← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 133

Sashe 126

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

na ara gaba Ni." Tace cike da gatsali "Zan zo fa, Allah zan zo tun kafin lokacin ma ba wasa nake ba, kin san dai ina sonki ban iya rabuwa dake koma me zai faru." Ji tai jikinta bai iya aukarta, saboda tun da ya shigo amshin turarensa yasa ta bu e idonta sai dai ganin fuskarsa ba alamar fara'a yasa ta kasa tashi ta tarbeshi ta bari ya shiga akin sai ta bishi don jin damuwarsa, ganin ya nufi akinsa kai tsaye bai shiga nata akin ba ta sake jin ba da i sosai amma sai ta tashi ta nufi akin don ta ji me tai mai Yau ya sauya baki aya? Sai dai jin yana waya da mace kuma taji me yake cewa yasa ta fahimci cewar ba ta ita yake ba don haka ta ja ofar don ta shiga ta ji ko da akwai abin da yake bu ata. Sai dai kuma akin a rufe yake alamar bai son ta shigar mai aki bai bu atar ta kusa da shi kenan, don haka ta ja jikinta cike da damuwa ta koma kan kujerar tana hawaye. Ganin har sha biyun dare bai fito ba sai kawai ta koma tai alwala ta cigaba da jera sallah har sai da taji bata iya bu e idonta sai kawai ta takure cikin hijabin tai barci a asa tana saukar da ajiyar zuciya lokaci zuwa lokaci. Sai wajen arfe biyun dare suka gama wayar duk da tsogumi da kashedi yafi yawa a wayar tare da jan kunne duk dai tai mai wanda duk ya ji ya amsa ya amince zai gyara mata duk wasu kura-kuran da take cewa ya yi mata a gidan na shi. Sai da suka gama wayar sannan hankalinsa ya dawo jikinsa ya dinga jin bai jin da in kwanciyar , sai yake jin kamar ya rasa wani abu a tare da shi, sai juyi yake ya kasa barci ya kuma rasa me ke damunsa don haka sai ya mi e tsaye ya fice zuwa falo ko ruwa ya sha ya ji sau in zuciyarsa. e ya ga akinta ko haske bata kashe ba, kai tsaye sai ya nufi akin don ganin me ya hanata barci har zuwa yanzu ita kuma. Bata kan gadon har ya auka tana toilet sai ya hango ta can asa a takure bisa abin sallah sai ajiyar zuciya take alamar taci kuka ba arami ba. Wutar kawai ya kashe mata ya fice ya ja mata akin yana jin bai kyauta mata ba, amma hakan shi ne daidai ya kamata ya yi mata idan ya kula ta tabbas gobe ba zata bar shi ya fice kan lokaci ba zuwa gidansu Hafsat ba. Ita kam Hafsat dama don ta ba Jiddah haushi yasa tace mai ya zo da sassafe saboda an ce mata jiya sai wajen azahar ya fito daga gidan nasa shi da tsiya ga ango to zata ga ta yadda za ai angonci indai ita ce Hafsat sai ta ga abin da ya turewa Buzu na i, za tai ta buga shi har sai ya gama buguwa sannan zata koma idan taga dama idan kuwa bata ga dama ba zata tsaya tsayin daka sai ya sake ta. Tunda asuba Jiddah ta tashi tai sallah ta nufi kicin ta fara ha a breakfast don taji ya ce zai fita da wuri don haka zata ha a komai da wuri bata son ya fita bai ci komai ba. Cikin sauri ta ha a simple breakfast ta jera ta shiga akin cikin sanyin jiki ta gaida shi ya amsa ba tare da ya bari sun ha a ido ba, ta maida hawayen dake son zubo mata tace, "Don Allah ka daure kai breakfast kafin ka fita na gama ha a maka komai." Bai ce komai ba yana ta arin fesa turare sai da zai fice ya ce, "Ki aje min idan na dawo zan yi." Ya zo ta gabanta ya ra a ta zai wuce, kamar ta yale shi sai kuma ta ga rashin dacewar hakan don haka ta jawo shi ta baya ta shige jikinsa tana cewa cikin raunanniyar murya, "Idan laifi nayi maka ina baka ha uri kuma ina neman alfarmar ka gayamin domin na gyara kuskurena, idan kuma ba laifina bane na wani ne ya shafe Ni ina maka addu'ar Allah Ya sassauta mata zuciyarka Ya tsare min kai Ya kiyaye min kai daga dukkan sharri da abin sharri Prince, sai ka dawo ka kula da kanka, idan ka jima ka samu wani abun ko a can ne inda zaka ka ci domin ban san kana zama da yunwa don Allah." Ta janye jikinta daga nashi ta shige cikin toilet akin saboda bata son ya ji sautin kukanta. Sanyi alau ya ja jikinsa ya fice ya kasa aiyana ko da kalma guda a zuciyarsa. Yana zuwa ofar gidan ya kira ta cikin barci ta amsa wayar tace ya jira ta zo ta bu e mai gidan. Wayarsa tai ara alamar sa o ne ya shigo ya bu e don ganin waye. "Dare da rana, safe da yamma ban tunanin akwai lokaci ko rana da zata zo wadda zan gaza fahimtar Prince ina balle na kasa yi mai uzuri kan dukkan abin da ya shafe shi, ina maka fatan alheri tare da addu'ar dacewa da abin da kake nema koma miye. Ka kula da kanka sosai don Allah ka ci abinci kan lokaci ina matu ar kewarka Prince ina, zuciyata sai ara aunarka take duk bayan sa'a guda. Sai ka dawo farin cikina abin alfaharina, daga taka Princess in ka." Ba don jingine yake jikin bango ba da sai ya fa i yadda ya ji jikinsa ya yi wani sakau kamar ba nashi ba. Princess kenan tana danne duk wani damuwa da takaicinta ta saka shi cikin nisha i ba ruwanta da yadda ya sauya daga jiya zuwa ya kasa bata kulawa ya kasa yi mata ko da rabin abin da take mai, to ya zai yi? Yana sonta kuma yana son matarsa Hafsat kowace da wajenta dole ne hankalinsa ya koma kan Hafsat don ba zai gangancin rabuwa da ita ba saboda yana sonta a duk yadda take. IN ALLAH* Labari da rubutawa
Chapter 126 · 0% Book details