Sashe 52
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Page 29 *Ban san da wane baki ba zan gode ma masoyana ba, masu kirana da masu turomin sa o sai dai ince Allah Ya bar auna da zumunci ina godiya kan alherinku gare ni sosai* . Suna cikin tafiya, sai Barista Alawiyya ta hango wata ba ar mota na binsu a baya, murmushi tai kawai ta saki kan motarta, maimakon ta koma gidan da suka kwana sai ta auki hanyar gidan gonar Babanta dake hanyar Zariya cikin an dajin dake tsakanin Kaduna da Zariya yake, ashe shima Daddy yaga motar don haka duk inda Alawiyya tai ita yake bi, ya yi mamakin abin da yasa ta kaisu gidan dake cikin jaji amma sai ya bari su isa sai ya tambaye ta. Sai kuma ya ga wata jar mota irin waccan ba ar na bin bayan waccan ba ar motar, hakan yasa ya kasa jurewa ya kira wayar Alawiyya. "Alawiyya ta ya za ki kaimu dawa bayan kina ganin mota har biyu na bibiyarmu? Kamar fa kin yi wauta a lamarin nan, saboda kin ga Hausawa na cewa Sarkin yawa yafi Sarkin arfi mota har biyu wa yasan abin dake cikin su?" Sai da ta furzar da numfashi sannan tace cikin muryar ko'in kula, "Kar ka damu Daddy mota guda tawa ce, gudar ce nake bu atar ta zama tawa ita ma, domin na jima ina mafarkin samunta sai Yau na ganta." Ta kashe wayar tana wani murmushi. Dr. Faisal ya ara gyara zama ya ha iye miyan bakinsa da yar ya ce a ransa, "Anya kuwa wannan Alawiyya ce wadda na sani? Wadda mutane suke kira shegiya iyar shegiya tashin Lagos? Anya kuwa ita ce wadda wajen kwana ya gagara shekarun baya da suka wuce? Tabbas idan ita ce to an sauya mata halaye kaso tamanin da tara na halayenta sun fece." Ya sake kallonta abin mamaki wa a ta kunna ta shiga girgiza kanta tana bin wa ar ko alama babu sauran acin rai a kan fuskarta. Kasancewar gidan ba kowa cikinsa, tunda babu wani abin amfani ciki yasa sai da ta fito da kanta ta bu e gidan, ta ja gate in gidan ya bu e Daddy ya shige a lokacin ne ba ar motar ta juya da gudun tsiya tabar gun, ita ma jar motar ta mara mata baya. Suna shiga cikin gidan kai tsaye kowa ya kama akinsa, amma sai Alawiyya ta dawo falo ta zauna ta kunna wa a a wayarta, ta kama rubuce-rubuce. Hakan yasa su ma su Daddy suka fito falon don duk jininsu akan akaifa yake, sun ga motoci na bin bayansu amma kuma tace wai guda motarta ce, gudar kuma neman ta take daman har a mafarki tabbas Alawiyya dabance ko da yaushe ara tumbatsa take gun ba da mamaki kan lamurranta. Cikin hikima ta dinga jansu da labari kan shari'ar da ta ta a yi irin wannan da hanyoyin da ta dinga bi har ta samu nasara. Sai suka samu kansu da daina jin tsoro suka ji tamkar ma an yi shari'ar an samu nasara, don haka Daddy yafi murna ya dinga saka mata albarka yana arawa. Sai da taga hankalinsu ya kwanta sannan ta shige aki sai gata ta fito cikin ba en kaya riga da wando hatta fuskarta ba a iya gani, su kansu don a gabansu ta fito da ba za su iya gane ta ba, hatta hannuwanta ba ar Safa ce, ta rufe kanta da ba ar hula irin mai rufe hanci wayar idanunta kuma ta saka ba in gilashi ta da Cikin an sauri tace, "Daddy idan na fita da awa guda za a kawo maku mota ku shiga za a maida ku gidana na cikin gari, amma idan mai motar ya zo to nice zan kira ku, kada ku bu ofa duk bugun da za ai mata ku jira kirana, zan je wani aiki ne na dawo sai mun ha e gida." Dukkansu kasa magana su kai, musamman Daddy da bai saba ganinta a wannan shigar ba, sai kace namijin Film in indiya ko American films. Ganin sun kasa mata magana yasa tai murmushi ta fice ta ja ofar ta baya ta rufe, cikin wani aki ta shige sai gata ta fito da sabon mashin ta haye ta fice, duk abin da take su Daddy na tsaye gun tagar da in suna kallonta, ba wanda bai mamakin ganin ta fiddo mashin ba cikinsu. Kamar an cilla ta haka ta harba mashin in cikin daji ta kama gudun gaske tana duba location a wata aramar na'ura dake hannunta. Daidai wata siririyar hanya ta tsaya ta samu waje ta oye mashin inta ta fito da aramar bindiga daga ugunta sai kuma ta fito da wayarta ta kira Daddy tace su bi mai motar dake jiransu ofar gidan, ta maida wayar ta nufi wata aramar hanya bayan ta gyara ri on bindigarta sosai. Tayi tafiya sosai kafin ta isa wani aton gida dake cikin dokar dajin shi ka ai ne ba wani gida a dajin baki aya idan ba shi ba. arar ki a