← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 133

Sashe 42

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

shima amma babu idanu sam bata gani. Kuka sosai kowa ke yi gun, abin da yasa Gandurobar da ta kawo Fatima le awa, hantar cikinta ta ka a ganin yadda Madam da kanta ke kuka ta rungume matar ga wani Alhaji dake tsaye yana share hawaye da gani shi ma mai fa a aji ne a asar baki aya. Sun jima a hakan sannan Faisal ya auko darduma mai girma ya shimfi a kowa ya zauna. Ba aramin tashin hankali suka shiga ba, lokacin da suka ga Mamar Alawiyya na lalube lokacin da zata zauna,alamar bata gani ta makance. "Fatima yaushe kika daina gani?" Cewar Daddyn Alawiyya yana share hawaye. "Labarin mai tsawo ne Baban Alawiyya, amma waye ya baku labarin ina nan?" "Cikin talabijin muka ga sanarwar abin da ya faru Fatima." Cewar Daddyn Alawiyya karo na biyu. Alawiyya kuwa har ta fara nazari matsayinta Na lauyan da tasan abin da take yi, taya makauniya zata kashe mijinta? Cikin sauri ta mi e tsaye ta kalli Daddynta tace, "Daddy bari na je na amshi file in case in naga yadda aka yi kisan." "To iyar kirki sai kin dawo." Cewar Daddyn Alawiyya, Faisal kuwa ya tashi ya bi bayanta, domin duk inda zata je indai bai aiki to tare yake tafiya da matarsa domin ya bata kariya, duk da ko da yaushe cikin addu'ar mutane data iyaye take. Har babban Ofishin ta je, ta amshi File in ta koma cikin mota ta fara karanta wa. "Fatima ta kashe mijinta mai suna Captain Aliyu Masani ta hanyar yanka shi a wuya, sannan kuma ta caka mai wu a a ciki har sai da rai ya yi halinsa." Gwauran numfashi ta ja, kafin ta sake nazarin zancen. Taya makauniya zata yanka mutum har kuma ta caka mai wu a? A yadda taga hoton marigayin yana suffar sadaukantaka, kuma yafi wadda ta kashe shi karfi ko a kallon jiki nesa ba kusa ba... Wayarta ce tai ara, ganin ba uwar lamba kamar ba zata auka ba, amma ganin wayarta ce ta wajen aiki sai ta aga kiran. "Ina magana da Barista Alawiyya Bello ne?" Ba tare da wani jinkiri ba ta amsa da cewar, "Tabbas kana magana da ita ne, wane taimako zan maka?" Wata mahaukaciyar dariya aka saki wadda sai ta kauda wayar daga dodon kunnenta, ya yi mai isarta sannan ya ce, "Ina son ki yi gaggawar ficewa daga case in da kika amsa na Fatima da ta kashe mijinta, idan ba haka ba za ki fuskanci alubale wanda baki ta a cin karo da shi ba ko a mafarki. Ki sani idan ta amarki taurin kai to kin zo madakata, domin kin zo fagen da taurin kai bai amfani asalima bai da waje a gurinmu." Kit ya kashe wayar. Wani malalacin murmushi ta saki, tabbas shari'ar irin wadda take so ce, ta jima batai Shari'a irin wannan ba mai cike da wasa da fa walwa ba. Wani ma ya yi rawa balle an maka Tabbas sai ta banka o asalin mashe in Marigayin indai ta cika ita in ita ce Barista Alawiyya wadda mutane ke jinjina wa baiwa da haza ar da take da ita wajen nuna warewa a aikinta. Faisal da duk ya ji abin da ya faru a wayar sai tsoro ya kama shi, cikin damuwa ya dube ta ya ce, Hubby akwai matsala kuwa a wannan lokacin, domin ga dukkan alama akwai mutane na daban dake auke da alhakin aukar mataki kan duk wanda ya shiga cikin shari'ar... "Dakata Faisal! Kana nufin saboda wasu ananan an daba da basu san abin da ake kira da Shari'a ba zan yi zaune na kame kaina da bakina tare da aikina na bar mahaifiyata a cikin wannan yanayin? To wallahi tallahi indai ina raye sai na buga Shari'a mai cike da abubuwan al'ajabi da mamaki kai wallahi sai na nuna wa ko su waye cewa sun ta o tsulayar Dodo, ba zan rangwanta ba, haka ba zan sassauta ba, sai na gurfanar da masu laifin gaban hukuma, sannan na nemi kadin ha inta na ata mata suna da akai ba zan gushe ba sai na yi lalalar da zan hamba e duk wanda ya yi ma mahaifiyata karan tsaye a rayuwarta ba zan asa a gwiwa ba sai na tabbatar da cewa ko kare ne ya ta a yi ma mahaifiya ta kukan da bai mata ba sai na nema mata ha inta balle mutum mai auke da afafuwa da hannuwa ha ora talatin da an kai a bakinsa." Zuwa yanzu tantama yake anya kuwa matarsa ce Alawiyya da ya sani macen da bata aga murya gabansa, macen da bata ta a kiran sunansa amma Yau ga shi har tsawa take mai mai cike da firgitarwa. Dole ya kama kansa kafin ya yi abin da zai ata ran matarsa a banza. Can gun ta koma amma sai ka tabbatar mata da cewa lokacin ganawa da Mamar ya wuce sai dai su dawo gobe. Haka suka taho suka bar Mamar a yanayi na ban tausayi. Gidan Alawiyya dake Kaduna suka sauka a nan NDC unguwar Kaji bayan gidan IBB, ko da suka je kowa ba wanda ya kula kowa daga Daddyn har su, da ya yi nufin zuwa ya kama hotel ko cikin gidajensa ya kwana sai Alawiyya tace kar da ya je ko'ina akwai matsala a lamarin. Haka yasa aka ba shi aki guda ya shige shima yana nazari da tunanin wace irin rayuwa Fatima ta yi bayan rabuwarsu. Alawiyya kuwa sallah tai ta gama ta zauna kenan zata fara bincike kan lamarin wayarta tai ara cike da gamsuwa da kanta ta auki wayar. "Watau ke baki jin kashedi ko? Ina son ki sani idan dai kikai gaggawar binciko gaskiya kamar yadda kika saba to wannan gaskiyar za ki binciko ta ne da tukuicin ran mahaifinki da mijinki." Kamar yana gabanta haka ta daka mai tsawar gaske tace, "Anya kuwa kasan wacece Alawiyya a duniyar Shari'a kuwa? Ina so ka sani ban jin nisha i sai ina sauraran wa annan banzajen maganganun naku masu sakamun nisha i a zuciya, kada ka sake ka sake kirana idan dai ba albishir in ka kama mijin nawa ko uban nawa ka kira kai min ba. Amma ina son ka sani nan da kwana ka an zan binciko duk wani sirri da kaidin abin da kuka aikata." Kit ta kashe wayarta ta fa a kan gado tana tunanin Mamarta. To masu karatu abin ya auko zafi fa. Alawiyya ta ga mahaifiyarta amma da laifin kisan kai. Wace irin rayuwa Alawiyya tai bayan rabuwarta da Jiddah? Ya Mustapha yake ciki da gidansa? Ina Jiddah take da halin da take ciki? Ku dai kar ku damu ku ci-gaba da bibiyar al alamin Haupha don jin wannan cakwakiyar gaske data kunne kai. Taku a kullum Haupha [8/10, 8:23 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa
Chapter 42 · 0% Book details