Sashe 63
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
runtsawa yasa ya tashi ya auro alwala ya kama sallah yana neman za in Ubangiji tsakaninsa da Jiddah. Sai wajen arfe biyu da rabi ya sallame ya kwanta yana mai jin sabuwar soyayyarta na ratsa dukkan hanyoyin jijiyoyin jikinsa, a hankali ya furta, "Princess sai da safe zan kula kamar yadda ki ka ce in." Ya shafa addu'a ya kwanta barci mai natsuwa ya auke shi. Washegari tunda safe Bilkisu ta zagayo gun Jiddah da wayarta sabuwa tace, "Don Allah ki turamin WhatsApp idan kina da shi wani littafi aka ce min ana saki a wani group don haka na nace sai da maigidan ya sai min wayar nan Yau." Jiddah ta auki wayarta ta tura mata ta bu e tace, "Ni kam ban yi sam bai dame ni ba wallahi kwata-kwata." Bilkisu cike da mamaki tace "Ai kuwa an barki baya wallahi don a chat babu abin da babu wallahi dama kin bu e kin ga me duniya ke ciki, har wanda baki tunani sai ki ga kun ha u da shi a can." "Tabbas ina son na ha u da Alawiyya kam Bilkisu da nasan zan ganta da zan bu Bilkisu tace "Tabbas za ki iya ganinta indai tana yi ita ma balle yanzu chat ya ga me duniyar kowa yi yake ." Cikin sauri Jiddah ta bu e facebook, WhatsApp, Instagram duk ta saka sunanta wanda Alawiyya zata iya gane ta watau Jiddah Iyami Lagos. Nan dai su kai ta fira da Bilkisu har tace mata zata ba da Number ta a saka ta groups in da ake posting littafai da abubuwan aruwa Jiddah tace ta gode. Da rana tana kwance tana duba mutanen dake cikin WhatsApp inta sai taga lambar Mustapha shi ma ashe yana chat don haka tai mai sallama ba a jima ba ya maido mata da sallama yana tambayar ina ta oye duk Yau bai ga wulginta ba. Sun jima suna fira da shi ta gaji ta sauka ya ce anjima ta shirya za su fita tace to. Facebook ta koma taga wani posting da mutane ke ta ka-ce-na-ce akan shi don haka sai ta karanta abin da akai posting in sosai. Wata uwar ara ta saka ta ruga gun Hajjo tana kuka tana cewa, "Wallahi arya su ke mata ina bayanki sosai kuwa nasan Mama ba zata kashe mijinta ba Alawiyya." Hajjo ta dube ta sosai jin ta ambaci Alawiyya tace, "Ina kika ga Alawiyyar ke kuma? Shekara da shekaru har Yau kin kasa manta ta ba mamaki ita ta jima da manta ki ma." Jiddah ta fashe da kuka ta tashi ta shiga aki sai gata auke da jakar goyo bayanta ta dubi Hajjo tace, "Hajjo ki yi ha uri zan tafi Kaduna a yanzu ba sai gobe ba, domin in gana da Alawiyya." Hajjo ta ta e bakinta tace "Sai kin dawo, amma wallahi ko sisi ban baki Allah Ya kai ki lafiya." Ita dai Jiddah kuka kawai take, don haka ta fice hankali tashe, sai dai dole ta tsaya don ganin Mustapha gabanta hankalinsa a tashe ganin tana kuka. "Jiddah ina za ki kina kuka?" Cikin kuka tace, "Kaduna zan je gun Alawiyya Yau Allah Ya nuna min Alawiyya." Wayarta ta fiddo ta nuna mai hoton Alawiyya da Mamarta a lissafi kuma Yau ne za a shiga kotu. Kowa yasan Jiddah yasan Alawiyya kowa yasan Salim yasan labarin Jiddah don haka ya tuna lokacin da Salim ya sa shi su kai ta neman Alawiyya basu ganta ba, don haka ya ce "Tabbas dole ki yi kuka ba zan barki ki je ke ka ai ba don haka bari na fito mu tafi tare." Kafin tace komai ya fa a gidansa. Bata jima ba sai gashi ya fito suka tsaida keke napep ya kaisu tasha suka shiga motar Kaduna har zuwa lokacin Jiddah kuka take. To masu karatu mu ha e a kashi na gaba don jin yadda zata kaya. Taku a kullum Haupha [8/30, 3:05 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa