Sashe 110
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
bakin ta gyara aurin kallabinta ta zauna tana jiran taji su waye suka zo. Tana jin yana magana da yara sai ta fito, kayan alaci ne aka aiko daga gidan Yayarsa ta amshi kayan tana tambayar yaran ya Auntyn take, ta juye komai ta zuba masu cin cin da dubulan suka zauna suna ci ita kuma ta ja Prince suka shiga kicin in don zubama Auntyn kayan bikin nata yaran su tafi da su. Sai ya dinga ganin abin kamar a mafarkin daya saba yi na rayuwar da yake so suyi da Princess insa idan sun aure, nisha i suke su duka kowa cike yake da annashuwa har ta gama zuba komai yana cewa sun yawa tana cewa Auntynsa za a kai mawa ko tata? Dole ya ja bakinsa yai shiru don abin yafi arfinsa. Suna fitowa yaran sun gama ta basu kayan tace su gaida mata da Auntyn sosai. Suna tafiya suka koma inda suke da ta jawo wayarta ta kira lambar Alawiyya kamar jira take daman ta kama kiran tana cewa, "Kaga amarya a gidan Mustapha bada kanki a sare ki je gida kice ya fa i, tun azun nake aukar waya da zummar kiranki sai Abbansu Anam ya hanani ya ce yasan baku tashi ba, haka kawai zan matsa ma sabbin amare da kira." Dariya ta saka tace, "Ya kyauta min kuwa, domin yanzu haka juyin farko ne mukai abinmu." Alawiyya tace,"Ai fa abu ya zo ga ma'iya daman breakfast in ku ne nace ya za ai kuna iya bu e gidan yanzu a kawo maku koko sai anjima?" Tai murmushi tace, "Aunty ta jima da kawo mana breakfast Madam ke dai kice kin kira ki ji gulma kawai to Prince da Princess na lafiya." Wayarsa ce tai ara don haka ya auka bai ma duba suna ba, sai ji ya yi ance, "Sai ka zo kaba yara ku in makaranta da ku in cefane?" Murmushi ya yi don Maryam ce hatta Jiddah dake jikinshi tana waya tana jin yadda take magana cike da gatsali da fusata. "Yanzu za a kawo, bari na kira waya, amma har cefanen jiya duk ya are?" "Ban sani ba, sai ka zo ka duba da kanka , kai dai ka ji haushin kanka kuma wallahi ka ji tsoron Allah tun yanzu ka fara mugun halin naka, to indai kai ne ai gata ga ka nan muna nan zamu ga yadda zata kaya." Murmushi ya yi yana cigaba da wasa da kitson Jiddah ya ce, "Shike nan za a kawo maku komai." "E daman kace haka man, ai Allah Ni ba zan juri wula anci ba don ta amar kayi wani auren banza can." Kashe wayarsa ya yi kawai don yasan idan ba katinta ya are ba, ba zata tsiyaya mai masifa ba, shi kam ko zaginsa za tai ba zai ji komai ba yanda yake tare da Princess insa matsayin matar aure . Duk abin da tace mai tsab Jiddah ta ji sai tai kamar bata ji ba, suka cigaba da waya da Alawiyya. Sallamar an Jalingo ce tasa ta tashi daga jikinsa su kai sallama da Alawiyya ta fita waje ta tarbe su, shi kuma ya koma aki. Sun gaggaisa suna ta zare ido sunga gidan Jiddah kamar ba Nigeria ba, gida mai kyan gaske ya ji kayan alatun rayuwa komai akwai a gidan wani abun ma basu san ko miye ba. Jiddah ta tarbesu da martaba ta kawo masu kayan abincin da Aunty ta aiko masu da shi, suna ci suna sunne kai domin baki ayansu ba wadda ta ta a taka afarta gidan auren Jiddah da Deeni. Suna gamawa ta kwashe kayan ta kai kicin ta le akin tace mai ya fito ya gaisa da mutan Jalingo suyi bankwana za su koma gida Yau. Tare suka jera suka fito yana ri e da hannunta suka gaisa suna ta yi mai Allah sa alheri da fatan zaman lafiya, ya kawo ku i yaba Jiddah ya ce ta basu idan za su tafi zai an fita ya je ya dawo. Ta basu ku in sunata godiya tabi bayan shi yana tsaye yana kallon ofar akin da tsammanin fitowarta . Tana zuwa ya bu e hannu ta fa a ciki ya maida ya rufe suka dinga saukar da ajiyar zuciya. A cikin kunnenta ya ra a mata, "Zan fita Princess ba jimawa zan ba zan dawo, zan je nima nayi bankwana da wa anda suka zo daga wasu garuruwan an'uwan Mamana." Cike da kulawa tace mai, "Allah Ya tsare min kai, Ya kiyaye min kai, Ya Kai ka lafiya Ya dawo min da kai lafiya Prince. Ina fatan zaka runtse Idonka daga kallon kowace mace, idan ma tsautsai yasa ka kalla kaga abin da ya birgeka a jikinta don Allah ka kira Ni a waya ko ka turomin message ka fa a min ko miye kafin ka dawo na tanadar maka ko miye ma." Suka ha e bakinsu waje guda suna kissing in juna na tsawon lokaci, sannan ta zare jikinta tana sake maimaita mai addu'a yana amsawa da "Amin Princess, sai na dawo ki kulamin da kanki sosai don Allah ban da aiki ki kwanta ki huta har in dawo." Murmushi tai tana sake aga mai hannu har ya fice daga gidan. Mutane da dama suka dinga shigowa ganin amarya da akin amarya, amma ita hankalinta na kan wayarta da suke chat suna waya da Prince inta yana gaya mata yadda yai kewarta itama tana gaya mai yadda tai tata kewar har tana cewa ta rame ita dai ya dawo gida haka nan ko ta saka mai kuka. Jin hakan yasa ya ru e ya ce mata ga shi nan zuwa yanzu insha Allah yana hanya. Ko da jin haka sai ta tashi da sauri ta shiga kicin kasancewar ta bada an siyo mata kayan miya da kifi ta ora taliya ta gama ta yi mai gurasa ta ha a lemu mai da i ta saka a fridge sannan ta shiga wanka tana fitowa matan dake gidan suka ce za su tafi ta zuba masu kayan biki ta raka su ta rufe gidan da niyyar ba zata sake bu e wa kowa ba sai Prince inta. ananan kaya ta auko masu kyau ta saka tai bala'in kyau a cikin kayan domin komai ya amsa sunansa a jikinta ya kuma bayyana ta fesa turare ta sake gyara ko'ina ta dawo kan kujera ta zauna ta kira shi. IN ALLAH* Labari da rubutawa