Sashe 92
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
koma can gefen gadon ta ra e tana gunjin kuka tace da arfi. "Me nayi maki da zafi ne da har kike min wannan maganar? Me yasa kike son kunyata ni tare da ci mun fuska ne Alawiyya? Ashe akwai ranar da kishi zai sa ki yi min wannan kallon? Kin manta da cewa Ni dake a Uwa aya Uba aya muka rayu haka kuma muke cigaba da rayuwa ne? Alawiyya ina hankalinki da tunaninki yake ne da har suka barki ki kai min wannan mummunar fahimtar? Kin ban mamaki Alawiyya ban ta a tunanin za ki min haka ba ko a mafarki na gode sosai ba mamaki don ina zaune a gidanku ne yasa ki kai min haka amma ba komai zan koma namu gidan ko da kuwa ace ban da shi zan nema." Alawiyya ta daskare a gun ta kasa ko aga halshenta tana ganin Jiddah ta auki hijabinta ta fice daga akin tana kuka sosai. Itama kukan ta saka tana jin me yasa tai ma Jiddah maganar ne? Ga shi nan ta kasa fahimtar ta ai har ta yi tunani na daban kan lamarin. Jiddah na fita ta le akin mai aikin gidan tasan su Afnan na can na wasa ta tarkata su kai tsaye tasha ta nufa ta hau motar Kano tana rungume da yaranta tana kuka mai sauti wanda yasa su ma yaran kama yin kukan, kowa na motar na kallonsu ba mai bakin yi mata tambaya don duk wanda ya ganta zai fahimci mutuwa ce kawai akai mata tasa ta a wannan yanayin. Har suka isa Kano bata daina kuka ba, napep ta hau har ofar gidan Hajjo, zuwa lokacin ta daina kukan sai dai kallo guda zakai mata ka fahimci ta ci kuka bana wasa ba. Yana zaune yana tunanin gobe ba bin da zai hanashi zuwa Kaduna kafin ya wuce wajen wata kwangilar aikin da ya samu sai ga napep ta tsaya ba aramin tashin hankali ya shiga ba ganin Jiddah a cikin mugun yanayi ba, kallo guda ya fahimci ta fi awa hu u tana kuka kuma damuwa ce fal ranta , tabbas akwai abin da akai mata mai girma daya sa ta zo tun daga Kaduna har Kano a cikin wannan yanayin. Yana kallonta ta ba mai napep in dubu aya yana magana ta aga mai hannu ta ja yaranta suka shige cikin gidan ko waigen mai napep in batai ba. Tsab ya tashi shima ya bi bayanta gabansa na fa uwa sosai da sosai, sai ya ji shima duk damuwar ta nanna e shi ta ko'ina. Tana shiga Hajjo na zaune tana duba wata tsohuwar jikka ta Uncle Salim data gani a ashin gadonta Jiddah ta fa a jikinta ta fashe da kuka mai cin rai. "Hajjo me yasa Alawiyya zatai min haka ne? Akan me zatai min wannan aukar? Me nayi mata ne da zata ce zan iya auren mijinta? Shin nayi kama da mai cin amana ne marar sanin darajar halacci da abota ne Hajjo?" Hajjo da farko tsoro taji sai daga baya ne ta fahimta sai tai murmushinsu na manya tace, "Shi ne abin kuka Jiddah daga wannan maganar? Na auka ai ke da Alawiyya har abada ba wanda ya isa ya shiga tsakaninku ya rabaku ai? Yanzu ina Alawiyyar take ita?" Cikin kuka ta gayama Hajjo abin da akai tas. Kawai samun waje ya yi ya zauna ya dafe irjinsa da yake ji tamkar zai faso irjin ya fito. Me yasa Alawiyya zatai mai haka ne? Me yasa ta zama mai son kai irin haka? Ba ita ce ta kamata ta so zuwan Jiddah gidanta ba shi ne yake da bu ata gaba da baya na zuwan Jiddah gidansa saboda shike rayuwar aure tamkar ba aure ba, shi ne cike da ba in cikin rayuwar aure da takaicin rayuwar auren baki aya don haka Allah Ya kawo mai maslaha ta hanyar kawo Jiddah a rayuwarsa a karo na barkatai. Hawaye suka zubo mai bai damu da gogewa ba ya samu da yar ya taka ya isa inda take kife tana kuka jikin Hajjo ya dafa bayanta ya ce, "Jiddah me yasa ne Ni ko da yaushe nayi hangen samun sau i a rayuwar aurena sai naga ya faskara? Jiddah me yasa Alawiyya ke da son kanta da yawa ne? Don Allah ki taimaka min ki yi min alfarmar aurena don na samu ko da rabin farin cikin da nake gani da mafarkin samu ne a wasu gidajen Jiddah. Na rasa me yasa ke ka ai ce nake ji a jikina cewar waraka ga ba ar rayuwar da nake mai cike da tauye ha i da zalunci ba Jiddah. Don Allah Jiddah ki amince min ki yadda da Ni kar da ki bari a rabani da ke wallahi zan shiga mugun yanayi mafiyin wanda nake a ciki Jiddah." Kuka yake sosai tamkar aramin yaron goye. Hajjo sai abin ya bata tausayi sosai itama domin dai tasan wasu abubuwan dake faruwa na gidan Mustapha in amma kuma bata da abin cewa saboda dai fa an da ba ruwanka da in kallo ne da shi aka ce. Mustapha ya sake janyo Jiddah jikinsa ko'ina rawa yake tsabar tashin hankali da shiga