Sashe 72
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ya zo nan?" Hajjo tace, "Ni dai ba Jiddah wayar na ba shi ta ja mai kunne kawai tunda ba yarinya bace ba ita." Kamar tana gabanshi Hajjon haka Mustapha ya zaro idanuwa waje, ai wallahi ko mai zai faru ya gama jin muryar Jiddah kai ko ganinta ba zai sake yi ba ta riga tayi mai nisan da ba zai iya kamota ba. Abin da yake raya wa kenan a ranshi a fili kuma sai ya ce ma Hajjon. "Ai tana akin ganawa da ba i don haka ba zan iya ha a su ba, kawai ya koma inda ya fito Hajjo." Hajjo ta dubi Deeni fuska cike da acin rai tace, "To ka dai ji da kunnenka Jiddah na can na ganawa da ba in kirki irin albarka sai ka koma inda ka fito kaban waje na gaji da kallonka ina tuna ba ar izayar da ka dinga ganawa yarinya. Kai Allah na tuba ma ba zan musu ba idan aka ce ba in cikin abin da kake ma yarinyar ne ya kashe mata Uncle Salim inta ba." Ko da Deeni ya ji Hajjo na neman ora mai kisan kai sai ya tashi yana share hawaye ya fice daga gidan bai san inda za shi ba. Mustapha na zaune duk ranshi ya aci akan me ma Hajjo zata bar wani banzan tsohon mijinta ya shigar mata gida har da cewa wai ya maida Jiddah akinta? akin ubansa ya maida ta? Tabbas akwai aiki a gabansa duk da yasan cewa babu yadda za ai Jiddah ta koma gidan mijinta amma kuma yana hango barazana daga Al alin nan yadda yake ure Jiddah da kallo, komi tace bai mata jayayya kai tsaye yake amsar bu atar ta. Shi kam ya zai yi ne ya tunkari Jiddah da maganar dake cin ranshi ta aunarta? Yasan cewa yana cikin matsala a gidansa amma hakan bai hana shi jin so da aunarta ba a ranshi ba. Yana zaune abin duniya duk ya dame shi Jiddah ta shigo fuskarta auke da murmushi kamar yadda take ko da yaushe. Ta dube shi tace, "Akwai yiyuwar zan fita na je gidan da Mamar Alawiyya ta zauna zan duba wasu abubuwan da nake bu ata, don haka mu je gidan da aka ban ka huta Ni sai na wuce." Kallonta yake yana jin tamkar ya ha e ta don so, ji yake tamkar ya maidata ciki ya huta da munafukan da ke mata kallon so, amma ba dama, sai dai ba zai amince tai yawo ita ka ai ba dole ne duk inda ta aje afa ya ora tashi afar a gun. Don haka ya mi e ya ce, "Mu je ai ban gaji ba, kuma daman amfanin rakiyar kenan ai." Ta juya ya bita a baya suka fice wata mota suka nufa suka zauna a baya dukkansu ya ja suka nufi gidan Major. Ko a motar sai kallonta yake yana ara jin aunarta na yawo a ranshi, ita kuma sai karanta file in case in take tana nazari wani lokacin tai murmushi wani lokacin ta ja tsaki. Suna isa gidan mai gadin gidan ya gaya masu masu gidan sun ce kada a bar kowa ya shigar masu gida hutawa suke. Jiddah ta fito fuskarta ba alamar damuwa tace, "Sa o mai kyau, amma ka sani a cikin dokar tasu ban da ta masu bincike don haka maza bu e mana ofa, da afa ma za mu yi tattaki har ciki." Ba yanda zai, kuma sai yaga yarinyar tai mai war jini, sai fara'a take ba wani ha e rai da nuna isa, don haka ya samu kanshi da bu e masu ofar gidan. Ita da Mustapha suka shiga gidan suna kalle -kallen yadda tsarin ginin gidan yake. Har suka isa ofar falon gidan su kai sallama ba wanda ya amsa ma su, sai da su kai sau uku ba amsa don haka ta shige gaba yana bin ta a baya suka zauna kan kujerun falon Jiddah na arewa falon kallo da nazarinsa. Tun da suka shigo Hajiya Turai ke kallonsu tana mamakin daga inda suke. Ganin sun zauna kamar wasu mutanen gidan yasa ta fito cike da ta ama da alfarma ta isa gabansu ta jefa masu tambayar wa suke nema? Jiddah tai murmushi tace, "Ke muke nema domin gunki muka zo, ina fatan za ki ban ha in kai kamar yadda aka saba?" Hajiya Turai ta