← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 133

Sashe 124

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

alheri da fatan zaman lafiya, ya kawo ku i yaba Jiddah ya ce ta basu idan za su tafi zai an fita ya je ya dawo. Ta basu ku in sunata godiya tabi bayan shi yana tsaye yana kallon ofar akin da tsammanin fitowarta . Tana zuwa ya bu e hannu ta fa a ciki ya maida ya rufe suka dinga saukar da ajiyar zuciya. A cikin kunnenta ya ra a mata, "Zan fita Princess ba jimawa zan ba zan dawo, zan je nima nayi bankwana da wa anda suka zo daga wasu garuruwan an'uwan Mamana." Cike da kulawa tace mai, "Allah Ya tsare min kai, Ya kiyaye min kai, Ya Kai ka lafiya Ya dawo min da kai lafiya Prince. Ina fatan zaka runtse Idonka daga kallon kowace mace, idan ma tsautsai yasa ka kalla kaga abin da ya birgeka a jikinta don Allah ka kira Ni a waya ko ka turomin message ka fa a min ko miye kafin ka dawo na tanadar maka ko miye ma." Suka ha e bakinsu waje guda suna kissing in juna na tsawon lokaci, sannan ta zare jikinta tana sake maimaita mai addu'a yana amsawa da "Amin Princess, sai na dawo ki kulamin da kanki sosai don Allah ban da aiki ki kwanta ki huta har in dawo." Murmushi tai tana sake aga mai hannu har ya fice daga gidan. Mutane da dama suka dinga shigowa ganin amarya da akin amarya, amma ita hankalinta na kan wayarta da suke chat suna waya da Prince inta yana gaya mata yadda yai kewarta itama tana gaya mai yadda tai tata kewar har tana cewa ta rame ita dai ya dawo gida haka nan ko ta saka mai kuka. Jin hakan yasa ya ru e ya ce mata ga shi nan zuwa yanzu insha Allah yana hanya. Ko da jin haka sai ta tashi da sauri ta shiga kicin kasancewar ta bada an siyo mata kayan miya da kifi ta ora taliya ta gama ta yi mai gurasa ta ha a lemu mai da i ta saka a fridge sannan ta shiga wanka tana fitowa matan dake gidan suka ce za su tafi ta zuba masu kayan biki ta raka su ta rufe gidan da niyyar ba zata sake bu e wa kowa ba sai Prince inta. ananan kaya ta auko masu kyau ta saka tai bala'in kyau a cikin kayan domin komai ya amsa sunansa a jikinta ya kuma bayyana ta fesa turare ta sake gyara ko'ina ta dawo kan kujera ta zauna ta kira shi a waya amma har wayar ta katse bai auka ba, sai ta samu kanta da turawa mai sa "Idanuwana sun rufe, kunnuwana sun toshe, jikina ya yi yaushi miyan bakina ya auke duk don rashin dawowar Prince gida da wuri, don Allah ka dawo gida ina son jinka kusa da Ni Prince cike nake da kewarka tunda ka fita." Yana ta sauri yabar gun abokansa sun ri e shi, ga shi hankalinsa na kan Princess insa, yana ganin kiran ya kasa amsawa ne saboda bai taho ba, sai dai ganin sa on yasa ya mi e tsaye duk da tsiyar da su angote ke mai ya nufi gidan. Sai da ya shiga unguwar sannan ya tsaya ya kira ta, tana auka ta fashe da kukan shagwa a. Baki aya ya rikice ya kama lallashinta. "Afuwan Princess ga Ni nan yanzu haka cikin unguwa ina hango ofar gidanma yanzu haka." Cike da shagwa a tace, "Na kusa mutuwa saboda kewarka Prince don Allah ka dawo ina jiran ka ko abinci ban ci ba sai ka zo mu ci kuma fa yunwa nake ji sosai Ni ." "Yanzu -yanzu za ki ganni Princess gaskiya ban kyauta ba ai min afuwa." Mintina ka an ta ji shi yana buga gidan, sai da sake fesa turare sannan ta nufi ofar tana bu e mai suka rungume juna tana sauke ajiyar zuciya ta tamkar wadda tai kuka da gasken-gaske. Shi kuma ya dinga shafa bayanta yana sunsunar wuyanta a hankali yana ra a mata kalaman auna da yaba kwalliyar da tai. Sannan ta ago tana murmushi ta sumbace shi ta sake shigewa jikinsa tana cewa "Oyoyo Prince, sannu da dawowa, Allah nayi kewarka sosai, shin ka manta da Ni ne yasa baka waigo gida ba tunda ka fita?" Cike da farin cikin ganinta ya ce, "Haba Princess taya zan manta da ke bayan ke ce rayuwata baki aya." Cikin aki suka nufa, kan kujera ya zauna ta ebo mai ruwa mai an sanyi ta ba shi a baki ya sha, sannan ta fara jera mai sannu kamar wanda ya yi wani uban aiki. Shi kam ji yake baki aya duk wani burinsa ya gama cika tunda har ya mamaki Jiddah matsayin matarsa kuma ta kasance irin macen da yake so ciki da waje. Allah Sarki Salim ina ma ace kana raye da kaga yadda anwarka ke sakani nisha i ta sakani cikin aminci da walwala yadda nake fata nake buri. Sai da ta tabbatar da ya an huta sannan ta ja hannunsa suka nufi inda ta ha a kayan abincin. Tunda