← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 133

Sashe 98

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ace kin yale Ni ba matata, saboda ke ce farin cikina haka ke ce natsuwata don Allah ki daina azabtar da Ni da wannan mummunan hukuncin naki wanda zai iya nakasar da zuciyata." Kuka yake sosai yana ara shigar da ita cikin jikinsa. Lub tai a jikinsa tana jin yadda yake zuba mata kalaman soyayya masu da i da sanyaya zuciya wanda rabon da ya furta mata kalma guda ta soyayya har ta manta. Sai da ta tabbatar da cewar ya yi laushi sosai sannan ita ma ta rungume shi jikinta tana cewa cikin sanyin murya, "Haba mijina abin tun ahon rayuwata, mai dasa min natsuwa da kauda min tashin hankali, me yasa ka za i raba tsakanina da wadda ban da kamar a fa in duniyar nan? Me yasa ka manta yadda na mutu kan aunarka nake biye da sonka lungu da sa o ne don kawai na tabbatar da cewa nayi kane-kane na hana idanunka da zuciyarka hangen wata iya mace bayan Ni? Don Allah ka daina razana zuciyata ta hanyar nuna kulawar soyayya ga wata mace bayan Ni mijina." Yana kwance jikinta tana wasa da sumar kansa ya ce, "Nayi maki al awarin ba zan sake tada maki hankali ba haka ba zan sake kallon Jiddah da kallon soyayya ba har abada insha Allah zan auke ta tamkar wadda kuka fito Uwa aya Uba aya insha Allah." Sai ga su sun baje suna ta fira kamar ba su ba, har ta tashi ta shige akin da take ta ha a mai ruwan wanka ta ja shi suka shige don ya yi wanka ya samu natsuwa. Jiddah kuwa tana gama waya da Prince sai tai murmushi domin ta lura duk lokacin da waninsu ke cikin damuwa sai gudan ya ji a jikinsa shima ya kasance a damuwar. Ba zata manta ba wata rana da wani ya biyo ta ya dame ta har dai ta gaji ta tsaya kasancewar tana tafiya ne a asa. Sun gaisa sama-sama ya gabatar mata da kansa da sunansa Jameel da sana'arsa ta saida zinari da azurfa a nan Kadunar yana da mata guda da yara biyu mace da namiji. Ba yadda bai ba ta shiga motarsa ya kaita gida ta i don haka ya amshi lambarta da al awarin zai kira ta tai mai kwatancen gidansu don da gaske yake ya ga mata shi a karo na biyu rayuwarsa bayan matarsa ta gida. Suna rabuwa da Jameel wayar Prince ta shigo wayarta tana agawa ya ce mata, "Princess gabana ke ta fa uwa sosai ina jin kamar wani abu ne zai faru da ke ko Ni marar da i don haka na kira ki naji ko kina lafiya?" Kamar ta bayyana mai abin da ke faruwa sai kuma ta share tace ba komai ya dinga Salati kawai daman haka ne wani lokacin ana jin irin hakan. Haka ma akwai lokacin da ta sake ha uwa da wani Abdul shi ma suna rabuwa ya kira ta hankali tashe yana gaya mata yadda yake jin damuwa da fa uwar gaba na addabarsa. Hawwa'u (Iyami) ta shigo akin tace " iyata ana kiranki bakin gate in ji maigadi yanzu." Sai da tai jim, domin dai tasan ba wanda su kai zai ganta a Yau koma tace yanzu amma sai ta share tunanin tace, "To ace mai ina zuwa ya shigo da shi cikin harabar gidan a ba shi ruwa kafin na fita." Hawwa'u (Iyami) ta fice tana murmushin yadda kowace rana sai Jiddah ta samu aukaka daga ko'ina kamar ba ita ce ta sha ba ar wahala ba a rayuwarta ba, ko da yake Malam ya gaya mata daman haka rayuwar take idan ka sha wahala da fari ka zo daga baya ka sha da i, to ita dai yanzu da in ne take sha har ya so yafi na Alawiyya ma, tunda ita a sake take ga maza nan birjik kowane so yake ya samu shiga gunta don haka sai banko alheri suke mata ta ko'ina tamkar babu talauci a duniyar ma baki aya idan akai mata wata kyautar, don ma ta kasance ar halak tana matu ar kula da danginta da mahaifiyarta bakin gwargwado. Yana zaune sai waige-waige yake tamkar ace arr ya ruga. Kallo guda za kai mai ka tabbatar da cewa duniya tai mai juyin taliyar Hausa da taji wuta. Ya jeme ya rame ya fice hayyacinsa kayansa duk sun yage da ganinsa yasan inda talauci ke kwana yake tashi ko ace ma shi ne talaucin don basu da mara ba. Sauke kansa asa ya yi lokacin da aka sauke mai ruwa mai sanyi da lemu tare da kayan tsotse-tsotse aka ce tace ya fara sha kafin ta fito yanzu. Ke duniya ina za ki damu ne? Yanzu nan Jiddah ke rayuwa a wannan gidan mai kama da aljannar duniya? Yanzu nan Jiddah ce a jikin jaridu da gidajen rediyo ake magana kanta?" Shi ne tunanin da ba on ke yi yana kallon kayan gabansa hawaye na zubowa daga idonsa. Cike da natsuwa