ce ke tashi a cikin gidan tamkar gidan casu. Kasancewar ofar gidan a kulle take yasa ta daka tsalle ta haye katangar gidan ta dira, a hankali ta dinga san o har ta isa ofar falon dake bu e amma kuma akwai wasu akunan sai dai su a rufe suke kamar ba kowa gidan, sai da ta le a falon ta taga ta ga ba kowa cikin falon sannan ta afka cikin warewa ta shiga akin dake cikin falon, ba kowa amma ga disko na tashi kamar ya tada gidan, cikin mintuna ka an ta fahimci wanda ta zo nema bai gidan sai budurwarsa dake toilet na wanka. Murmushi tai don hakan ma ya yi mata da Waje ta samu ta zauna bayan ta rufe ofar akin, ta jima sannan ta ji alamar bu ofar toilet in, ko kanta bata aga ba, balle ta nuna alamar damuwa ko jin tsoron kar wadda ta fito ta ganta. Jennifer da ta fito daga wanka tana sauri ta shirya kafin masoyinta ya zo, ya gaya mata akwai aikin da zai fita na sati don haka yake son su je yawo na Yau kawai don ya ji da in aikinsa, ta ga mutum kwance kan gadonta ga alama ma barci yake, sai abin ya bata tsoro ta nufi wayarta da hanzari amma kamar a mafarki taji an buge mata hannu wayar ta fa asa bata samu damar ri e wayar ba don azabar dukan da akai mata. Tun da Dauda ya kawo ta gidan nan bata ta a ganin wani ya shigo ba, idan ba yaransa ba, sai kuwa irin mutanen da yake kawowa ya aje su kuma a tsorace suke don azabar da yake gana masu shi da yaransa wasu mutuwa suke wasu kuwa dama don ya kashe su kawai yake kawo su, sai kuma manyan an siyasar dake zuwa kawo mai aiki, amma Yau ga wani shafaffe da mai ya kawo kansa har gidan mutuwa... Kaya ya mi a mata ta amsa cike da mamakin arfin halin mutumin, amma data tuna masoyinta Oga Dauda na tafe sai murmushin mugunta ya kubce mata, ta amshi kayan ta saka. Alawiyya ta fito da ankwa ta saka mata kenan ta ji dirin mota, ko shakka babu tasan ta Oga Dauda ce, ita kuma Jennifer tana jin dirin motar masoyinta sai ta wage baki da nufin yin ihu, ta manta arar discon data kunna ba zai bari ko arar harbin bindiga a ji ba. Cikin sauri Alawiyya ta fisge ta kamar wata aramar yarinya haka ta jata suka fice daga akin ta bu e na kusa da shi suka shige, a lokacin da yaran Oga Dauda suka shigo auke da bindigu suna ihun bin wa ar dake tashi cikin gidan. Suna shiga akin Alawiyya ta ga mutune su uku aure da igiya duk dattawa kuma maza, suna ganinsu suka nuna alamar razana, amma ganin yadda aka wurgar da Jennifer matar gidan sai suka waro idanuwa waje suna kallonta da mamaki arara kan fuskarsu. arar ki an ta tsaya, sai kuma su ka ji ihun yaran na a kiran sunan "Madam where are you?" Cikin sauri Alawiyya ta toshe mata baki, ganin zata bata matsala yasa ta kama bayan kunnenta ta murza kawai sai Jennifer ta fa i a sume ba numfashi. Cikin ra a Alawiyya ta dube su tace, "Ku me kuke a nan?" Suka kalli juna suka ara kamar masu mamaki sai guda ya ce, "Sunana Alh. Hassan garkuwa su kai da Ni Yau sati guda, sai iyalina sun kawo masu Miliyan goma za su sake Ni." Cikin mintuna ta fahimci damuwar don haka ta nuna masu I'D card in ta, tace "Ku ban mintuna biyar na gama da su na dawo." Bata jira komai ba ta kwance masu aurin, ta bu ofar ta fice ta maida ofar ta rufe, hakan ya yi daidai da fitowar yaran Oga Dauda uku tsakar gidan, cikin sauri suka zare makamansu suka nufi Alawiyya da nufin yi mata kwa aya. aramin mamaki su kai ba, ganin yadda mutumin ya ware gun kare duka da maida martani cikin lokaci , ba su ankara ba, har ya buge biyu da mummunan raunuka shi kau har zuwa yanzu ko sau aya ba wanda ya samu ya isa gare shi, sai shi ne kawai ke ta dukansu ta ko'ina tamkar ba shi ka ai bane su kuma su uku ne ba. Sauran biyun su ma suka shigo suka sake komawa su uku, amma a banza don haka suka auko bindiga don wu a bata kama shi suka harba, sai dai arar alburishin kawai suka ji ya fa asa ba wani alamar jini alamar ita ma bai ji kenan. Sai suka karaya cikin sau i Alawiyya ta buge su ta aure ta watsa akin, ta fito da wayarta tace, "Maza a kawo mota babba cikin sauri." Bincike ta koma ta cigaba da yi cikin akunan gidan, duk abin da take so ta auka, sai ga motar da ta kira ta zo , cikin gaggawa suka kwashe duk mutanen dake gidan suka fice daga gidan, ita kuma ta auki mashin inta ta bi bayansu. Basu jima da tafiya ba sai ga Oga Dauda ya zo, tun a