← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 133

Sashe 120

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

haka suka dinga ihun murnar zuwan Jiddah gidan nasu. Lokaci ka an kowa ya hallara don haka Mustapha ya gaida kowa ya gabatar da kansa matsayin wanda ke neman auren Jiddah ba musu kowa ya amince to daman wane musu za su yi tunda ba wanda ke ci da ita ko shayar da ita balle ya damu da halin da take ciki ko a baya balle yanzu? Washe gari Baffa ya zo da tarin mutanensa inda dangin Mustapha suka iso suma da zummar kawo ku in neman aure sai dai labarin ya sha bamban inda nan take aka ce a bada ku in sadaki dana jin magana da komai a aura auren. Cikin ikon Allah mutane suka shaida aurin auren Hawwa'u da Mustapha akan sadaki naira dubi hamsin cif. Nan da nan bakin ango ya kasa rufuwa ya dinga kiran abokai da an'uwa yana gaya masu an aura mai aure da Jiddah yanzu haka a Jalingo. Cikin murna ya kira matarsa Maryam ya gaya mata an aura aurensa da Jiddah tai ta ruwan masifa da bala'in nan za a zo a iske su a tai a barsu dai. Washegari aka dunguma baki aya har da Baban Jiddah sai Kano don ganin inda za a aje Jiddah. Gida mai kyan gaske kuwa aka kai kayan Jiddah wanda tsayawa bayyana su abin kamar auyanci ne, saitin kaya biyu masu kyan gaske an yayi Baffa ya yi ma Jiddah da kujerunta masu kyau komai ya ji a gidan sai fatan zaman lafiya ga masu gidan kawai. An tsaida lokaci Jiddah zata tare gidanta bayan sati biyu cif wanda hakan sam bai ma ango da i ba ji yake tamkar an ce sai bayan shekara biyu Jiddah zata tare a gidan nashi. Jiddah kuwa ta ji da in hakan don ba shirin da tai, don haka cikin lokaci suka fara kimtsawa ita da Alawiyya, ba a bar Iyami (Jiddah) a baya ba itama ta tashi tsaye ta shiga kimtsa Jiddah ta ko'ina Jiddah amsar kayan gyaran jiki take hakan yasa duk lokacin da suka ha u da Prince sai ta yi da gaske suke rabuwa sai ya bi ya narke ya koma abin tausayi ya ce bata jin tausansa ta daina sonsa orafi kala-kala kuma wai sati biyun ta i yi ma shi ina zai sa kansa? Duk inda Jiddah ta saka afa Mustapha na biye da ita, haka duk inda zai je tana tare da shi hakan yasa Hajjo ta agara su tare gidansu ma a huta da nacin da Mustapha ke yi duk da yadda matansa ke ruwan masifa da aiken ba en maganganu abin bai mata da i amma ta lura ita uwar gayyar ko a jikinta harkar gabanta kawai take ba ruwanta da ananan lamurran da ake yi kanta da mijin nata. Bayan sati biyu Tunda safe ya kira Alawiyya a waya yana tambayarta yanzu za a zo aukar amarya ko ko sai da rana?" Abin dariya ya ba Alawiyya ta dubi agogo taga arfe bakwai na safe amma yake kiran yanzu za a zo aukar amarya, lallai Mustapha abin nashi azimun ne don haka sai tace ka kira Hajjo ka ji man ai sune masu bada amaryar. Jiddah na gefen Alawiyya ta dubeta suka fashe da dariya suka tafa , Alawiyya tace "Ke nifa ban ga laifinsa ba taya ina da mata kamar ke ace kina can ina can? Tab ai kawai ya yi magana akai mai matarsa kowa ya huta shima ya huta kema tsohuwar munafuka ki huta. Yawwa wai ya akai kika gayama Yusuf Matashi za ki aure har naga ya aiko maki da sa on Allah Yasa alheri da kyautar girma Jiddah?" Jiddah tai murmushi tace, "Ranar da muka fito kotu kan case in Abubakar a ranar ya turomin da hotonsa da wata yarinya ya ce min ita ce za in da mahaifiyarsa tai mai ta kuma yi rantsuwa cewar ba zai auri Lauya ba ar wuta ba ya kai mata cikin zuri'a ba. Hakan yasa yake ban ha uri don Allah na yafe masa amma don Allah kar da mu yanke zumunci nayi murmushi nace abin ya yi min da i don haka bayan kwana biyu na tura mai hotona da Prince nace mai ga wanda zan aura an'uwana ne. Shike nan yanzu haka maganar da nake maki suna matu ar mutunci da Prince nima ina gaisawa da matarsa Hanan sunce ma yau za su zo gun