zubama Jiddah ido tana mamakin tsaurin idon yarinyar, da tunanin wace ce ita kuma? Daga ina ma take? Waye ya turo ta? Jiddah ta gyara zaman tabaran fuskarta tace, "Sunana Barista Jiddah nice sabuwar Lauyar da ke kare Fatima a shari'ar da ake gwabzawa." Hajiya Turai ta yamutsa fuska, "Maganar banza to Ni ina ruwana da wannan can ku ta shafa ai." Jiddah tai murmushi sosai tace, "Ko zan iya sanin ala ar ki da Fatima?" Cikin masifa Hajiya Turai tace, "Kishiya ta ce sai me kuma?" Jiddah ta dubeta sosai tace "Kishiyarki kuma? Dama Fatima nada kishiya ne?" Hajiya Tani dake isowa gun tace, "Ga wata ma nan, domin ni ma kishiya tace Fatima." Jiddah tai murmushi tace, "Na fahimta sosai na gane lamarin, sai dai na kasa fahimtar abin da yasa ban ga an rubuta Fatima nada kishiya ko aya ba a file in case inta ba." Suka fashe da dariya suka ta a, Hajiya Turai tace, "Saboda Fatima ba asalin kishiya muka auke ta ba, tun fil azal daman baiwa muka auki Fatima a gidan nan." Hajiya Tani tace, "To ban da ma wauta ina mu ina kishi da Fatima daman Hajiya Turai? Ai Fatima kasada ce tasa ta auri mijinmu ba komai ba, ko da yake rabon makance ne yasa ta shigo gidan nan." Suka sake kashewa da dariya. Mustapha ji yake kamar a mafarki lamarin, kamar ba da gaske ba abin ke faruwa, mamakin wane irin mutane ne wa annan yake a ransa, ta gefe kuma jinjina wa Jiddah yake yadda ta maze take jefa masu tambaya kawai yake. Suna cikin dariyar ita ma Jiddah ta tuntsire da dariyar sai su kai shiru suna kallonta da mamakin dariyar me take ita kuma? Jiddah cikin sautin dariyarta tace, "Wai daman sai da kuka fara makantar da Fatima a gidan nan ashe?" Su kai tsit, wace irin yarinya ce wannan kuma? Ta dakatar da dariyarta tace, "Amma kuma nayi mamakin yadda fasahar maidata makauniya ta zo maku amma ta she eta bata zo maku ba kai tsaye sai da dole ku kai mata azafin kisan mijinta. Ko kun auka ta haka ne kawai kuke ga zaku iya halakar da ita?" Hajiya Turai ta zaro idanuwa ta dubi Hajiya Tani su kai shiru, sai kuma suka mi e kowacce ta nufi angarenta. Jiddah sai ta gyara zama tace, "Waye ya gaya maku ana Shari'a da kurma? Waye ya gaya maku ana Shari'a da mahaukaci?" Tare suka juyo, "To ai Fatima ba kurma bace kuma ba mahaukaciya bace mu ne muka maidata hakan." Jiddah ta fashe da dariya tace, "Kun kyauta, na jinjina maku ta yadda kuka buga wasanku kuka saka kyautar ku sannan kuka dawo kuka cinye abinku." Kallon ban fahimce ki ba su kai mata. Ta sake sakar masu murmushi tace, "A tsarin doka baka shari'a da kurma domin kurma bai cikin cikakkun mutanen da addinin musulunci ya amince su yi wa annan abubuwan. 1. Shugabanci 2. Limancin 3. Bada shaida a kuto 4. Wakilci Sannan ina kuka ta a ji ko ganin inda makaho ya yi kisan kai irin wanda ake tuhumar Fatima da shi? Don haka Fatima kai tsaye kotu zata sallame ta da nayi niyyar hakan da tuni an sallame ta, sai dai na tsawaita abin ne don kawai na baku damar gyara abin da kuka ata, hakan ne kawai zai sa ku samu abin da kuke bu ata." Ta mi e tsaye ta dubi Mustapha tace, "Mu je na gama abin da ya kawo Ni." Haka suka fice suka bar su Hajiya Turai na kallon juna sun kasa furta ko da kalma guda. Har motarsu ta bar gun, sannan Hajiya Tani tace, "Kin ga mun yi wauta ashe ba a Shari'a da kurma muka rufe mata baki?" Hajiya Turai tace, "Ai ban san hakan ba da bamu yi ba, amma ko yanzu ai zamu iya gyara wannan matsalar mu bu e mata idanu da bakinta." To ko hakan zai sa su cimma manufarsu? Anya ba shigo-shigo ba zurfi ba Jiddah tai masu ba? Taku a kullum Haupha [9/8, 8:16 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa