Sashe 58
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amma shi duk babu abin da matansa ke da ra'ayin yi daga ciki, idan ya yi magana suka saka ananan kayanma da ya shiga sashensu sai su dinga oyewa suna kakkarewa abin sai ya ba shi haushi kawai ya fice. Kallo guda ya sake bin ta da shi ya gyara kwanciyarsa, alamar bai da lokacinta. Ta fasa kuka ta zauna da as tana cewa, "Ai daman nasan ba zaka kula Ni ba tunda baka sona yanzu to wallahi nima yanzu haka ne kar kai tunanin akwai sauran ragi da ragowa a tsakaninmu." Tamkar zubar dalma kan rauni haka yake jin kalamanta, bai san yaushe za su gane gaskiya ba, bai san yaushe za su gyara halayensu ba, ji yake kaf duniyar yafi kowa damuwa indai maganar iyali ne. Yanzu yana sakinsu za a cigaba da saka shi bakin duniya kamar yadda yake ciki daman, mutane ba su yi mai uzuri ba su san gaskiyar komai ba amma shi suke cewa bai da halin kirki baki aya cewa ake bai iya ri on aure, babu irin maganganun da basu dawowa kunnenshi da ake yi na bai da kirki matansa wahala suke sha. Bai san lokacin da hawaye suka zubo mai ba, ya cigaba da hasaso muggan maganganun da ake yi kansa, duk dai akan matan nasa. An manta da cewa duk ba in halinsa da ace ya samu mace guda wadda zatai rayuwar aminci da mutunci da shi tabbas da kowa sai ya yi sha'awar gidansa. An manta da cewar mutum guda bai iya tafiyar da rayuwar farin ciki a zaman aure dole dai da taimakon abokin zamansa. An manta cewa shi namiji ne aiki yake zuwa fafutuka yake dare da rana don kawai ya ji da in rayuwarsa gidansa, domin da bai da iyalin wasu lamurran duk ba zai yi su ba amma a banza. Mutane sun manta cewa shi ne ya aje matan don haka shi ne ya kamata ace matan na bi suna yiwa ladabi da biyayya suna jin tausansa suna yi ma shi uzuri kan duk wasu ananan lamurran da suka shafi zaman gidan amma ba su iyawa. Me yasa shi ne kawai yake a matsanancin hali na rashin zaman lafiyar gidansa ne? Yana jin kamar ya mutu ko haka nan ya tuna matsalar gidansa, idan yaga abokansa na waya da matansu sai ya ji damuwa ta ziyarci zuciyarsa, shi bai san irin ai wasa da dariya ba da matar aurensa ba, kowacce jin kanta take tamkar uwargijiyarsa ba mai ba shi kulawa balle ta dinga fitar da lokacin jin damuwarsa, kowace daga cikinsu ta kanta da yaranta kawai sai jiran ta ga gazawarsa ta ci mai mutunci ko da kuwa a gaban yaransa ne kuwa ba su jin damuwa suke ci mai mutunci son ransu babu guda aya tilo da zai ware ya ce tana yi mai abin da yake so kowacce gani take bata da lokacin ba shi kulawa balle nuna mai tausayawa. Maryam ganin bata ita yake ta gama gaya mai magana ta fice tana sakin tsaki ta banko ofar da arfin tsiya. Kawai fashewa ya yi da kukan fili mai ratsa zuciya, kuka yake yana jin ina ma ace shi ne Salim? Ina ace shi ne ya mutu ya barsu ba Salim ba ne ya mutu? Cikin kukan yake cewa, "Salim ka huta da matsalar mace, ka tafi baka ajiye kowace mace ba balle ace ka ta a zubar mata da hawaye ka tafi salin alin ba ba in cikin aure a zuciyarka na tayaka murna Salim dama ni ne na mutu ba kai ba." Ya jima a yanayin kana ya tashi ya ha a ruwa ya yi wanka ga yunwa dake addabar shi domin ba komai a cikinsa tun safe daya fita sai ruwan Lipton ya dawo ya ci abinci ne aka ata mai rai ya fasa cin abincin sai kuma abincin yasa suka kama fa a kamar gidan mayunwata. Allah Ya sani yana bakin arinsa na fita ha insu ko da yaushe yana ba su abinci yana ba su duk abin da ya kamata amma da yake so suke su wula anta shi ga idanun mutane sai su dinga nuna bai masu komai, hakan yasa mutane ke zaginsa suna cewa bai iya ri e aure gidansa yunwa ke akwai. Yasha zuwa gaban Mamarsa ya yi ta kukan ba in ciki domin abin na damunsa sosai kamar shi a dinga cewa gidansa ba abinci babu kaza babu kaza. Ko da yaushe mahaifiyarsa na jajanta mai ta yi mai nasiha ta kuma yi mai kyakkyawar addu'a daga arshe ta rufe da mai albishir na samun wadda zata kula da shi duk daren da ewa indai ya ara ha uri domin Allah ba zai barshi a haka ba. Kalaman iyayensa da danginsa kawai ke sawa yana samun natsuwa amma ba don haka ba da Allah ka ai yasan yadda ba in ciki zai maida shi sanadin matansa. Tun daga ranar bai sake ganin Jiddah ba har ya amince da ta koma wannan karon ma bai amayar da abin da