← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 133

Sashe 64

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 33 A motar kowa kallon Jiddah yake, har wasu na tunanin ko dai mutuwa akai mata ko kuma mijinta ya sake ta idan tana aure, hakan yasa. Mustapha jin kukan Jiddah yake tamkar zubar ruwan dalma a rauninsa. Ji yake tamkar ya janyo ta jikinshi ya lallashe ta , baki aya ya rasa sukuni ko jin da i, so yake ya lallashe ta amma ya rasa da wa anne kyawawan kalmomi ne zai lallashe ta. Hakan yasa ya kife kansa shima ya kama kukan, domin suya zuciyarsa ke yi ba ka an ba. Tashin hankali yake shiga ko a tunani ya hasaso Jiddah a damuwa balle yanzu da take gabansa yana kallonta tana kuka mai cike da damuwa. Sosai yake jin ina ma ace tana matsayin matarsa ne akai hakan, tabbas da har su isa Kaduna tana lafe jikinsa yana lallashinta da gaya mata kalaman soyayya wa anda za su saka mata natsuwa ko ya ya ne a zuciyarta. Hawaye yake sosai duk lokacin daya kalleta yaga nata hawayen sai nashi hawayen sun zubo. Jiddah kamar ance ta kalli kujerar da yake sai taga yana kuka abin da ya tsaida nata kukan kenan ta tambaye shi da muryar kuka abin da ya sa shi kuka. Cikin raunanniyar murya ya ce mata, "Na rasa yadda zan yi na lallashe ki ne, don haka kukanki ke sakani kuka nima, wallahi ban so na ganki a damuwa ko naga ranki ya aci sai naji nima nawa ran ya aci ko naji damuwa fiye da taki damuwar ma. Don Allah ki yi ha uri ki daina kukan nan tunda dai kin gano inda take insha Allah ita ma Mama zata ku uta domin ina ji a jikina Alawiyya ba zata ta a bari a kada ta a shari'ar mahaifiyarta ba. Anya kuwa kin san wacece Barista Alawiyya akan aikinta kuwa? To ita in ta shahara tayi aurin suna kan kada duk wanda ya ja da ita a Shari'a kowace irin Shari'a ce kuwa don haka ki daina damuwa insha Allah muna zuwa nasan komai zai daidai." Magana yake mata cikin natsuwa da lallashi, sai ta samu kanta da sauke ajiyar zuciya akai-akai. Hannu yasa ya goge mata hawayen fuskarta ya sakar mata murmushi cike da son kore mata damuwa ya ce, "Wai me yasa wasu matan ke ara kyau idan suna kuka ne?" Bata san lokacin da dariya ta su uce mata ba,ta ce cikin dariyar, "Au dama kuka kyau yake arawa? Ai ban da labari gunka ne Yau farkon jin wannan sharhi na masu kuka to." Har zuwa yanzu kallonta yake, kallo mai cike da auna da soyayya ya sake murmusawa ya ce, "Ke ba fa wai gane wa nake ba a sauran matan, ke ce dai na lura da hakan gunki a Yau don haka nayi tunanin akwai wasu matan ma masu wannan baiwar kyan idan suna kuka." Tana lura da har matar dake gefenta sai da tai murmushi jin maganarsa. Ganin ta kasa magana sai kuma ya ce, "Kin san wani abu ma dake ban mamaki gare ki? Ko da yaushe fara'arki ara yawaita take alamar cewa ke baki san Buhari na mulkin Nigeriya ba ko?" Dole ta sake yin dariya tace, "Kana dai zolaya ta ne kawai, amma an makaranta ina shi ina wani jin da in rayuwa balle har aje matakin daka aje Ni." Matar dake zaune ta kasa ha uri ta dubi Jiddah tace, "Baiwar Allah gaskiya mijinki na sonki idan fushi kike da shi ko wani abu ya yi maki ki danne a asan zuciyarki domin samun najimi mai ba mace kulawa irin wannan matu ar wahala yake a wannan lokacin , ke kin samu naga kina son wasa da damarki don Allah ki gyara yarinya kafin lokaci ya ure maki." Kunya ta kamata, domin dai ga dukkan alama ya ji abin da matar tace don sai murmushi yake yana basarwa. Cikin in'ina tace wa matar, "Ayyah ! Ai ba mijina bane ba, shi in Uncle ina ne ko kuma Yayana." Matar ma murmushi tai, "To gaskiya indai haka ne yana matu aunarki sosai yadda har hakan ya gaza oyuwa ga idanun mutane. Shawarar da zan baki ita ce kar da ki rasa wannan umbin aunar yarinya." Yau tana ganin ikon Allah! Haka kawai mace daga ganinsu tare sai tace wai soyayya? Ita kam ko kalmar so bata son ana gaya mata, ji take da tana da iko ko damar dakatar da soyayya da yanzun babu mai sake ambatar soyayya a wannan lokacin, don haka sai ta ja bakinta tai shiru kawai fuskarta ba yabo ba fallasa. Shi kam Mustapha ji ya yi idan ba kyauta ya yi ma matar ba, zuciyarsa ba zata sarara ba, daga tsabar jin da in abin da tai mai ba, yana cikin jin da in aka tambayi ku in mota sai kawai ya bada hada na matar tunda wannan ce hanyar da kawai zai iya bata tukuicin maganarta. Saboda haka