← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 133

Sashe 111

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Dr. Faisal ya sake jin karaya a zuciyarsa yadda sam yanzu Alawiyya bata auki abin da muhimmanci ba. Ko da yake yasan yadda take daman bata da sau i ya yi mamakin yadda ma ta daure ta nuna mai bata fahimci komai ba tun farkon lamarin har kuma ya dinga sauka kan layi tana biye da shi ba alamar rashin fahimta yasan da gaske take a lokacin daya samu sa'ar auren Jiddah da ya gama hayewa amma yanzu don ba in bu ulu bai samu Jiddah ba ita kuma tana gara shi tamkar wata garaya ko waina a tanda. Baffa ne ya shigo ya iske shi zaune ya ha a kai da gwiwa suka gaisa ya wuce ba tare da ya tanka kan abin da ya kawo shi gidan ba. Yana cikin yanayin ne Baffan ya sake fitowa har ya sauya kaya zuwa marassa nauyi ya zauna ya kira sunansa ya ce, "Faisal daman ina son ganinka kiranka ne kawai ban yi ba. To masha Allah tunda ga ka ai shike nan. Daman abin da nake so da kai shi ne ka fita sabgar Jiddah domin ba aurenka zatai ba, da kanta ta tabbatar min da cewa karatu za tai don haka kar da ka sake kiranta da sunan soyayya na yanke ala ar hakan a tsakaninku." Zufa ta yanko mai ta ko'ina yana jin tashin hankali nayi mai sallama. Kenan ba mai iya daidaita tsakaninsa da matarsa kowa ya kawo ido ya saka masu duk abin da take ba mai iya yi mata magana ta daina? Gaskiya ba ai mai adalci ba sam. Baffa ya tashi ya shige aki yana yi mai Allah Ya kiyaye hanya idan ya tafi zai kwanta ne shi. Alawiyya ta dubi Jiddah sosai tace, "Me yasa naga duk kin damu ne daga wannan abin? Ko dai kina jinsa ne a zuciyarki daga zuwansa?" Jiddah tai ajiyar zuciya tace, "Wallahi ban san ya akai ba kawai naji gabana na fa uwa haka kawai sai nake hango fuskar Prince cikin damuwa." Wayarta tai haske sai ga pic inta da Prince suna murmushi wani sansanyar ki an India na fitowa. Kasa aga kiran tai, sai da Alawiyya ta aga kiran ta mi a mata wayar sannan ta amsa cikin sanyin murya ta ambaci sunansa. Shima kamar ha in baki ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Wallahi Princess tun azun gabana ke fa uwa duk na rasa me ke damuna ban jin farin ciki ban jin da i don haka na kira ki ko naji farin ciki domin nasan ko kuka nake idan naji muryarki sai dariyar farin ciki ta maye gurbin kukan." Bakinta ya yi mata nauyi ta kasa ko da furta kalma guda. "Princess ko dai na zo ne? Wallahi baki ji yadda nake ji ba, ina cikin matu ar damuwa kuma ban san miye dalilinta ba sam." "Ba sai ka zo ba, ka yawaita karanta innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, zaka ji ka daidaita Prince." Tana furucin ne yayin da hawaye ke zubowa daga fuskarta. "To amma Princess ji nake tamkar ke ma kina cikin damuwar ai, don Allah me ke faruwa da ke ne? Tabbas akwai abin da akai wanda ba zai mana da i ba don Allah miye ya faru ne?" Magana yake da muryarsa kamar ta mai kukan shima. Cikin dakewa tace, "Ba abin da ya faru Prince, ba kana gun aiki ba? Don Allah ka dage kai aikinka ban da wasa da ja masu hankali don Allah na san halinka fa." Tana jin sautin ajiyar zuciyarsa irin hankalinsa ya fara kwanciya in nan ya ce mata, "To ki yi min." Dariya tai, Prince akwai rigima duk lokacin da su kai waya idan bata ce mai Love You ba ya ce mata love you too ba sai ya yi mata tsogumi ya ce ta i yi mai, tsabar abu har kiss yake cewa sai ta hura mai ta wayar ya ji haka suke ko da yaushe idan suka gama waya sai sun yi ma juna. Yau kau bata jin zata iya ce mai hakan balle har ta hura mai wani kiss. "Ni, Ni, Ni, dai ki yi min nace." Da muryar shagwa a ya furta hakan. Dole ba don tana jin son yi ba tai mai, don dai kawai su rabu lafiya. Alawiyya ta mi e ta fice daga akin saboda yadda mijinta ke ta kiranta. Duk da ya fara bata tausai sai ta share tai kamar bata ma ga yadda ya yi tsugunne ba ga damuwa fal a ransa ta samu waje ta kame ta watsa mai ido alamar tana jinsa. Komai ya kwance mai ya rasa ta ina zai ke o ta don haka ya tashi da sauri ya rungume ta ya fashe da kuka yana cewa, "Bai kamata ba don kowa ya yale Ni kema ace kin yale Ni ba matata, saboda ke ce farin cikina haka ke ce natsuwata don Allah ki daina azabtar da Ni da wannan mummunan hukuncin naki wanda zai iya