ru u ya ce, "Princess don Allah ki tuna da cewa kin amince min da kanki kin amsa min cewa kina sona don Allah ki taimaka min to ki yi iyakar yinki gun korar duk wata katanga da zatai mana gicci a soyayyarmu Jiddah." Hajjo ta mi e tsaye ta kama hannun yaran da su kai cirko-cirko suna jiran ka an sui kuka suka shige aki. Jiddah ta janye jikinta tana son ta tashi ita ma ta bi su Hajjo akin Mustapha ya kama hannuwanta ya tsugunna asa ya ce, "Don darajar Allah Princess kar da ki zama silar lalacewar rayuwata! Tabbas idan kika i Ni ban san wane irin gararin rayuwa zan fa a ba, idan kika kasa amsar soyayyata ki ka aure Ni ba, kada ki yi mamaki idan aka ce maki an ganni na koma shaye-shaye ko na haukace duk ba wanda ba zai iya faruwa ba idan kika barni Jiddah." Cikin kuka ita ma tace mai, "Na rasa ya zan da kaina baki aya kun saka Ni a halin ha'ula'i ban san waye zan auka ba ban san waye zan duba lamarin soyayyarsa ba, don Allah ku yale Ni haka nan na jima da daina soyayya baki aya a rayuwata." arfi ya ci-gaba da girgiza ta yana kuka yana cewa, "Ba ki min adalci ba idan har kika sakani a cikin jerin wa anda ke sonki a yanzu kin cutar da Ni domin baki min adalci ba sam, yadda nake sonki tun kafin kisan miye so, nake aunarki tun kafin kisan mece ce soyayya nake sonki don Allah ki daure ki amshi soyayyata Princess wallahi ke ce duniyar soyayyata kece wadda nake mafarkin samun natsuwa da aurenmu don Allah ki agaza min ki ji tausayina ki share min hawayen idanuna ki wanke min zuciyata daga dattin dake kewaye da ita Princess don darajar Allah kar da ki barni na lalace ki ji tausan yarana iyayena don Allah Princess." Bata da yanda zatai da shi ta amsa mai har cikin zuciyarta tana sonsa, saboda samun wanda zai maka soyayya irin wannan tabbas ya cika masoyi haka yasan me yake kuma ba son yaudara ko arya yake maka ba. Don haka tai ajiyar zuciya ta dube shi tace, "Kai min al awarin cewa zaka sauya daga duk wani halin rashin kirki naka, haka zalika zaka zama mai min adalci tsakanina da matanka, sai magana ta arshe ba zan zauna da matanka ba, zaka aje Ni gidana daban kai min alfarmar zama gidana har abada ba tare daka ha a Ni da matanka ba, to tabbas zan aure ka idan kuma zaka cigaba da nuna min soyayya tamkar yadda kake nuna min ita a yanzu domin soyayya a jinina take ban jin da in zaman aure babu soyayya ba zan iya juriya ba a wannan lokacin zan iya sake waje kan rashin kulawa." Rumgume ta ya yi yana saukar da ajiyar zuciya, natsuwa na ratsa shi ta ko'ina, ji yake ya samu natsuwa da kwanciyar hankali mai orewa tunda Jiddah ta amince da soyayyarsa. Cikin farin ciki yake ce mata, "Na gode sosai Princess insha Allah zan cika maki dukkan wani burinki zan zama mai share maki hawayenki, ba makawa al awarinki zai zama abin ri e wa gareni har abada." A hankali ta zare jikinta daga nashi tana jin tamkar ta sauke wani babban nauyi da ya danne mata zuciya, sai ta ji duk wata damuwa ta fice daga cikin zuciyarta. Zaman dirshan ya yi gabanta yana are mata kallo cikin zuciyarsa yana gode wa Allah daya azurta shi da samun mace kamar Jiddah matsayin matar aure. Ita ma kallonshi take asan ido tana ganin yadda yake da kyau na daban komi na shi ya yi mata, ga shi an gayu ko da yaushe amshin turarensa ke bayyana zuwansa waje tun kafin ya zo wajen, gayunsa na birgeta tana son miji an gayu wanda ko da yaushe yake cikin tsabta da amshi kamar dai yadda Mustapha ya kasance. Hancinsa ta kalla yana da dogon hanci wanda ya fi nata sosai tsawo, ga shi da idanu masu kyau fuskarsa Masha Allah komai ya yi mata yadda take bu ata. Babban abin da ya sake tafiya da hankalinta wushiryarshi babba mai ara mai kyau idan yana dariya, ita kanta sautin dariyarsa abin tsayawa ce a ranta, murmushinsa na matu ar birgeta tabbas ita ma tana sonsa ba yanzu bane ta fara sonsa ba kawai dai bata maida hankali bane da ta gane ita ma ta kamu da sonsa. Sai ga su suna ta tsokanar juna kowa na jan kowa, suna ta dariya tamkar ba sune ba suke kuka yanzu ba cikin damuwa da tashin hankali ba. Mustapha ya dube ta ya ce, "Princess wai ya naga sai wani kallona kike ne hala kin ga an mummuna ne." Tai dariya sosai tace, "Anya kuwa an ta a gaya ma kana da kyau kuwa Prince?" Yana murmushi ya ce mata, "Kawai dai ki ce min kin lura da muni na kawai Malama." Tana murmushi tace, "Kasan wani abu kuwa