← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 133

Sashe 32

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page 21 Na du a na auki wayar na shige aki, ku in na irga naga sun kama dubu goma sha takwas, nayi murmushi na adana abuna na mi e cike da warin gwiwa na ora sanwar taliya, cikin lokaci ka an na gama, na zuba a tire na zauna kenan zan ci sai ga anina da gudun masifa yana ta shassheka ya fa i gabana yace, "Mamarmu tace, duk abin da kike ki yi maza ki je tana nemanki yanzu-yanzu." Gabana ya fa i na kalle shi nace, "Bata da lafiya ne?" Ya girgiza kai sai kuma yace, "Lafiyarta lau Babansu Haidar ne ya je da gudu yace kin auki wu a za ki kashe shi." Ni abin dariya ma ya ban, don haka sai na gyara zama na ce, "Idan zaka ci abinci, bisimillah ka ji, idan muka gama mun je kiran ba na gaggawa bane ashe." Ya zauna kuwa na zuba mai, muna ci ina tambayarshi abin da Abban Haidar ya ce da yaje. Yana dariya ya ce, "Yo yana shigowa sai ganinsa mu kai kanmu yana ta nishi yana kallon bayansa, shi ne Mamarmu tace mai lafiya kuwa? Ya ce "Wallahi Jiddah ce ta fiddo wu a zata kashe Ni, shi ne na rugo nan, don Allah ki bata ha uri kar da ta kashe Ni." Mamarmu ta zabura tana Salati tace, "To ita kam me ke faruwa da ita ne? Kanta lafiya kuwa, anya tana cikin hayyacinta kuwa?" Ya zauna yana cewa a ba shi ruwa masu sanyi don Allah. Shi ne fa tace na rugo da gudu na kira mata ke. Sai da muka gama cin abincin na amso yarana sannan na tasa anina gaba, muka nufi gun Mamana ina tafe ina lissafin yadda za mu da Mama idan na isa, nasanta bata da son rigima kwata-kwata magana kanta bata dameta ba, nasan tana can ta kasa tsaye ta kasa zaune Yau ta ji zan yi kisan kai. Muna shiga kau na iske ta tsaye tayi zugudum alamar tunani take, tana ganina tai ajiyar zuciya ta shige akinta na bita. Tun kafin in zauna ta fara cewa, "Wane irin mugun labari ne nake ji ya fito daga gareki iyar nan? Kisan kai fa nake samun labarin za ki aikata? Anya kuwa kin san darajar aure kin san wane ne miji da darajarsa? Shin kina san ki gama da duniya lahiya kuwa iyar nan?" Ai sai Mama ta fashe da kuka abin da ya tada min hankali kenan, domin ba abin da na tsana irin naga Mama ta sauya fuska ko alamar damuwa a tare da ita, sai nima na kama kukan na kasa gaya mata abin da ya faru. Sai da muka gama kukanmu sannan Mama tai ta min nasiha taban shawarar na dinga shan ruwan alwala idan na rage ta sallar la'asar. Ni dai na samu naita bata ha uri har muka rabu lafiya na kama hanya na koma gida ina jiran Abban Haidar ya zo naga da me zai zo kuma. Wai nice nace zan kashe shi! Abin yaban mamaki ba an ka an ba, tabbas na yarda Abban Haidar zai iya shiga tsakanina da Mama don haka ya zama tilas na san matsaya ta da shi, don ba zan lamunci ya dinga zuwa yana tada ma tsohuwata hankali ba. Da dare na le a gidan Maman Khairat na gaya mata abin da ya faru Yau, da yadda mu kai da yarinyar da Abban Haidar yaba kayana da zuwansa gun Mamana da yadda ya je ya yi min sharri gun Mama zan kashe shi. Itama dai fa a tai min kan bai kamata ba, da na bar mata kawai na kwashe kayana daga gidan shike nan, ai sai ya gani sannan zai auka, idan ban aje ba ya gani ai ba zai auka ba. Wajen tara na dare na bar Haidar nan gidan ya auki su Afnah na nufi gida hankalina kwance. Sai can cikin dare naji alamar shigowar Abban Haidar kamar naje nayi mai magana sai kuma na fasa, kamar na auki wayarsa na ba shi sai kuma na tuna wayata hu u yana saidawa daga aro, wata ma auka kawai yake sai dai na fahimci ya saida da kaina ba dai ya gayamin ya saida ba, haka waya uku yana cinyewa ta Mama don haka don naci wannan ba wata tsiya bace, cikin wanda ya ci nawa ne na amshi guda, ko da na gama wannan tunanin sai na auko wayar na zare sim card in na tura gefen kujera wayar kuma na adana ta cikin jakar hannuna. Bayan na gama sallar asuba na koma na kwanta naji mutum kan kaina yana magana, Ni kuma daman nace idan dai ba kiran sunana ya yi ba ko yace Maman Afnah ko Afnan ba zan amsa ba don ya shekara kirana da Ke. Komi ya gani sai ya an bubbuga afa ta na bu e idona na watsa mai su, nace "Lafiya Abban Haidar?" Cikin maganar hanci ya ce, "Ina wayata? Kamar nan na yada ta jiya." Na tashi zaune ina murje idona nace, "Wace