ta nufi inda tasa a sauke ba on nata, ko a ranta bata kawo komai ba har ta isa inda yake ta ja kujera tai sallama ta zauna. A firgice ya ago kansa ya kalleta sai kuma ya mi e tsaye sai kuma ya tsugunna ya kama afarta yana cewa, "Don Allah ki taimaka min kar da ki tuna baya ki taimaka ki yi min abin da Ni na kasa yi maki watau halacci ki ceci rayuwata daga angin data afka don darajar Allah Jiddah." Bata gane shi ba, ga dai shi kamar ta so tasan fuskar amma ta kasa tuna inda tasan fuskar don haka ta janje afarta tace, "Bawan Allah tashi ka zauna ka gaya min waye kai. Wane halacci ne zan maka?" Sadda kansa asa ya yi ya ce, "Tabbas nasan daman ba za ki iya gane Ni ba a yanayin da kika ganni yanzu ba Jiddah, amma hakan duk ya faru ne saboda sakayyarki da ke bibiyar rayuwata ta hanyar mallakar wata hatsabibiyar da ke ce ya kamata ki zauna inda take." Sai kanta ya aure ta rasa inda zancen sa ya nufa baki aya ma, don haka tace mai, "Kai ha uri na kasa gane inda maganarka ta nufa idan ba damuwa kai tsaye mu je kan abin da ya kawo ka guna domin ina sauri ne fita zan." Ya jima yana kallonta kafin ya nuna kansa da yatsa ya ce, "Ni ne Abubakar wanda mu kai karatu a makaranta guda wanda ya zuba maki yarda da aminci tare da soyayyarsa ya guje ki ya auri wata ya barki ba tare da duba tarin alherin da ki kai mai ba a tarenku ba." Da sauri ta kalle shi ta nanata sunan, "ABUBAKAR! Kansa ya aga mata alamar amsawa ko nuna cewar e shi ne fa. Kanta ta sadda sai kuma ta ago fuska cike da murmushi tace, "Don Allah kai ha uri Abbakar da kasa gane ka da nayi. Ban san yadda akai ba na kasa gane ka ba." Hawayen takaici suka zubo mai ya dube ta ya dubi jikinsa ya ce, "Dole ki kasa gane Ni Jiddah saboda yadda na koma ai." auki robar ruwa mai sanyi ta sha ta dube shi tace, "Abbakar ina aikinka da nasan kana yi? Ina matarka da yaranka domin nasan lokacin da akai ta posting in hoton yaronka a facebook da Media duk da lokacin ban fara chat ba. Ko da yake shi ne abin da yasa na ara tsanar waya a rayuwata ma baki aya a lokacin." Ya goge hawayen fuskarsa ya ce, "Jiddah don Allah ki yi ha uri na zo ne na baki ha uri kuma na nemi alfarma gunki don Allah ki tsaya min a shari'ar da za ai da Ni wadda ban aikata komai ba illa son zuciya da zafin kishi ne kawai suka sa matata tai min sharrin da yasa na rasa komai nawa komai ya are kuma na kasa samun nasara kuma an i yanke min hukuncin daya kamata an barni sai yawo ake da ni gari-gari da sunan shari'a." Jiddah ta gyara zaman tabaran fuskarta sosai tace, "Ban labarin asalin abin da ya faru da kai yadda zan samu damar taimaka maka to." Abubakar cike da tausayin kansa ya fara bata labarin abin da ya faru gare shi. SHEKARUN BAYA "Lokacin da na ga A'isha na kuma samu labarin Babanta mai ku i ne kuma an siyasa mai ci yanzu, sai naji cewar irinta ya kamata na aura wadda zan samu wani abu daga gare ta ba irin ki ba wadda ke ma kanta komai ba, ga yaranki wa anda ban san ma me kike nufi da su ba idan mu kai aure da su za ki zo min gida ko'ina za ki kai su? Duk lokacin dana tuno ki sai naji nayi tsaki kawai ina jin cewar sam bamu dace da ke ba tunda baki da ko sisi Ni kuma a lokacin da uwar ku ina sai nake ganin da A'isha kawai na dace tunda Babanta na da ku Ban sha wahalar samun soyayya gunta ba saboda yadda nayi fice gun iya kalaman soyayya da iya tsara mace. Hatta Babanta ban samu matsala da shi ba, sai ga mahaifiyarta wadda sai da nayi da gaske sannan ta amince da aurena da arta domin ta raina abin da nake samu a wata na aikina. Babban abin da na fara samu na ribar neman auren A'isha shi ne motar da Babanta ya ban kyauta, sannan kuma ya maida Ni na hannun damansa a kowane harka nashi. Cikin lokaci ka an ya taimaka min na gama gidana wanda ke ce kika tsara yadda kike son ginin ya kasance. Ba a auki lokaci ba aka saka ranar aurenmu da A'isha wata shida masu zuwa. Tabbas nayi farin ciki da saka ranarmu da akai, duk da wani lokacin kina ban tausayi yadda kike tsaye kaina komai kina yi min, duk abin da kika siya makaranta sai kin saimin, duk sarin kayan da ki kai akwai nawa ciki bayan ban ta a sakin jiki nayi maki wata kyauta ta bajinta ba, sai dai kece mai min kyauta kike min gata baki kuma jin komai haka baki ta a nuna jin haushin yadda ake ma
Chapter 98 · 0% Book details