suka doshi gun yake jin amshin abincin har miyansa ya fara tsinkewa. Cikin natsuwa ta zaunar da shi ta fara zuba abincin tana jerawa gabansa shi kuma sai aikin kallonta kawai yake yana jiran ta gama ya fara tada saiti. Kamar yadda ya zata dai, ita ta dinga ba shi abincin har zuwa lokacin da ya ji cikinsa ya fara nauyi sannan shima ya fara bata a baki. Sai da ya ci mai an dama daga gurasar har taliyar sannan ya ora da lemu mai sanyi suka koma kan kujera ta shige jikinsa ta fara karanta mai wani littafi da take karantawa yana sauraren ta. Suna cikin karatun suka ji sallamar Bilkisu, ta amsa mata sallamar ta an zame daga jikinsa ba tare da ta tashi baki aya ba. Bilkisu na shigowa tana cewa, "Mun zo mu ga gidan amarya wankakka da sabulu da mai... Tai shiru ganin Mustapha kwance cikin kujera Jiddah na kishingi e a rabin jikinsa. Tai baya da sauri wai irin abin nan maigida ya shige aki ko ya fice anyi ba Jiddah tai murmushi tace, "Ban gane komawa ba, kina nufin ba onki ne Prince in ko me?" Daga can tsakar gidan Bilkisu ta saka dariya tana cewa, "Ke Ni ban san iskanci ce maki nai ba ona ne Mustaphan?" Sai ta sake dawowa cikin falon. Shi dai ko kallo bata ishe shi ba, balle ya daina wasa da kitson Jiddah da yake, har sai da Bilkisun ta gaida shi sannan ya amsa yai mata kallo guda darajar yaron dake bayanta yana ma yaron wasa. Ganin ta tukara a zaman wajen yasa Jiddah jan Prince cikin akinta suka bar Bilkisun a nan. Suna shiga ya fara sunsunar wuyanta yana jan ta, so yake ya biye mai su bar Bilkisu a falo don haka ta samu da yar ta lalla a shi ta fice gun Bilkisun. Tana zaune sai kalle-kalle take tana jinjina kanta, Jiddar ta fita, suka kalli juna Jiddah tai murmushi ya yin da Bilkisun tace murya asa - asa "Amarya kin iya kama angoki tun jiya ake nemansa gidansa ba a ganshi ba har yanzu ashe yana nan ana shan madarar auna ta shekaru da aka kwashe ana zabgawa." Jiddah tai murmushi domin tuni Bilkisu ta fice mata a rai ta san dai gulma ce kawai ta kawo ta, don haka zata yi iyakar yinta ta bar gidan shike nan. Abinci ta zubo mata da kayan biki ta zauna sai dai sam ta kasa sakin jiki da Bilkisun domin ta san cewar Bilkisu awar Maryam ce don haka dole ta kiyaye abubuwa da dama idan tana son kare kanta daga sabgar tsegumi da gulmace-gulmace irin na Bilkisun. "Shegiya awata sai da kika dai aure Prince in nan hankalinki ya kwanta, kin zo daga sama kin wace ma mata miji sai yadda ki kai da shi, naji ana cewa bayan lefen da ya yi maki har wasu ku i ya baki wai kiyi siyayyar abin da baki da shi ko?" Ta idasa maganar tana kallon kayan dake tsaune a falon masu matu ar tsada. Jiddah ta dubeta sai kuma tai dariya tace, "Ai ke dai bari kawai ko da yaushe cikin yi wa Allah godiya nake daya azurtani da miji irin Prince ban san wane irin farin ciki yake ban ba domin abin yafi kwatance balle misali, ai shi komai nashi nawa ne daman don haka kar ki yi mamakin komai aka ce ya yi min zai iya don yana aunata kamar yadda nake aunarsa." ut, Bilkisu ta ha e miyau ta mi e tsaye"To Jiddah ni zan tafi sai anjima Allah Ya bada zaman lafiya Yasa a jima tare." Jiddah ta gyara zamanta sosai alamar ba zata iya ko rakata ba tace, "Amin Ya Allah zama kam ai mun fara kenan ba maganar tafiya ko rashin arko." Bayan tafiyar Bilkisu ba jimawa Prince ya fito zai tafi Jiddah ta raka shi tana shagwa ar kar da ya jima ya dawo da wuri ita dai. Gidansa kai tsaye ya nufa fuskarsa fal fara'a da farin ciki ba alamar damuwa ko ka an a tare da shi. Matan gidan na aki kowace tana jin yana sallama amma ba wadda ta samu ikon amsa mai sallamar balle a le o ai mai tarba ta musamman. Ya bi yaran duka yai masu magana kana ya bu akinsa ya shige yana jin kewar Jiddah fal a ransa, da ace gidanta ne ya je da yanzu tana jikinsa tana masa sannu da zuwa ta ba shi lemu ko ruwa mai sanyi tana shagwa a tana ba shi har sai ya oshi ta ja shi zuwa toilet tai mai wanka ta tsane mai jiki tai mai shafa ta fesa mai turare. Kan gadonsa ya fa a yana hasko jiya zuwa Yau kawai irin nau'in ni'imar da ya kwasa gun Jiddar... "To marar adalci, wanda bai san Annabi Ya faku ba, ashe kai ka sai mata kayan akin da nake jin ana cewa sun yi kyau? To wallahi Allah Ya Isa kuma sai ka ban nawa ha in dole tunda ba tsoron wani nake ba." Hafsat ce tsaye kansa take ta masifa ta
Chapter 124 · 0% Book details