← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 133

Sashe 96

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ku in aikinsu na shekara biyu, bai bata ko sisi ba kuma bai nemi shawararta ba kan lamarin duk da cewar tun suna yara ya sake ta ya amshe gidan da suke ciki duk da cewar nata ne na gado ya amshi dukiyarta da sunan zai juya mata sai kawai gani tai ya kama gyaran gida ya sai mota, bata san hawa ba bata san sauka ba sai ganin masu gini tai sun shigo sun kama aikin gini, yana dawowa tai mai magana ya ce tasa mai ido ba ruwanta. Karshe dai sai ga motar kawo amarya an kawo an saka ta cikin fallelen akin da aka gini, bata samu damar tanka mai ba washegari ya dan ara mata takardar saki uku ya ce tabar mai gidansa idan tana da mai iya wace mata kuma ta turo ya amsar mata. Hakan duk bai ata mata rai ba ta ha e fushin ta zata tafi ya ce kar ta bar mai yaro ko guda ya bar mata su, don ba abin da ya'ya mata za su tsinana mai a rayuwa. Haka ta nufi gun danginta ashe suma duk ya bi su ya yi mata sharri don haka suka kore ta ita da yaranta arshe gidan haya suka kama ta ci gaba da sana'ar saida abinci tana biyan ku in haya shi ne yanzu yaran duk sun girma har biyu sun samu mijin aure zai kama su ya kai su Makkah aikatau don shi azzalumi ne na gaske." Alawiyya tai ajiyar zuciya tace, "Lallai ya kamata a watar masu ancin su, amma me zai hana ki bu e ofis kema kamar yadda na bu e a Kano? Sai inga sai kin fi samun damar taimakawa duk wanda ya kamata Jiddah." Jiddah ta jinjina kanta kamar mai tunani tace, "Kin kawo shawara kema amma fa karatu zan koma har Baffa ya gama yi min komai. Amma duk da haka akwai lokacin da zan ware don hakan insha Allah." Wayar Jiddah tai haske alamar kira zai shigo, sai ga wata wa a mai da in gaske ta indiya na tashi daga wayar. Alawiyya na ganin yadda Jiddah ke murmushi alamar taji da in kiran wayar da akai mata. Furucinta na farko yasa ta gane da wanda take waya, Mustapha ne ko tace Prince kamar yadda taji Jiddah ta ambata. Ba kunya Jiddah ta saki baki ta dinga yi ma Prince inta shagwa a abin kamar a mafarki haka Alawiyya take ganin lamarin yadda Jiddah ke waya cikin shau i da farin ciki ta kuma soyayya wayar. Ita kanta Jiddah ta birgeta ina ga shi wanda ake abin don shi? Haka take raya wa a ranta, lalle ne Mustapha shi ne za in Jiddah kuma Jiddah ita ce za in Mustapha don ga alama sun ha u a maha ar da kowane daga cikinsu ke so. Jiddah ga alama ta manta da Alawiyya dake zaune baki bu e tana kallonta cike da mamaki sai kalamai suke musaya ita da Prince inta zuwa can ta marairaice murya ita ala dole kuka take yi. Lallai ta tausaya wa matan Mustapha indai ba su kasance yadda yake ba to tabbas akwai daru a gaban Jiddah don za su ce ne ta asirce masu miji ta mallake shi, tunda zuciya na san mai kyautata mata kuma ga alama Jiddah ta dage gun hakan. Sun jima suna wayar wadda farin ciki ke aruwa duk bayan kalma guda da Jiddah ke ambata a kan fuskarta. Alawiyya tasan daman can Jiddah akwaita da son rayuwar soyayya don haka ne ma tafi kallon Film in indiya akan na Hausa ko da suna gun Iyami idan suka saci jiki suna zuwa kallo gidansu wata Badiyya to indai Hausa ne Alawiyya ke murna amma idan suka iske an saka indiya Jiddah ke murna har da rawa, musamman idan Film in jaruminta ne Rothick Roshan. Ko haka nan suna maganar soyayya idan suka ga wasu na fira Jiddah kan ta e bakinta tace, "Ni fa ba kowace soyayya ke birgeni ba, kamar yadda ba kowane namiji ke birgeni ba. Idan ta ga wani an gayu tace "wannan kam ya birgeni sosai. Idan taga wanda bai da tsabta takan ce, "Wannan kuwa ko za a ha a min da kyautar gidanmu ba zan amshi soyayyarsa ba." Tun fil'azal Jiddah tana son soyayya tana son mai kyau haka tsabta na matu ar jan ra'ayinta kan kallon namiji idan suna tafiya. Sun kwashi awowi suna ta shan soyayyarsu wadda har Alawiyya ta gaji ta tashi ta fice tana jinjina wannan lamari na Prince da Princess insa. Washegari da wuri suka shirya zuwa kotun saboda da abin kowace daga cikinsu ta kwana, suna shiga kotun an jarida su kai masu caa, domin zuwa yanzu sunansu ya kewaye ko'ina da ance Barista Alawiyya za a ce Barista Jiddah. Bayan kowa ya natsu ne aka fara shari'a mai cike da son kai da nuna rashin adalci arara, wanda hakan ya fusata Barista Jiddah tace zata shigar da shi kanshi Al alin ara bayan kammala shari'ar. Kasancewar da dama sun san waye Al ali Mansur sun fahimci kuma shi ne