Sashe 18
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
da Ni, yasa na kasa magana sai kawai kaina na aga ma shi tamkar adangaruwa. Jiki sanyaye na dawo cikin mutane ina mamakin halin Deeni da arfin zuciyarsa, bai bada ko sisi ba amma ji yadda yake ban umarnin abin da yake son nayi ma shi, ba wannan ne ya ban mamaki ba illa irin umarnin daya ban kan Safiya, watau shi ke ci da ita kenan ma yanzu amma ko a jikinsa ya barni a zaman yunwa da wahala ga ciki na haihu ya kasa bu e bakinsa ya yi min ko da sannu ce balle ya yaba min abin kirkin da nayi na haifar masa an fari. Nan inda nake daskare ya ra a ni zai wuce ya dawo kuma yace, " an ban dubu biyu nan ma tunda nasan dai kin fara kamawa naga danginki sai wani aure-dauren fuskar banza suke tunda dai ba su ne suka ban aurenki balle suce na sake ki ba." Haka na bu e jakar hannuna na auko ku in na ba shi ya amsa bai ko waigo ba ya fice daga akin, ina jin mutane na gaida shi suna mai barka da murnar an ra a suna. Cikin ikon Allah akai taron suna mai ban mamaki domin mutanen gari sun yi min kara sosai wadda ban ta a zato ba, na samu alheri iyakar alheri ga kayan jarirai ga atamfofi ga ku i ga kayan abinci komai alhamdulillah! Da dare bayan kowa ya watse Hajjo tace a rufe gidan Yau Deeni bai kwana gidan duk rashin kunyarsa, sai da gabana ya fa i jin maganar Hajjo, domin nasan wani sabon tashin hankalin ne zan afka idan suka tafi suka barni da Deeni. Ya kuwa dawo yaita buga gidan, Hajjo da kanta ta le a tace , "Kai Deeni wai mu in sa'anninka ne? Koko akwai sa'arka a cikinmu ne? Ban san rashin kunya maza ka ba mutane waje tunda baka san abin da kake ba." Ta maida gidan ta rufe ta barci a tsaye yana kallonta. Ta dawo tana ta fa a tana cewa da nan garin nake sai na saka iyayenta sun gyara mai zama wallahi shegen yaro ko kyan kirki babu sai rashin kunya da rashin sanin darajar mutane, ban san uban da ya yi ma shi jagorancin auren yarinyar kirki irin Jiddah ba." Nan fa mutane kowa ya yo caaa! Da abin da yake cewa,kowa na fa in kalar rashin darajar da Deeni ya yi a gabansa. Ni dai Salati kawai nake ina neman mafita gun Ubangiji kan abin da Hajjo ta jawo min Yau. Sun jima suna ta ban shawarar na daina nuna mai tsoro na daina barinsa yana taka ni na zama mace na nuna mai nasan ciwon kaina idan ba haka ba kasheni zai a banza ya auro wata hankalinsa kwance. Ni dai jinsu kawai nake ban jin na auki shawara guda a gunsu. Bayan sun gama maganar Deeni aka fito da duk abin da na samu aka irga ku i Naira dubu arba'in da takwas da canji , sai turmin atamfa guda goma sha aya kayan jarirai ne ba a irga ba, saboda ance yaron dama bai da kaya. Hajjo ta dube ni tace, "Jiddah yanzu wane shawara kika yanke akan ku enki? Zannuwan dai dama an gaya min an sace maki kayan lefe don haka ki aje abinki a hankali ki dinga inka abin ki tunda Allah Ya baki miji mugun gaske wanda bai san ha in aure ba, sai ki cire kala biyu ki ba da a kaiwa Mahaifiyarki ita ma ta ara tunda tana da bu ata itama, ku inma ki bata wani abu daga ciki sai ki samu sana'ar kirki ki fara yi saboda ki samu abin da za ki ri e kanki da yaronki." Kowa ya yi na'am da shawarar Hajjo, don haka na cire dubu goma sha biyar nace akaiwa mahaifiyata na ba Inna data zauna min dubu biyar na adana sauran ku in, zannuwan ma kala biyar na bata amma akace na bata uku nace a bata hu u Inna ta auki gudan. Washegari suka gyara min gidana fes suka wuce ina kuka Hajjo na kuka suka barni da wata tsohuwar da Hajjo tasa aka kira ta dinga zuwa safe da yamma tana ora min sanwar ruwan wanka tana yi ma yaron wanka kullum har mu yi arba'in. Sai yamma lis Deeni ya shigo gidan cikin matu acin rai da fusata tun daga bakin ofar gida yake a min kira. Mu ha u a kashi na gaba don jin yadda zata kaya tsakaninsu . Wace irin sana'a Jiddah zata yi? Wane irin mataki Deeni zai auka kan Jiddah? Taku a kullum Haupha [7/23, 8:49 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa