← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 133

Sashe 34

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 22 Tafiya nake ba kowa kasancewar safiya ce sosai, sai da nayi nisa sosai sai kuma nayi tsaye hawaye suka zubomin wata zuciyata tace min, "Yanzu Jiddah kin amince kema yaranki su taso suna maki kallon da kika taso kina yi ma mahaifanki? Yanzu Jiddah ba za ki zauna ki raini yaranki ba, ko dan ki hana su kukan rashin Uwa? Haba Jiddah za ki yi babban rashin hankali idan kika tsallake yaranki kika bi duniya, ribar me za ki tsinta a yawon duniya? Jiddah wa ke gareki wanda zai tausaya maki idan kika bi duniya? Wannan shi ne sakayyar da za ki yi ma Mahaifiyarki? Ashe baki tausanta? Ashe za ki iya ora mata wahala ki bar mata yara ki bi uwa duniya? Lallai Jiddah akwai sauran rashin tausayi a cikin zuciyarki." Sai kawai na fashe da kuka na kamo hanya na dawo gida, tun daga ofar gida nake jin kukan Afnah da Afnan tamkar ana dukansu, da sauri na ida shigewa na auki Afnah ina lallashi ina shafa kan Afnan, shi kau Haidar yana zaune da kofin ruwa ba shakka su ya ba don naga duk rigarsu ta jike da ruwan. Rungume su nayi duka na fashe da kukan tausayin kaina dana yarana. "Ya Allah ga baiwarka tare da yaranta a halin da kafi kowa sani Ya Allah ka agaza mana ka bamu mafita kan wannan yanayin rayuwa da mu ke ciki mai wahala." Ita ce kawai addu'ar da nake ina kuka tamkar raina zai fita, sanin ina fama da ciwon hawan jini dana gushewar hankali yasa na samu da yar na natsu na daina kuka na koma ajiyar zuciya kawai. Har arfe biyun rana ba abin da muka ci Ni da yarana saboda ban da komai haka ban da abin da zan ba su, sai na saka hijabina nabar su nan na je wani shagon Mustapha mai shago muka gaisa nayi shiru domin dai ban iya neman taimako kuma ina jin kunyar amsar bashi duk da nima ina bin bashin amma an hana ni dole na ha ura na barsu sai mun je can sai su biyani. Ganin nayi an jim yasa mai shagon cewa, "Jiddah lafiya lau kuwa?" Nayi Jim saboda ban san ya zan ce ba, amma sai na samu bakina da furta "Don Allah ka ban taliya da magi idan mu kai aikin polio zan kawo maka insha Allah." Ya dube ni sai kuma ya auko abin da nace ya ban. Na yi godiya na tafi ina jin da i sosai. Ko da na je gidan na iske Haidar nata yi masu wasa suna dariya kamar ba yunwa suke ji ba, tausayin su ya kamani nan da nan na ha a wuta na ora sanwar, sai ga Haidar ya zo yana ta hura wutar gwanin ban tausayi. Su kuma su Afnah sai sukai barci nan da nan na gama dafawa na tada su na zubawa Haidar amma sai yaron nan ya ebo taliyar ya nufi bakina, alamar yana nufin na fara ci kafin ya ci shi. Na girgiza kaina ina jin da in yadda tun yanzu Allah Ya sakawa yarana tausayina komai su ke ci sai sun ban a baki, Haidar ko kukan yunwa bai yi yaron sai dai ya lafe ya yi shiru kawai, idan su Afnah ke kukan sai ya kama yi masu wasa da dariya har sai ya auke masu hankali sun daina kukan. Idan kuwa ban lafiya sai ya zauna kusa da Ni ya dinga ta a jikina yana mun sannu ya ebo ruwa ya ban duk abin da ya samu ya kawo min, idan kuwa yaga na lullu e sai ya kama kuka ya dinga shiga makwabta yana cewa a zo Umminsu bata lafiya. Polion da nake yake matu ar taimaka min, duk wata ina amsar kayan abinci gun Mustapha mai shago da an bamu ku in polio sai na kai ma shi na amshi wasu kayan. Abban Haidar bai dawo ba sai da ya yi wata guda har da kwana shida rannan kwatsam ina shara sai ga shi ya fa o gidan ba ko sallama kamar wanda ya fito daga kewaye (toilet) na dube shi nayi ma shi sannu da zuwa na cigaba da sharar da nake ina jin yaran na kiran ga Abba ga Abba nasan ba lallai bane ba ya dube su balle ya tanka masu na aje tsintsiyar na bi shi akin da ruwan sha. Yana zaune kan gado yana duba rediyon shi na shiga da sallama ta. Ya ago kai ya dube ni ya ci gaba da abin da yake yi. Sai naji na kasa yi mai maganar ku ina daya kwashe ranar da zai tafi, sai dai na yi zaune kawai bakina ya rufe sai a cikin zuciyata nake siffanta maganganun da zan yi mai. Ya dube ni a she e ya ce, "lafiya dai ko? Naga kin wani tasa ni gaba da wani ruwa kamar kin ban abinci na ci." Madadin na yi magana sai kawai na mi e na fice don ban da ta cewa a fili sai a zuciya, to kuma bai fa uwa na zuciyar. Cikin yarana na koma na zauna nayi tagumi hawaye suka zubo min. Ji nai ana share min hawayen, ashe Haidar ne, shima kukan yake yana cewa, "Ummi Abba ne ko?" Girgiza kaina nayi nace, "Kaina ke ciwo Haidar." Tashi ya yi ya ebo ruwa ya auko min maganin da nake ba Afnan da bata lafiya ya ban wai na sha na warke. Muna haka Abban Haidar ya fito ya le a diram in da ake zuba ruwa yaga babu ya ja tsaki y a yaye labulan akin ya ce min, "Ke wai ba ruwa ne gidan?" Cikin sanyin jiki nace "Yanzu zan je na ebo dama shara zan gama na je na ebo kamar ko da yaushe." Ya saki labulan ya fice ina jin arar rufe gidan. Na sauke ajiyar zuciya na tashi na auki bokiti na nufi mono ibar ruwa, Haidar ya auko buta ya biyo ni da ita shima zai taya Ni aukar ruwan. Tun daga lokacin nice ke ebo ruwan gidan, Abban Haidar na kwance zan je na ebo ruwa a mono mutanen unguwa nata gulmata wasu ma da kansu suke tareni a hanya suna tambaya ta ina maigidana da nake zuwa ibar ruwa? Ni dai dariya kawai nake na wuce don ban da amsar ba su. BAYANA SHEKARA BAKWAI Ana cewa ba a sabo da wahala to Ni dai na saba da wahala sai dai ba yadda za ai ka ganni ka gane cewa ina cikin matsala, domin ko da yaushe cikin fara'a nake da murmushi, ban ta a wanke afa na je gun iyaye da maganar abin da Deeni ke mun ba, amma ina matu ar jin tsana da iyayyarsa a zuciyata duk tsawon lokacin nan ban da tsanar shi babu abin da ke yawo a jikina. Kasancewar yanzu ban da polio ina yin duk wani aiki daya shafi angaren sai na samu sau i sosai har na shiga makarantar koyar da sana'a ta shekara biyu, duk sanda zan tafi sai na kai kayan yarana gun Mama idan sun dawo daga makaranta su saka idan na dawo na biya na taho da su gida. Itama Mama har zuwa yanzu ba sau i saima cigaba da zaman uncin da take a gidan mijinta, abin da duk idan na tuna nake kuka ina arawa ina jin a raina wai yaushe ne zan zama kamar kowa ne? Yaushe ne zan farin ciki Ni da yarana kamar kowa? Kowa ne yara zaka gansu da kazar-kazar amma ban da nawa, sun fahimci wace irin rayuwa mu ke da mahaifinsu sun gane cewar su kansu ba tasu yake ba, domin hatta makaranta nice na samu mai sau i ta gwamnati na saka su, haka ma islamiyya duk Ni na kai su. anci guda na samu shi ne wanda na datse duk wata ala a ta aure tsakanina da Deeni, saboda na lura bai damu da ciwon da ya yi yawa a duniya ba, don haka na same shi na gaya mai na gaji da aurensa don haka ba zan sake amincewa da shi ba. Bai damu ba yace min idan kau haka ne hatta yaranki sai dai kisan yadda za ki yi da su domin ba zan iya ri e su ba Ni. Har ga Allah naji da in hakan domin daman Ni ke ri e da su ba shi ba, don haka na amince da shara in babu ruwana da shi haka ba ruwana da hidimarsa kowa ya yi abin da zai fissheshi nace na yarda. Sai dai ba a jima ba ina zaune aka zo a'a ce na gyara za a duba gidan nace kamar ya aka ce ai Deeni ya saida rabin gidan ne shekara biyu da suka wuce. Naji mugun tashin hankali domin kuwa nasan idan har Deeni zai iya saida rabin gida ban sani ba to tabbas wata rana gidan zai saida ban da labari. Hakan yasa na nufi gidansu domin na gayama iyayensa sai dai Mamarsa nuna min tai shi ya sai gidansa don haka duk yadda ya yi da shi ba ruwan wani. Jin haka yasa na koma gida jikina sanyi alau domin akwai yiyuwar watarana ace gamu can gidan haya..idan kau haka ne tabbas ku in hayar Ni ce zan dinga biya kenan. Cikin lokacin komai ya yi min tsanani polion aka daina sai na koma ban da wani tsari illa abin da ya samu daga jama'ar gari mutanen arzi i masu aunata. Ina a halin ne kwatsam Allah Ya jeho Uncle Salim kamar daga sama, ya jima yana kuka ganin halin da nake ciki, cikin acin rai yace na shirya kayana da yarana mu tafi Kano, cikin sauri na ha a komai sai dai muna zuwa Mama tace bata yarda ba kar da in sake na tsallake gidan mijina na tafi tunda ba sakina ya yi ba. Babu yadda Uncle Salim bai ba dole ya ha ura amma sai da ya biya min ku i na sauya jarabawa ya biya min jamb
Chapter 34 · 0% Book details