← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 133

Sashe 78

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zama Lauya, ina son na ganni da kayan Lauya. A cikin taskun musgunawar Inna Saude da sauran masu tsoron ta na gama primary na shiga Secondary har a lokacin ina fuskantar barazana sosai gun Inna Saude da sauran mutanen gidan har ma dana waje wasu da dama da sunan shegiya suke kirana. Tun abin na damuna har ya daina damuna na ha ura amma na saka a raina duk sanda na gama karatu zan bazama duniya neman Jiddah da iyayena sannan zan zama babbar Lauya na dinga kare marassa arfi na dinga bi ma yara ha insu gun iyayensu. Lokacin da na gama Secondary lokacin Allah ya yi wa mijin Inna Saude rasuwa, a lokacin kuma Faisal yana asar waje karatun Likitanci, don haka sai komai ya tsaya min, na gama karatu ina son cigaba ban da wanda zai saka Ni makaranta haka zalika abubuwa da yawa sai ara faruwa suke a gidan. Hatta kai ta kawo ba a bani abinci a gidan duk da cewar nice ke girkawa amma ba a ban, ina ji ina gani Inna Saude zata kira almajiri ta ba shi abinci ga Ni ina jin yunwa amma bata ban. Sai dai na je gareji gun Yaya Mansur ya sai min abincin, to shi ma da yake ya yi aure an kai ma matar zugata wasu ma suna ce mata aurena zai sai ta tsane Ni don haka bata bari ko da wasa Yaya Mansur na zuwa gida balle ya ban wani abu idan na je kuma gidansa jikin garejin yake tana yawan le owa tana gani na zata fito ta dinga masifa tana zagina sai na bar wajen. Ban san ya akai ba, sai aka wayi gari shi ma Yaya Mansur bai san gani na dana je yake kora ta ya ce ba zan kashe mai aure ba na kama tsagina. arshe dai ya zazzage Ni ya tara min mutane ya ce kada na sake nuna na san shi ma. Hakan yasa naga dacewar ha a kayana na kama gabana ba mamaki na gano mahaifiyata ko mahaifina. Cikin dare kuwa na ha a na kayana nabi dare na gudu na bar gidan ina kuka ban san ina zan je ba. Tashin farko naji baki aya Kano ta fice daga raina, sai na ke jin kuma duk yadda akai ita ma Jiddah tabar Kanon don haka zaman Kano ya are gareta ita ma. Ina zuwa tasha na rasa motar da zan hau sai naji ana ambatar Sokoto, don haka sai na ji na amince da zuwana Sokoto kai tsaye na shige motar ina jin na yi bankwana da Kano har abada a raina. Lokacin da muka isa Sokoto na rasa inda zan sauka sai na tambayi gidan mai unguwa, aka nuna min gidan kai tsaye na tafi, na ji tsoron kada in sake fa awa gidan mutane irinsu Inna Saude amma kuma sai zuciyata ta dake na isa gidan cike da warin gwiwata. Tsoho ne sosai mutumin bayan mun gaisa na ba shi labarina duka ban oye mai ba, ya tausaya min sosai ya ce , "Tabbas kin sha wahalar rayuwa yarinya, insha Allah za ki aukaka kuma za ki ha u da iyayenki da yardar Allah. Amma ina so ki sani Ni ban da mata balle na she ki wajena amma zan kai ki gidan babban Hakimi insha Allah can za ki zauna lafiya ba tare da wata matsala ba, saboda gidan an'uwana ne. Haka akai kuwa, ya shirya muka nufi gidan babban Hakimi bayan mun gaisa ya gaya mai komai kamar yadda na gaya mai, Hakimi daman tunda na zauna yake kallona yana murmushi yana lashe baki ya ce, "Ai ba komai nan ne ma ya kamata ta cigaba da zama ai, kuma zai saka ta makarantar boko ta cigaba daga inda ta tsaya Sosai naji da in maganarsa. Aka kira wani aka ce ya shigar da Ni gidan ya kaini gun Hassu ya ce taban waje akinta zan zauna. Matar mai kirkin gaske, ganin farko da ita na ji ta zauna daram a raina kuma naji ina matu aunarta a raina kamar naga mahaifiyata haka naji. Ita ma haka ta saki fuska cike da fara'a ta tarbeni ta kawo min fura ta kawo min abinci, tana ta cewa na ci. Saida na ci na oshi sannan na bata labarina kaf. Kuka take sosai tana arawa, arshe ta bini da addu'ar Allah Ya bayyana iyayena a duk inda suke. Zamana gidan Hakimi ya yi min da i sosai, domin ba tsangwama ba kyara komi nake so shi Baba Hassu ke yi min. Duk da akwai sauran mata har uku a gidan na lura ba ruwan Baba Hassu da su, sune ma suke yawan haye mata amma bata tanka masu, suna yawan tsokanarta amma bata nuna masu ta gane ma. Gani na ma sun so su ji inda ta samo Ni amma ba damar hakan dole suka koma yi mata habaicin haihuwa. Sai dai kuma sam ban bari sun ga wajen kwana na ba balle su raina Ni, duk