wayar kuma Abban Haidar? Ni ba wanda ya kawo min ajiyar wayarka nan gidan gaskiya." Ya an tsura min ido kamar yana son karantar wani abu kan fuskata sai kuma ya ja tsaki ya juya aki. Na ta e bakina na gyara kwanciya ta, nace a raina kai dai ka sani amma waya da ku i sun zo kenan sai dai wasu. Bayan na gama gyara gidana nayi wanka na yiwa yara na wanke kayan da na cire masu don na saba da yadda tsohuwar dake dafa min ruwan wanka take tana gama masu wanka take wanke kayansu, nima sai na auki halin ina gama masu wanka nake wanke kayansu. Hatta karin kallo na gama, na shirya tsab ina karanta wani littafi (ADON DAWA) na Jamila Umar Tanko, sosai labarin soyayyar Aunty Madina da Abba ya tsaya min a zuciya, ko shakka babu irin soyayyar da nakeafarkin samu kenan a rayuwata, amma ina zan masu mai yi mun ita? Duk da cewa har zuwa yanzu ban cire rai da samun irin wannan soyayyar ba, amma na rasa ta ina zata zo min, waye zai nuna min ita ? A wace duniyar za mu ha u? Duk ban sani ba, amma nasan dai ba zan iya barin gidan Abban Haidar ba, saboda ba inda zan je idan na bar gidan, amma ina addu'ar Allah Ya azurta Ni da samun soyayyar da nake mafarki ko da ta yini guda ce a wajen Abban Haidar... Sallamar da na ji ce ta katse min tunanina na tashi duk da nasan maigidan na nan na nufi ofar gidan don ganin mai sallamar saboda tunda na fara sana'a mutane na zuwa amsar atamfofi da shadda wajena bashi sai arshen wata su biyani, shi yasa Abban Haidar idan za a shekara sallama bai amsawa balle ya fita. Ina zuwa kau na iske Baban yarinyar jiya, na du a na gaida shi, domin tsoho ne, ya dube ni ya sadda kansa asa ya ce, "Yarinya na zo ne na kawo maki kayanki, na kuma baki ha uri kan abin da ya faru don Allah ki yi ha uri yaran yanzu ka haife su ne baka haifi hakinsu ba." Na mi a hannu na amshi kayana na duba naga komai na ciki nace ina zuwa. Komawa nayi aki na auki ku in na irga dubu takwas na irga hu u sai kuma na tuna ba lallai bane ba idan ya je yaba matar ku inta don haka sai na aje na matar na fita na ba shi ku in shi nace " irga Baba." Ya gama irgawa ya ce, "Tabbas sun cika haka na baki su." Nace to madalla, amma don Allah Baba idan kun orawa yaranku talla ku dinga ankarewa da abin da suke idan sun zo birni tallar don gudun lalacewa. Ya girgiza kai ya ce, "Ke dai bari iyata ai Hinde ta ja wa kanta domin jiya muna komawa gida sai ga aike daga gidan angwayenta wai a basu kayan aurensu sun fasa, sun samu labarin abin da ya faru." Naji ba da i amma kuma ya na iya, don haka nace, "To Baba me zai hana ku ce shi maigidan nan (Abban Haidar) ya fito a maida auren kansa?" Ya yi murmushi irin nasu na manya ya ce, "Ai hakan ba zai yiyu ba, saboda kowa nasan ya kai nashi gidan kirki iyata ke dai ki ta ha uri da addu'a." Ya barni tsaye ina jinjina maganarsa, Abban Haidar na iske zaune kan kujera ya dubeni fuska ba walwala ya ce, "Ai sai ki ban ku ina yanzu ko? Tunda an kawo maki kayanki, bayan rashin mutunci da rashin kunya ma me ye abin rufe masu yarinya daga kawai kin ji labarin an bata kaya sai kace ke ka ai ce mai kaya a garin nan." Yanzu Ni kaina nasan nafi Abban Haidar miskilanci don haka duk maganar da yake ala ban ce ba, ko inda yake ma ban kalla ba, arina guda shi ne na goya Afnah na sa a Afnan na bar gidan don ban san muna zama ko kusa da juna. Gabanshi na fiddo da sauran kayana na irga na tattara su na auki sabon kwa on dana siyo guda biyu na fitar da makullan na raba su biyu na aje mai rabi na fice da rabin na sungumi kayana na fitar waje na kai gidan Binta sannan na dawo na auki Afnan duk yana yadda na barshi. Alhamdulillah! Sana'a ta amshe ni domin yanzu har kayan kicin nake siyowa ina saidawa, na koma ba abin da ban saidawa kuma ina samu ba laifi, don haka ba wanda zai ganni yace ina fuskantar matsala a gidan aurena. Sai dai zuwa lokacin tsakanina da Abban Haidar sai ido domin na gaji da yadda yake kawo mata cikin gidan da zarar na fita, tabbas idan zan dawo da wuri sai na iske shi da wata hakan na ara jefa min wutar tsanarsa a raina amma ba yanda zan a haka dai nake cijewa bayan lokaci-lokaci ina ba shi ha insa idan ya nema. Lokacin dana yaye su Afnah sai kasuwa ta fara ja baya domin mutane duk sun amshi kaya ba
Chapter 32 · 0% Book details