sai kawai Jiddah ta janyo wayarta ta fara latse-latse kai tsaye sai kuma ta rubuta sunan Alawiyya ta shiga cikin page inta. Ta cigaba da karanta abubuwan da suka shafi Alawiyyar tana jin tsantsar farin cikin cewa rayuwar Alawiyya ta yi kyau bayan rabuwarsu, har ta ga inda Alawiyya ke cigiyarta da sunan ta da an wani labari na su wanda zai sa ta gane da ita take. Hawaye suka zubo mata, "Tabbas ta ji da in ganin Alawiyya a matakin da take yanzu, ba mamaki ita iyayenta ba su yi mata yadda nata iyayen su kai mata ba, n yi mata auren wuri ba tare da tayi ilimi mai zurfi ba, ko da yake ai ita Alawiyya daman iyayenta suna sonta kawai addara ce ta raba su, tasan kuma ita ce ta sake ha a su har su kai mata jagora ta zama abar alfahari ga jama'a. Ganin ta koma kukan sai ya ji nashi hawayen sun dawo, ko da wasa bai son ganin damuwa a fuskarta, yana son kallon murmushin nan nata da ko da yaushe yake kan fuskarta. awarine ya yi ma kansa duk ranar daya aureta ba zai sake barin hawayen damuwa, ko ba in ciki zubowa daga kyakkyawar fuskarta ba. Sai dai ko yanzu yana so ya zama babbar katanga mai kange mata zubowarsu amma ta ya zai hakan? Sosai ya yi zurfi a tunanin hanyar da zai bi ya jefa natsuwa da walwala a fuskarta, don har ga Allah ji yake ya fita shiga cikin mayuwacin halin da take ciki, zafi sosai zuciyarsa ke yi, una yake ji duk sadda hawayenta suka fito ji yake tamkar ana yankan naman jikinsa ko ana gasa zuciyarsa da garwashi. Jiddah kuwa tai nisa a tunanin Alawiyya sai ta samu kanta da tuno rayuwarsu ta baya, komai ya dawo mata dalla-dalla a cikin zuciyarta. Kawai sai ta tsinci zuciyarta da hasko fuskar mahaifinta, rabon da ta saka shi a idonta tun ranar data haifi su Afnah bata sake ganin sa ba. Ita kam tasan cewa tafi wani marayan maraici indai akan Uba ne, domin ita nata Uban sam bata ma san inda yake ba balle ace tasan ya yake ba, tana son ko a mafarki ne ta ganta da mahaifinta suna wasa da dariya ta ganta zaune suna magana ba ta fa a ba, babu zagi babu tsangwama tabbas a ranar da sai ta yi sadaka ta godiya ga Allah, amma abin da yafi arfinta ko a mafarki kenan. Wasu hawayen suka sake zubo mata masu aci wai yaushe ne zata daina hawaye a rayuwarta? Yaushe ne zata daina ba in ciki a rayuwarta? Allah Sarki Uncle Salim kai ne kawai mai fahimtar damuwa ta ko da ban ce mai komai ba, yakan fahimci abin da take bu ata ko da bata nuna a fuska ba, yakan nema mata mafita kan hanyar data shige mata duhu ko da tai nisa hanyar yakan gajarce mata ita. Uncle Salim shi ne kawai mai mata albishir da alheri da abin alherin gareta, shi ne ko da yaushe bakinsa na kanta, ko da yaushe shawara yake bata ta tsaya da afarta ta tsaya ma rayuwar yaranta ta zama jaruma jajirtatta kan lamarin ta dana yaranta duk rintsi ta tsira da abu biyu zuwa uku a rayuwarta, karatunta, karatun yaranta, sai kuma sana'a to tabbas ba za ta ta a wula anta ba. Shi ne wanda ya biya mata komai na karatunta kamar yasan zai tafi ya barta ya ajiye mata ku en da zasu isheta karatunta a bankinta, bata mance ba ya matsa mata kan maganar bu e banki ya takura mata sai da ta bu e bankin ashe don ya saka mata ku in da zatai karatu da su ne. A fili ta dinga cewa, "Allah ka ji an Uncle Salim ina, ka gafarta ma shi, kasa ya huta. Allah ka azurta shi da jin da in zaman kabari kasa yafi jin da in can fiye da yadda ya ji da in rayuwar duniya." Kuka take sosai wanda sai da mutanen gun suka dinga yi mata magana kan tai ha uri, domin yanzu sun fahimci rasuwa ce akai mata jin addu'ar da take ta yi da arfi. Shi kanshi Mustapha sai rayuwarsa da Salim ta dawo mai sabuwa a ransa. Duk da sun kasance an'uwa ne na kusa kuma sa'annin juna to akwai wata sha uwa ta musamman dake tsakaninsu, domin ba su ne kawai kai guda ba a cikin dangin nasu ba suna da yawa wa anda suke kai aya amma basu shiri kamar yadda suke shiri da Salim kaf dangin nasu, ko da yake a gidansu Salim in ma su hu u ne maza amma da Salim kawai yake shiri. Salim mutum ne mai hangen nesa da sanin ya kamata, bai mantawa duk lokacin daya fuskanci yana cikin damuwa yakan zauna ya dinga ba shi ha uri ya ce mai, "Musty kana ban mamaki idan kana damuwa da sabgar mata, su fa mata baki aya idan ka fahimce su zama da su sai ka iya ha uri da kau da kai, sannan sai ka zama shasha
Chapter 64 · 0% Book details