Sashe 16
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
sauran zata je ta dawo. Bata jima ba ta dawo da kayan abinci masu dama ba laifi ta kawo ku i Naira dubu uku taban tace ki ri e kafin suna ki dinga yin cefane da sauran abubuwa da ake bu ata." Kasa magana nayi saboda tsabar jin da in kayan abincin nan, domin na lura Deeni bai sauko ba, babu ruwansa da haihuwar da akai cigaba da halinsa zai ko a gaban mutane . Matan unguwa suka cika gidan, Allah Ya rufamin asiri kayan abincin da aka kawo min daga gun Mama aka ebo shinkafa aka gyara aka dafa, nan da nan aka auni gero aka ni o shi aka ora ruwan damun kunu. Dare nayi kowa ya watse aka barni da Yayar mahaifiyata ta zauna min kamar yadda ake yi a al'ada haihuwar farko ana kai tsohuwar da zatai zaman aki har na tsawon kwana bakwai, idan mai jego bata koma gida wankan jego ba kenan. Muna zaune muna ta fira Deeni ya shigo an ci sa'a ya yi sallama Yau, ya shige aki mun auka kayansa zai auka ya fice tunda yaga Inna kuma yasan nan zata kwana tunda har goman dare ta gota. Ai sai kawai mu ka jiyo tashin wa a na tashi daga cikin akin alamar ya kwanta ma shi. Bata ce komai ba, tace na samo mata zani ta kwana nan falon, ganin rashin kunyar Deeni tai yawa yasa nima na shimfi a zanin gado muka kwana nan duk da ta dage sai na je aki na kwana na i. Haka mu kai ta kwana falo Deeni na kwana aki yana kunna wa a kullum har barci ya auke shi sai ya farka ya kashe. Da safe kuma idan ba ita ce ta fara gaida shi ba sam bai gaidata. Nasha zuwa gidajen barka cikin unguwarmu naga an kawo ma mai jego naman an baki, har mu an zaman barka mu ci, amma ni ko kan kifi Deeni bai siyo ya kawo min ba, ko da yake abincin ma bai badawa sai dai da rana ya aiko yaro ya amsar mai abinci da kunu kullum haka yake. Inna tai ta fa a ni dai ban cewa komai, sai idan abin ya dameni na shige kewaye naci kukana na fito. Har ga Allah so nake na ci abu mai da i amma ban da yadda zan yi, ku in da aka kawo min ma sun are Yau daren suna tun da safe da yar suka isa mu kai kalaci. Ranar daren suna mutane su ka cika gidan suna jiran a fito masu da kayan miya da garin tuwo su rage aiki kamar dai yadda ake yi kowane gidan daren suna amma babu alamar Deeni zai kawo ko ruwan sha a gidan balle kayan abincin suna. Har zuwa lokacin babu mutun guda da ya zo daga dangin mahaifina kuma a gari guda muke da su amma ba wanda ya zo min barka. Ko da yake shi kanshi Babana ance min yana garin amma bai zo ba, don haka ban ga laifin danginsa ba da basu zo ba. Tunda na shiga wankan yamma na shige cikin robar wankan na fashe da kuka ina addu'ar Allah Ya fitar da ni daga wannan kunyar da Deeni ke neman saka Ni. Gida cike da mutane amma babu abin da za su yi aikin abincin gobe na suna. Wannan wane irin bala'i ne haka? Sai da Inna tayi da gaske ta fito dani daga kewayen Yau dai ita kanta ina lura da yadda take kallona tana share hawayenta a oye. Muna zaune mun yi zugudum naji sallamar Safiya, tun da na haihu bata zo ba, ko da yake ba mamaki sai Yau ta dawo daga unguwar da ta je. Muka gaisa ta auki jariri tana ta yaba kyan shi, anan ne ma naji sunan yaron daga bakinta Deeni ya gaya mata sunansa Al'ameen, nace Allah Ya raya min shi a raina. Bayan ta fice Binta ta shigo da Naira dubu taban tace, "In ji mijinta yace na auki ari biyar naba Deeni ari biyar." aramin da in ku in nan naji ba wallahi kamar an saka ni aljannah haka naji. Muna a haka ya shigo na je na same shi yana ta cika yana batsewa na gaya mai an bamu ku i amma don Allah ya amsa ya siyo min kayan miya da su domin Inna tace daga can gida za a kawo min garin da za ai tuwo da fate gobe. Wani banzan kallo ya bini da shi yace, "Dilla ban ku ina, kuma ki sani sai kin ban ku in mashin sannan zan je siyo maki kayan miyar idan ba haka ba sai dai ki nemi wani ba dai Ni ba. Kuma da da ki yi abin arzi i ma da kin bar min ari biyar inki domin nasan ke gobe cikin ku i kike." Baki bu e nake kallon shi na rasa abin cewa. Ikon Allah! Ku dai biyo Haupha don jin shin zata ba shi ku in ya ha a duka ne koko zata hana shi? Daga taku a kullum Haupha [7/22, 3:34 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa