← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 133

Sashe 112

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma ya tsugunna ya kama afarta yana cewa, "Don Allah ki taimaka min kar da ki tuna baya ki taimaka ki yi min abin da Ni na kasa yi maki watau halacci ki ceci rayuwata daga angin data afka don darajar Allah Jiddah." Bata gane shi ba, ga dai shi kamar ta so tasan fuskar amma ta kasa tuna inda tasan fuskar don haka ta janje afarta tace, "Bawan Allah tashi ka zauna ka gaya min waye kai. Wane halacci ne zan maka?" Sadda kansa asa ya yi ya ce, "Tabbas nasan daman ba za ki iya gane Ni ba a yanayin da kika ganni yanzu ba Jiddah, amma hakan duk ya faru ne saboda sakayyarki da ke bibiyar rayuwata ta hanyar mallakar wata hatsabibiyar da ke ce ya kamata ki zauna inda take." Sai kanta ya aure ta rasa inda zancen sa ya nufa baki aya ma, don haka tace mai, "Kai ha uri na kasa gane inda maganarka ta nufa idan ba damuwa kai tsaye mu je kan abin da ya kawo ka guna domin ina sauri ne fita zan." Ya jima yana kallonta kafin ya nuna kansa da yatsa ya ce, "Ni ne Abubakar wanda mu kai karatu a makaranta guda wanda ya zuba maki yarda da aminci tare da soyayyarsa ya guje ki ya auri wata ya barki ba tare da duba tarin alherin da ki kai mai ba a tarenku ba." Da sauri ta kalle shi ta nanata sunan, "ABUBAKAR! Kansa ya aga mata alamar amsawa ko nuna cewar e shi ne fa. Kanta ta sadda sai kuma ta ago fuska cike da murmushi tace, "Don Allah kai ha uri Abbakar da kasa gane ka da nayi. Ban san yadda akai ba na kasa gane ka ba." Hawayen takaici suka zubo mai ya dube ta ya dubi jikinsa ya ce, "Dole ki kasa gane Ni Jiddah saboda yadda na koma ai." auki robar ruwa mai sanyi ta sha ta dube shi tace, "Abbakar ina aikinka da nasan kana yi? Ina matarka da yaranka domin nasan lokacin da akai ta posting in hoton yaronka a facebook da Media duk da lokacin ban fara chat ba. Ko da yake shi ne abin da yasa na ara tsanar waya a rayuwata ma baki aya a lokacin." Ya goge hawayen fuskarsa ya ce, "Jiddah don Allah ki yi ha uri na zo ne na baki ha uri kuma na nemi alfarma gunki don Allah ki tsaya min a shari'ar da za ai da Ni wadda ban aikata komai ba illa son zuciya da zafin kishi ne kawai suka sa matata tai min sharrin da yasa na rasa komai nawa komai ya are kuma na kasa samun nasara kuma an i yanke min hukuncin daya kamata an barni sai yawo ake da ni gari-gari da sunan shari'a." Jiddah ta gyara zaman tabaran fuskarta sosai tace, "Ban labarin asalin abin da ya faru da kai yadda zan samu damar taimaka maka to." Abubakar cike da tausayin kansa ya fara bata labarin abin da ya faru gare shi. SHEKARUN BAYA "Lokacin da na ga A'isha na kuma samu labarin Babanta mai ku i ne kuma an siyasa mai ci yanzu, sai naji cewar irinta ya kamata na aura wadda zan samu wani abu daga gare ta ba irin ki ba wadda ke ma kanta komai ba, ga yaranki wa anda ban san ma me kike nufi da su ba idan mu kai aure da su za ki zo min gida ko'ina za ki kai su? Duk lokacin dana tuno ki sai naji nayi tsaki kawai ina jin cewar sam bamu dace da ke ba tunda baki da ko sisi Ni kuma a lokacin da uwar ku ina sai nake ganin da A'isha kawai na dace tunda Babanta na da ku Ban sha wahalar samun soyayya gunta ba saboda yadda nayi fice gun iya kalaman soyayya da iya tsara mace. Hatta Babanta ban samu matsala da shi ba, sai ga mahaifiyarta wadda sai da nayi da gaske sannan ta amince da aurena da arta domin ta raina abin da nake samu a wata na aikina. Babban abin da na fara samu na ribar neman auren A'isha shi ne motar da Babanta ya ban kyauta, sannan kuma ya maida Ni na hannun damansa a kowane harka nashi. Cikin lokaci ka an ya taimaka min na gama gidana wanda ke ce kika tsara yadda kike son ginin ya kasance. Ba a auki lokaci ba aka saka ranar aurenmu da A'isha wata shida masu zuwa. Tabbas nayi farin ciki da saka ranarmu da akai, duk da wani lokacin kina ban tausayi yadda kike tsaye kaina komai kina yi min, duk abin da kika siya makaranta sai kin saimin, duk sarin kayan da ki kai akwai nawa ciki bayan ban ta a sakin jiki nayi maki wata kyauta ta bajinta ba, sai dai kece mai min kyauta kike min gata baki kuma jin komai haka baki ta a nuna jin haushin yadda ake ma abokanki kyautuka ba amma ke ko da wasa ban ta a ko saka maki katin