ke cinsa a rai ba game da ita ba, duk da cewar babu abin da ya sauya na daga halayen matansa sai dai a yanzu su biyu ne kawai suka rage ya saki amaryar tunda haka take bu ata ya gaji da zuwa ban ha uri iyayenta da ita kanta na ci mai mutunci suna tozarta shi, don haka ya yanke shawarar sakinta duk da yasan hakan zai ara ma mutane aimi gun ba shi ba ar sheda amma ya zai yi ? Ai Allah Yasan abin da ke faruwa kuma ba laifinsa ba ne ba. Jiddah satin ta biyu ta koma gida, zuwa lokacin ta saba da Abubakar a waya ko da yaushe yana kiranta su sha fira duk da ba firar soyayya suke ba, domin ta gaya mai gaskiya ita ta gama soyayya don haka kar da ya auka akwai so a tsakaninsu, shi kuma ya amince da hakan don haka ala ar ta jima a tsakaninsu har aka koma makaranta sai suka yi wata irin muguwar sha uwa ta gasken-gaske wadda babu wanda zai yarda ba soyayya bace a tsakaninsu ba. Domin dai Abubakar ya riga ya fahimci Jiddah mace ce mai son kulawa da nuna mata soyayya a zahiri tare da sakata a cikin nisha i ko da yaushe don haka sai ya yi amfani da damar wajen shiga jikin Jiddah ba tare da ita kanta ta ankara da hakan ba, sai dai ta wayi gari ta ganta cikin aunarsa kawai ba tare da tasan daga ina ta faro soyayyar ba. Da farko ta damu, amma daga baya data tuna da yadda yake sonta yake nuna mata kulawa ga gaban kowa nuna wa yake tafi kowa gunsa sai ta ji sau i ta ji ba komai bane don ta amince da soyayya da shi ba, don haka sai kawai ta saki jiki suka dinga wata irin soyayya mai ban mamaki wadda baki aya makarantar kowa yasan Jiddah da Abubakar masoya ne. Daga ita har shi babu mai kula wani da sunan soyayya sun yarda da juna sun amince da juna ko da yaushe tsara rayuwar aurensu suke idan suka gama karatunsu domin ya fita da aji biyu. Duk wanda ya zo ga Jiddah da maganar soyayya kai tsaye zata ba shi ha uri ta are da ba shi labarin Abubakar da yadda suke son junansu, hakan yasa Jiddah bata da masoyi idan ba Abubakar ba, shi ka ai ne burinta shi ne damuwarta shi ne fatanta, duk lokacin da ake maganar rashin cika al awarin maza kan aure Jiddah kan cire Abubakar a jerin mazan takan ce, "Shi in na daban ne, haka yasan darajar soyayya da sanin martabar ta don haka bata ji ko da wasa Abubakar zai zama aya daga jerin maza masu karya al awarin masoyansu. Wasa-wasa Jiddah tai nisa a soyayyar Abubakar wanda hatta gidansu kowa yasan da zaman Abubakar a rayuwar Jiddah, zuwa yanzu Jiddah ta zama babbar ar kasuwa babu abin da bata saidawa, kasancewarta mai kyauta yasa ko da yaushe ita ce ke hidima da Abubakar bata damu da yadda suke ba, na yadda ko da yaushe kiran waya ne kawai ke ha a ta da Abubakar ba wani kyauta ba komai, amma ita duk lokacin da ta saro kaya takan za i wanda su kai mata kyau ta kai ma shi, hatta makaranta ita ce ke saimai duk abin da yake so ko ya nuna ko bai nuna ba, ku i ne kawai tsabar su bata iya ba shi, amma abin ku i ko ya kai na nawa tana iya ba shi kyauta. Da dama awayenta na yi mata fa a kan hakan amma takan ce ita duk abin da tai ma Abubakar ba wani abu bane idan aka ha a da yadda yake nuna mata soyayya da kulawa ba, don haka ita ba soyayyar ku i ce a tsakaninsu ba soyayyar aure ce a tsakaninsu don haka ya adana ku insa idan su kai aure ya bata. Babu irin shawara da zugar da awayenta basu bata ba amma a banza jin su kawai take, duk lokacin data fahimci yana cikin matsalar wani abu takan yi mai abin kanta tsaye. Yana yawan gode mata ya ce Allah Ya ba shi ikon cika burinsa kanta na yi mata alheri ninkin wanda take mai ko da yaushe amma ita bata son yana maganar ma sam. Suna a haka ne ya nuna mata filinsa daya siya tai ta murna sosai domin tasan ita ce za a saka a gidan, hakan yasa ta hana shi kashe ku i wajen wasu abubuwan duk ta sake auke mai nauyinsu ta cigaba da ba shi shawarar yadda za a gina gidan domin yana amsar ku in gwamnati na S POWER da ake biya duk wata-wata. Nan da nan ya fara tara ku insa ya fara haramai ginin gidansa wanda ko bulo aka siya sai ya nuna mata shi ta hoto abin na yi mata da i yadda Abubakar ke nuna mata komai na shi ita ce kan gaba, domin hatta tsarin gidan ita ce ta nuna mai yadda take son gidan nasu ya kasance kuma hakan ake yi komai yadda tace haka yake yin shi hatta shibkokin gidan duk ita