tare wa ta insha Allah." "Kai Jiddah tabbas kina da sa'a a rayuwarki duk yadda abu ya dun ule maki sai kinga inda haske ya fito ya warware maki shi." Cewar Alawiyya kenan tana murmushi. Da yamma aka auki amarya sai gidan mijinta kuma Prince inta. Mahaifinta ya jima yana mata nasiha haka ma su Baffa sun yi mata nasiha sosai ta zauna gidanta lafiya da abokan zamanta kar da ta zama silar damuwa ga mijinta. Bayan kowa ya watse ne Alawiyya ta dubi Mustapha tace, "A al'adarmu bayan an kawo amarya an watse Ni zan sake aukar amarya na kaita gidana tayi sati biyu sannan na dawo da ita akinta." Ya zabura ya mi e tsaye sai kuma ya zauna ya ce, "Amma da Ni za ki tafi ko? Don Wallahi Yau ba zan iya rayuwa ba sai naga matata cikin akina." Jiddah sai dariya take tana oyewa don tasan zolaya ce kawai take mai. Sai da Mustapha ya haukace ya fara rantse-rantsen sai dai a tafi da shi sannan Alawiyya ta kwashe da dariya tace, "Ku in sayen baki kawai zaka ban na wuce mijina nacan na jirana ." Sai lokacin ya sauke ajiyar zuciya ya fito da ku i masu dama ya bata ya bu e mata ofar fita ya ce, "Ranki ya da e mu tashi lafiya sai Allah Ya kaimu." Wannan karon dole dariyar Jiddah ta bayyana ta mi e ta raka Alawiyya har wajen motarsu Faisal na ciki na jiranta. Bayan sun tafi ne sun dawo cikin aki cikin hanzari Jiddah ta fa a toilet ta ha a ruwan wanka ta zuba kayan amshi ta kira Prince tace ya yi wanka ya samu sau in gajiya. Yana shiga ta koma aki da zummar fito mai da kayan da zai saka marassa nauyi sai wayarta ta hau ara ta auka Alawiyya ce ta sake kira tai mata sharhi sai kuma taji sa anin hakan don bata duba lambar ba daman. "Sannu amarya, ina maki barka da zuwa gidan tashin hankali da rashin kwanciyar hankali tattare da gur acewar rayuwa! Ba dai kin shiga gidan Mustapha ba? To ki sani kin kawo kanki a gidan matsala don ko shi maigidan bai isa ya aiwatar da abin da yake so ba haka bai isa ya saka ba balle ya hana ba. Ina jajanta maki zuwa cikin gidan Mustapha Jiddah za ki gane kurenki za ki nadama da danasani saboda za mu gwabza kishin bal-bal dake a cikin gidan nan zamu fitar dake ko ta halin anikayi saboda mune kawai zamu iya rayuwa a gidan Mustapha. Ba yana tunanin ya auri wayayyar mace ba wadda zata mantar da shi ba in cikin gidansa ba? To ina so ki sani ke baki isa haifar masa da ko da rabin farin ciki ba indai ina raye." Kit ta kashe wayar tabar Jiddah da waya ri e a hannu tana murmushi madadin ata fuska. Cikin fara'a ta adana lambar wayar ta saka sunan mai lambar tana jin ta samu matakin farko na samun abin da take nema a gidan Prince. Kamar yadda matarsa tai alwashin sai ta wargaza mata aure sai ta saka ta cikin kishin bal-bal ta raba ta da jin da in aure to itama tai al awarin sai ta gyara gidan Prince sai ta maida mai gida tamkar gidan lumana da farin ciki haka zalika sai ta gyara mai duk wata matsala ta gidansa ta inke mai duk wata waraka da take bayyane cikin gidan nashi sai an wayi gari ana cewa gidan Mustapha gwanin ban sha'awa sai an dinga kwatancen matan Mustapha da mata masu saka mijinsu farin ciki da walwala insha Allah sai samunsa ya sake yawaita ya ara cigaba a rayuwarsa fiye da baya. shi ne al awarin da Jiddah taima kanta na gyara gidan Mustapha a daren farkonta. To jama'a sai mu bi page na gaba don jin wane irin kishi ne na bal-bal da za a kwabsa tsakanin matan Mustapha da Jiddah? Shin Mustapha zai zama mai cika ma Jiddah al awarin daya aukar mata na share mata hawayenta na shekara da shekaru? Shin da gaske Mustapha ne mai matsala ko matansa ne masu matsala? Ta wace hanya Jiddah zata bi don warware duk wani ba in hali da ta samu ga Mustapha? Ku biyo Haupha [11/5/2022, 9:27 PM] Haupha: *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa
Chapter 120 · 0% Book details