ke mara ma Barista Jiddah baya kan kowace shari'ar da take yasa wasu ke ba Al alin shawarar ya yi adalci idanma cin hanci ya amsa ya maida ya yi shari'ar gaskiya kafin an jarida su fara watsa labarai musamman da suka fahimci yadda zukatan Baristocin suka hasala har ta kai ga Barista Jiddah tace ta aje shari'ar amma tana gayyatarsa babbar kotu don ya kare kansa. Abin da Al alin bai sani ba ashe hada an gidan talabijin da rediyo suka halarci shari'ar kowane ya auki abin da ke faruwa ya watsa. Abin da ya ja hankalin sauran Al alai kenan suka yo mai caa kowa na cewa zai zubar masu da mutunci, a nan take aka aiko da takarda an maida shari'ar babban kotu dake high court dake Abuja. Abin da ya ara aukaka sunan Barista Jiddah kenan nan da nan sunanta ya dinga yawo a jaridu da gidajen rediyo da talabijin. A can ne ta ha u da wani matashi wanda ya ji u da Naira ya sha karatu har ya oshi ya nace mata kan yana son ta. Hon. Yusuf Matashi shi ne sunansa, an siyasa ne kyakkyawa ajin farko a kyawu yana rayuwarsa a Abuja amma siyasa tasa babu inda bai sani ba, haka ba inda bai da masana'anta ya ha a kasuwanci da siyasa yana yi kuma ba laifi komai na tafiya yadda ya kamata gare shi. Lokacin da akai shari'ar ne ya ga Jiddah nan take ya ji duk duniya bai da wadda yake so yaga dacewarsa da ita irin Jiddah, duk da cewar akwai tarin an mata an masu hannu da shuni dake bibiyar rayuwarsa domin ya kula su amma abin ya ci tura, wasu sun sha yi mai tayin kansu ko da na rana guda ne amma ba tasu yake ba. Shi kansa mamakin kansa yake yadda kallo guda yai mata wani kakkaifan abu ya fito daga idonta ya shige cikin nashi idanun ya bi jikinsa ya shige kowace kafa ta jikinsa. Ita kam Jiddah bata san wainar da yake toyawa ba, tana gama shari'arta suka ara kwana biyu ita da Alawiyya suka dawo gida cike da farin cikin nasarar da suka samu, wanda akai ta kawo kyautuka ana ba Barista Jiddah saboda jin da in namijin arin da tai gun watarwa matar nan ha inta ita da yaranta, ta kuma watarwa yarinyar da anin mahaifinta ya lalata a lokaci guda duk da cewar manyan shari'ar gaske ne duka biyun amma ta ha a su ta make lokaci guda. Dr. Faisal da gaske abin ya fara damunsa na Alawiyya kwata-kwata ba tashi take ba, sai dai ya gani a labarai tai kaza tai kaza baki aya bai cikin tunanin ta, abin da ya fara ba shi tsoro kenan ya shiga damuwa ya je kai tsaye ya samu mahaifinta da maganar. Sai dai shima kamar yadda kowa ya nuna ba ruwansa da sha'anin su haka ya ce mai ba ruwansa da shiga abin da ba ruwansa sun fi kusa. Iyakar tashin hankali yana ciki sai kuma ga sa on ta wai ya sake ta ko ya samu takardar sammaci ko da yaushe. Ranar ya tarkata ya nufi Kadunar hankali tashe, domin yasan wace ce Alawiyya akwai ta da kafiya da naci da aukar wa kanta abu komin wahalar da zata sha indai tasa kanta bata ganin wahalar sa. A kar cat ya isa gidan, amma ba wanda ya kula da ko zuwansa a gidan sai yaran Jiddah kyawawan gaske da su. Yana zaune yaran nata wasansu yana kallonsu yana tuno yaransa su Anam da Ammar yana murmushi hakimar ta fito cikin shirinta na barin gidan tana waya, ko kallon inda yake ba tai ta nemi wucewa. Sakin baki ya yi yana kallonta yadda tai wani kyau na daban ta sauya ta ara haske na ban mamaki komai ya ji tamkar wata ar shekaru ashirin. Ganin zata bar shi zaune yasa ya jawo gyalenta ta baya tilas ta juyo, ta watsa mai idanunta masu haske da kaifi. Lumshe idonsa ya yi yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa kamar zata fito don fargaba saboda yasan yadda kallon matar tashi yake yasan mai ke biyowa baya idan ta yi shi. Tamkar bata san shi ba, tamkar Yau ta fara ganinsa haka take binsa da kallo, abin da yasa yaran suka zubo masu ido suna are masu kallo tamkar sun samu talabijin. Jiddah da akai ma waya ana kiranta bakin get ta fito cikin takunta tana tunanin waye ya ke kiranta ta amshi sa o kuma wai daga Abuja? Ta ga yaran sun yi zuru suna kallon su, tai murmushi ta kama yaran ta tura su aki, ita kuma ta ra a ma'auratan ta fice tana murmushin yadda ko kallo bata ishi Faisal ba duk yadda yake zuzuta mata yadda yake aunarta yake burin aurenta, Yau ga shi gaban matarsa ya zama abin tausayi ba ta ita yake ba ta kansa ma yake. Tana fita ta iske mutane biyu kallo guda tai masu ta fahimci tabbas duk inda suka fito su in ma'aikata ne. Bayan sun gaisa ne guda daga cikinsu ya bata wata takarda da makulli ya ce,
Chapter 96 · 0% Book details