sadda su ka nemi taka Ni rufe ido nake na yi masu rashin mutunci domin nayi al awarin ba zan sake bari wani ya cutar da Ni ko ya wula anta ni ba. Da farko sun kai arata gun Hakimi amma sai ya rufe ido ya ci masu mutunci ya ce masu a kaina zai iya ata masu rai don haka su kiyaye ni. Dole suka shafa min lafiya suka koma kan Baba Hassu da rashin mutuncinsu don haka sai na sake nuna masu nan ma ban yadda ba, domin Baba Hassu tamkar uwata ce duk wadda ta ci mata mutunci sai na yaga mata rigar daraja a gidan. Sai dai inda Gizo ke sakar guda ne, Hakimi ya matsa min duk dare sai ya shigar min aki idan ina barci, yai ta kallona yana lashe baki, bai ta a tada Ni ba ko ta a Ni ba amma tabbas ina ganinsa tsaye kaina yana kallona. Hakan yasa na shida tashin hankali sosai domin zuciyata ta fara rawa kan Hakimi, me yasa yake zuwa akina cikin dare? Kallon me yake min yana lashe baki? Sune tambayar da nake yawan yi wa kaina ban san amsar su ba. Hikimi kuwa tun da yaga Alawiyya yake jin matu ar sha'awarta azuciyarsa domin yasan dai ba aurenta zai ba, saboda matansa hu u cif don haka ba maganar ara aure, koma ba hakan ba yasan yarinyar ba zata ta a amincewa ba ya aure ta ba, da yasan zata amince da babu abin da zai hana ya saki matarsa guda ba ya maye gurbin ta da Alawiyyar ba. Duk lokacin da ya shiga akinta cikin dare sai ya samu kan shi da kasa iya aiwatar mata da komai sai kallo yana jin nisha i sosai a zuciyarsa. Duk lokacin da ya shiga akin yana shiga ne da zummar ya aiwatar da udurinsa kan yarinyar amma sai ya kasa koda ora yatsansa a kanta. Ya rasa yanda akai hakan ke faruwa sam. Ga wani irin kyau da yarinyar ke ara yi mai amma ya rasa me yasa yake kasa cimma burinsa kan ta. Ni kuma a angare na sai na samu kaina da jin me zai hana na gaya ma Baba Hassu abin da ke faruwa na zuwan Hakimi akina cikin dare? Don haka na same ta akinta na gaya mata abin da ke faruwa. Sosai ta razana na lura maganar ta girgiza ta sosai amma sai ta dake don ina wajen ta ce min, "Ki yi ha uri Alawiyya zan dakatar da faruwar lamarin insha Allah." Daren ranar kamar yadda ya saba, ya shigo min aki sai dai Yau ga dukkan alama da arfinsa ya shigo don yana shigowa ya maida akin ya rufe har da sakata. Ya tasanma gadona hai an da wata kwalba a hannunsa yana niyyar watsa min abin da ke cikin kwalbar. Baba Hassu dake oye cikin toilet akin Alawiyya ta fito ta ka e kwalbar ta dube shi cike da acin rai tace. "Na gode wa Allah da bai azurtani da samun zuri'a da kai ba, ashe daman baka da imani har irin haka? Tabbas a Yau zama na da kai ya are tunda ba mutumin kirki bane ba kai, daman ina zaune ne a cikin gidan nan saboda kai tunda kai ma baka da halin kirki to mun raba hanya. Ya dube ta cike da ru ani kan fuskarsa, sai kuma ya ce, "Kin yi wauta mai girman gaske Hassu da kika jefa kan ki a cikin abin da babu ruwanki, ya kike da ita ne? Kar ki manta ni ne na kawo maki ita da baki san ta ba sai da na kawo maki ita. Don haka duk abin da naga dama zan yi da ita ke baki isa ki hanani ba. Ya sake auko kwalbar zai watsa min duk da ina zaune ina kallonsu ina jin duk abin da suke cewa kuma. Baba Hassu ta sake buge kwalbar ai sai kawai Hakimi ya sha e ta ya buga mata kai da bango, nan take jini ya fito ya sake ta asa tana kakarin mutuwa, sauri ya fice daga akin, cikin kuka na rumgume Baba Hassu amma sai ta ce min da yar, "Ki yi hanzarin guduwa domin dawowa zai kuma idan ya dawo sai ya cimma burinsa Ni kam nasan mutuwa zan, amma idan kika cika burinki na zama Lauya ki bi min ha ina domin ban da kowa duk duniyar nan, dangina sun mutu a wani hatsarin da akai. Na takaice maki labari dai irin labarin da tsohuwa ta bamu Ni da ke ta gaya min ya faru da su, ashe iyar Yayan Mamata ce ita. Nan Ni ma na bata labarin mahaifiyata Fatima tai murmushi duk da halin da take ciki tace "Allah na gode maka, da zan mutu bayan naji labarin ahalina, tabbas to za ki ga mahaifina da sauran danginmu don Allah ki ce su yafe min... Cak ta tsaya da maganarta na ta a ta naji shiru na kira sunanta naji shiru alamar rai ya yi halinsa. Da hanzari na tashi na auki ka an daga kayana na ibi ku i na tsallake gawar ar'uwata kwance na bar gidan. Ina kallon lokacin da Hakimi ya koma
Chapter 78 · 0% Book details