nakasar da zuciyata." Kuka yake sosai yana ara shigar da ita cikin jikinsa. Lub tai a jikinsa tana jin yadda yake zuba mata kalaman soyayya masu da i da sanyaya zuciya wanda rabon da ya furta mata kalma guda ta soyayya har ta manta. Sai da ta tabbatar da cewar ya yi laushi sosai sannan ita ma ta rungume shi jikinta tana cewa cikin sanyin murya, "Haba mijina abin tun ahon rayuwata, mai dasa min natsuwa da kauda min tashin hankali, me yasa ka za i raba tsakanina da wadda ban da kamar a fa in duniyar nan? Me yasa ka manta yadda na mutu kan aunarka nake biye da sonka lungu da sa o ne don kawai na tabbatar da cewa nayi kane-kane na hana idanunka da zuciyarka hangen wata iya mace bayan Ni? Don Allah ka daina razana zuciyata ta hanyar nuna kulawar soyayya ga wata mace bayan Ni mijina." Yana kwance jikinta tana wasa da sumar kansa ya ce, "Nayi maki al awarin ba zan sake tada maki hankali ba haka ba zan sake kallon Jiddah da kallon soyayya ba har abada insha Allah zan auke ta tamkar wadda kuka fito Uwa aya Uba aya insha Allah." Sai ga su sun baje suna ta fira kamar ba su ba, har ta tashi ta shige akin da take ta ha a mai ruwan wanka ta ja shi suka shige don ya yi wanka ya samu natsuwa. Jiddah kuwa tana gama waya da Prince sai tai murmushi domin ta lura duk lokacin da waninsu ke cikin damuwa sai gudan ya ji a jikinsa shima ya kasance a damuwar. Ba zata manta ba wata rana da wani ya biyo ta ya dame ta har dai ta gaji ta tsaya kasancewar tana tafiya ne a asa. Sun gaisa sama-sama ya gabatar mata da kansa da sunansa Jameel da sana'arsa ta saida zinari da azurfa a nan Kadunar yana da mata guda da yara biyu mace da namiji. Ba yadda bai ba ta shiga motarsa ya kaita gida ta i don haka ya amshi lambarta da al awarin zai kira ta tai mai kwatancen gidansu don da gaske yake ya ga mata shi a karo na biyu rayuwarsa bayan matarsa ta gida. Suna rabuwa da Jameel wayar Prince ta shigo wayarta tana agawa ya ce mata, "Princess gabana ke ta fa uwa sosai ina jin kamar wani abu ne zai faru da ke ko Ni marar da i don haka na kira ki naji ko kina lafiya?" Kamar ta bayyana mai abin da ke faruwa sai kuma ta share tace ba komai ya dinga Salati kawai daman haka ne wani lokacin ana jin irin hakan. Haka ma akwai lokacin da ta sake ha uwa da wani Abdul shi ma suna rabuwa ya kira ta hankali tashe yana gaya mata yadda yake jin damuwa da fa uwar gaba na addabarsa. Hawwa'u (Iyami) ta shigo akin tace " iyata ana kiranki bakin gate in ji maigadi yanzu." Sai da tai jim, domin dai tasan ba wanda su kai zai ganta a Yau koma tace yanzu amma sai ta share tunanin tace, "To ace mai ina zuwa ya shigo da shi cikin harabar gidan a ba shi ruwa kafin na fita." Hawwa'u (Iyami) ta fice tana murmushin yadda kowace rana sai Jiddah ta samu aukaka daga ko'ina kamar ba ita ce ta sha ba ar wahala ba a rayuwarta ba, ko da yake Malam ya gaya mata daman haka rayuwar take idan ka sha wahala da fari ka zo daga baya ka sha da i, to ita dai yanzu da in ne take sha har ya so yafi na Alawiyya ma, tunda ita a sake take ga maza nan birjik kowane so yake ya samu shiga gunta don haka sai banko alheri suke mata ta ko'ina tamkar babu talauci a duniyar ma baki aya idan akai mata wata kyautar, don ma ta kasance ar halak tana matu ar kula da danginta da mahaifiyarta bakin gwargwado. Yana zaune sai waige-waige yake tamkar ace arr ya ruga. Kallo guda za kai mai ka tabbatar da cewa duniya tai mai juyin taliyar Hausa da taji wuta. Ya jeme ya rame ya fice hayyacinsa kayansa duk sun yage da ganinsa yasan inda talauci ke kwana yake tashi ko ace ma shi ne talaucin don basu da mara ba. Sauke kansa asa ya yi lokacin da aka sauke mai ruwa mai sanyi da lemu tare da kayan tsotse-tsotse aka ce tace ya fara sha kafin ta fito yanzu. Ke duniya ina za ki damu ne? Yanzu nan Jiddah ke rayuwa a wannan gidan mai kama da aljannar duniya? Yanzu nan Jiddah ce a jikin jaridu da gidajen rediyo ake magana kanta?" Shi ne tunanin da ba on ke yi yana kallon kayan gabansa hawaye na zubowa daga idonsa. Cike da natsuwa ta nufi inda tasa a sauke ba on nata, ko a ranta bata kawo komai ba har ta isa inda yake ta ja kujera tai sallama ta zauna. A firgice ya ago kansa ya kalleta sai kuma ya mi e tsaye sai
Chapter 111 · 0% Book details