← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 133

Sashe 35

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

sannan ya sai min waya yace mu dinga magana karatu zan koma ba zan zauna haka ba. Cikin ikon Allah na samu jarabawata tai kyau yadda ya kamata don haka na je na rubuta jamb cikin kwanciyar hankali da fatan dacewa, komai nake Uncle Salim na taimaka min daga Kano yake turomin ku i domin yasa na bu e account na banki, don haka sai na sake samun sau in rayuwa karo na barkatai. Harma na dinga tunanin gani can a makaranta ina karatu yarana kuma suna gun Mamana cikin aminci da kulawa, Bayan wani lokaci na gama komai duk Deeni na kallona bai ce komai ba sai ana saura sati guda na fara zuwa makaranta yace sai na biya mai ku in makarantar shi ma idan dai ina so nayi karatun nima. Na gayama Uncle Salim sai yace ba komai don haka ya turomin ku in na ba shi, shi dai fatanshi na kama karatu kawai na barshi ya yi duk abin da zai. Cikin ikon Allah na fara zuwa makaranta babu abin da Uncle Salim bai saimin ba, ranar da na fara zuwa makarantar ji nayi tamkar na fara sabuwar rayuwa, ji nayi na manta duk wata damuwata ji nayi kamar wata sabuwa a wata sabuwar duniyar. Cikin kwana biyu nayi awata guda aya mai Rahma Kazaure, zaune mu ke cikin farin ciki ban manta yarana ba ina masu addu'a duk lokacin da nayi sallah haka ina neman Allah Ya shirya mahaifina Ya ha a kanmu waje guda Yasa mana fahimtar juna haka ina yawan saka mahaifiyata sai dai har ga Allah mantawa nake da wani Deeni a rayuwata sam don haka ban wani saka shi a cikin lissafina sam. Ina duk lokacin dana dawo daga makaranta sai na iske Deeni da wata, amma ko a jikina saboda na riga na cire shi a raina baki aya kawai karatuna nake ina jiran na gama nasan Uncle Salim zai samar min aiki na kula da kaina da yarana tare da mahaifiyata. Ranar da akai mana hutun semester na dawo gida ina jin duk ban jin da i, don haka na kasa ko zuwa gidanmu don in taho da yarana sai nayi kwance kawai ina jin duniyar tai min zafi baki aya. Barci ya kwashe Ni sai nayi mafarkin gani zaune da Uncle Salim yana kallona ya ce, "Jiddah ki yi ha uri da rayuwa kowace iri ce, don Allah ki zama jaruma ki jajirce kan lamurranki da yaranki ki natsu ki kama kanki ki kama mutuncin kanki insha Allah watarana za ki yi dariya." Ya nuna min wani mutum daya juya baya ya ce, "Jiddah zan tafi Ni, tafiya mai nisan gaske amma kin ga wancan? Shi ne zai maye maki gurbina duk rintsi kar ki rabu da shi tabbas na yarda da shi nasan zai kula da ke Jiddah." Ya tashi ya juya ya tafi ina ta kiran sunansa bai ko waigo ba... arar wayata ce ta tada Ni daga barcin da nake ina mafarkin Uncle Salim. Mamarmu ce ke kirana, "Ki maza ki shirya ki taho Kano za mu je an yi rasuwa." Iyakar abin da Mama tace kenan ta kashe wayarta. Gabana ya fa i daram! Kar dai ace Hajjo ce ta rasu! Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Tabbas idan Hajjo ta rasu na shiga uku ni Jiddah shike nan komai zai iya tsayawa sai Uncle Salim kawai ya rage min duk da cewar yafi Hajjo taimako na amma Hajjo macece dole wata damuwar sai mace. Haka na shirya na nufi gida na iske Mama cikin shirinta tana ta jan carbi, kawai tasha muka nufa sai Kano, tun a ofar gidan naga tarin mutane sai na ida amincewa Hajjo ta rigamu gidan gaskiya. Sai dai ina shiga Hajjo na fara cin karo da ita zaune tana sanye da hijabi tana jan casbaha. To waye ya rasu ne?" Ita ce tambayar da nake ma kaina. Sa o ya shigo wayata ina dubawa naga daga Deeni ne ga abin da ya ce. "Ni amaraddini na saki matata Jiddah saki biyu." Idan kin gama idda ki aure kuma kayan akinki na saida sai ki ri e yaran duk na bar maki. To masu karatu waye ya rasu? Deeni ya saki Jiddah saki biyu ina zata je? Mu ha u a kashi na gaba. Taku a kullum Haupha [8/5, 10:12 AM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa
Chapter 35 · 0% Book details