wayar daya kai darajar ari biyar ba. Don kar ki gane komai yasa na gaya maki ban da waya amma sai kika ban taki wayar, haka zalika na dinga yi maki arya don kawai baki ganina saboda a lokacin ina cikin hidimar bikina ne da A'isha. Bayan anyi auren ne na zo gareki da zummar na cigaba da yaudararki har na gama karatuna na tsere daga rayuwarki ashe kin gane nayi aure ki kai min magana kuma kika nuna min acin ranki har ki ka ce min duk wanda ya cuci wani Allah Ya saka mai. Naso warai mu shirya kika i baki aya kika tsane Ni kika fita sabgar kowane namiji amma ban ji komai ba sai naga ma a lokacin ai ke kika sani kawai don haka na cigaba da kula da matata na bar ko tuna mai sunanki, idan an kira ma sai nayi dogon nazari nake gane inda na ta a sanin mai irin sunan. Lafiya lau muke rayuwa da matata, har ta samu ciki wanda nayi murna kamar me, duk da cewar ina azabtuwa da abubuwa da dama daga matar tawa, irinsu raini bata ganin girma na sam ban isa idan zata fita ba ta tambayeni ba, idan nayi mata magana sai tace tana da ku in mota don haka tsayawa tambayar me zatai min? Daga arshe ma ta koyi mota duk inda zata motata take auka kawai ta fice ban isa nace mata don me ba? A haka ta samu ciki na sha ba ar wahala domin daina komai tai na gidan tace ita cikinta ba zai wahala ba, don haka nike komai na gidan wanki, girki, da wanke-wanke duk nike mata su. Bayan suna da kwana biyu sai ga wata yarinya an kawo mata daga gidansu wai ita ce zata dinga mata reno da sauran aikin gida ita kam bata iyawa. Abin ya ata min rai sosai domin na lura duk bayan lokaci sai A'isha ta fito da sabon salon iskanci wanda ban isa nace ga nawa ra'ayina ba kan nata. Komai na gidan Aminatu ke yinsa kasancewar yarinyar na da natsuwa da hankali sosai take da tsabta yasa naji da i wani wajen na zuwanta gidan. Babu ruwan A'isha haka take barin yarinyar da yaron ta fice sabgarta don yanzu ita ma ta zama ar siyasa don haka bata zama gida ko da yaushe tana waje idan ta dawo gidanma tare da jama'arta take dawowa maza da mata. A takaice dai bata da lokacina ko na Yarona sai na hidimar siyasar da take yanzu nayi mata magana tai min rashin mutunci ta tafi gidansu na auka idan naje iyayenta zasu yi mata fa a bayan na gama karanta masu zaman da nake da ita sai naga sun goyi bayanta har suna i rarin jin zafi nake mata so nake na ga tana zaune kamar yadda nake zaune ina jiran wasu an canji daga gwamnati wanda ba abin da za su yi mata ga iyali ta fara tarawa. Haka dai naita basu ha uri amma duk da haka sai da ta shafe sati uku bata dawo ba sai dai nike zarya kullum ina ara bata ha uri da iyayenta. Sai da yar na samu ta dawo, amma fa da sabon salo ta dawo na raini da wula anci, gadara da nuna min isa ko shan waye haka zata ci min mutunci ba ruwanta da mijinta ne Ni. Yawo kuwa sai tai sati bata nan kuma yarinyar nan take barma yaronta haka bata gayamin zata yi tafiya sai dai idan ban ganta ba na kira wayarta sai ta gayamin ai bata gari ne lafiya nake nemanta? Abin na matu ar damuna ko da yaushe na dawo daga aiki Aminatu mai aiki nake iskewa ta ha a min abinci tai ma yaro wanka komai na gidan a hannunta yake. Sannu a hankali sai na fara jin cewa gwara na auri yarinyar tunda ta saba da kula min da gida haka ta iya rainon Yarona tamkar ita ce ta haife shi. Ban oye mata ba, amma sai Aminatu tace min a'a tana tsoron Hajiya A'isha nayi ha uri, Ni kuma sai na kasa ha uri domin a lokacin sai A'isha tai wata bata ma asar tana wata asar hidimar ta. Kin san namiji da naci kan abin da yake ganin zai ba shi mafita don haka na dage gun cusa ma Aminatu soyayyata har kuwa nai nasarar saka mata soyayyata a cikin zuciyarta ta amince zata aureni amma ba gidan zata zauna ba zan ware mata gida daban. Na amince domin gaskiya na gaji da ba ar wahalar da nake da sunan ina da aure kuma, kai tsaye naje gun iyayen Aminatu da farko basu amince ba sai daga baya sannan suka amince aka tsaida maganar aure wata hu u, matsalar da aka samu ita ce, sai na dawo da Aminatu gidana ta ci gaba da zama, ban san wa ya gayama A'isha maganar aurena da Aminatu ba sai gata a fujajan ta dawo ta kama yarinya da duka da yar na wace ta, na tabbatar mata da cewar aurena da Aminatu babu fashi sai dai duk abin da zata yi ta je tayi
Chapter 112 · 0% Book details