawowa ya ha ura da zaman gidan ya ha ura da cewa dole sai ya zauna da su yadda yake so ya bar su ne su zauna yadda su ya yi masu. Duk wadda ta ga damar kula shi ta iske shi akinsa shi dai ba zai kore ta ba, haka zai saurare ta amma ya daina biyewa ana jin muryarsa ma wabta yana fa a ya yale su duk abin da su kai daidai da su ne. Duk da haka ko da yaushe cikin masifa suke da junansu ba su daina tashin hankali ba haka basu daina zaginsa suna ganin yana tauye masu ha i ba, kowacce gani take shi ne damuwarta shi ne bai kulawa da ita bai damu da farin cikinta ba, wannan yasa ya watsar da su baki aya yake rayuwa tamkar marar mata yake rayuwa tamkar saurayi. Iyarsa da su ya ajiye duk abin da yasan ha insa ne yana bakin arinsa kan hakan, amma su ya daina neman wani ha i nashi kan su na wai su gyara gidansu da jikinsu ko yaransu duk ya daina haka ya daina ji a ransa cewar shi ya isa yasa ai mai abu a gidansa komai shi ke yin abinsa tun daga gyaran akinsa linke kayansa da duk abin da ya danganci aikinsa shike abin sa. Hutun makarantarsu ya are kamar yadda su kai al awari da Abubakar zai fara komawa da kwana guda sannan ita ma ta koma , sai dai har akai kwana hu u da komawa ba Abubakar ba labarinsa ko da yaushe a waya sai ya bata uzurin cewa hidimomi sun yi mai yawa ne , yanzu haka wayarsa ma ta lalace aron wadda yake kiranta da ita yake yana kiranta kuma bai da ku i domin an gama ginin gidan baki aya ku in sun tafi can. Hakan yasa ya bata tausai ta cire layukan wayarta ta aika mai da wayarta ita kuma ta siyi wata wayar. Cikin lokacin sai waya tsakaninta da Abubakar ta ragu, sosai abin ke damunta sai tai ta kiransa a waya amma bai auka, haka bai damu daya kira ta ba daga baya. Kowa yasan Jiddah na cikin damuwa saboda ta sauya sosai, sai da Abubakar ya kira ta ya gaya mata cewar tai ha uri ya rasa wayarsa ne babba sai arama don haka ko a chat bata ganinsa. Ta yarda sosai da Abubakar don haka ta samu natsuwa da kwanciyar hankali kan lamarin har ta dawo daidai kamar baya. Kasancewar ya ce mata bai da waya babba yasa bata damu da chat ba kawai sai idan ta kira shi ko ya kira ta take waya da shi kawai. Wata ranar Litinin ta je makaranta duk ta damu da rashin dawowar Abubakar ana cikin sati na uku da komawa makaranta sai kira ya shigo wayarta kamar kada ta auka don sabuwar lamba ce sai kuma ta auka. "Salamu alaikum, ina magana da Jiddah ne don Allah?" Daga can angaren aka tambayeta, kamar mai maganar yana gabanta haka ta girgiza kanta. Zuwa can ta amsa da cewa "E Ni ce Jiddah ke magana." "To Jiddah don Allah ki yi ha uri ba ki san Ni ba amma Ni nasan ki, ina so ne na gaya maki abin da ke faruwa kan ala arki da Abubakar, ko kin san cewa Asabar in nan data wuce aka aura mai aure? Nasan za ki yi mamaki amma ki je facebook ki duba za ki ga hotunan auren ki duba page ina domin duk mun saka har dana amaryar ma." Kawai wayar fa uwa tai daga hannunta ba tare da tasan lokacin da hakan ya faru ba, rabon da taji alamar hawan jininta ya tashi ko zai tashi har ta manta amma nan take ta dinga jin kanta na sarawa numfashinta na fita da yar. Kamar mahaukaciya haka ta warto wayar ta kunna data ta shiga facebook ta duba sunan Abubakar in amma bata ganshi ba, hakan yasa ta fahimci ya yi blocking nata don haka sai ta saka sunan abokinsa da ya kira ta. Kamar a mafarki haka ta ga hotunan Abubakar da amaryarsa wani kuma da abokansa, tun daga na wajen wallon amarya da ango har na wajen aurin aure har da na walima duk an ora. Kuka mai arfi ya wace mata bata san lokacin data yanke jiki ta fa i gun ba. To masu karatu mu ha u a kashi na gaba don jin yadda zata kaya. Me yasa Abubakar ya yi mata hakan? Taku a kullum Haupha kuma [8/23, 8:12 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa