Sashe 45
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *Happy 5 years anniversary Kainuwa Writer's association* Page 27 Barista Alawiyya ce dubi Daddy da Dr. Faisal tace, "Kuma an ja maku kunne ne? Anyi maku albashir da ajalinku idan baku saka baki na janye daga niyyyata ba halan?" Daddy ne ya fara bata amsa, "Ta ya kika san me aka gayamin haka Alawiyya? Tabbas sun ce min ko dai nasa ki janye ko kuma na rasa raina na rasa ki baki aya kuma tabbas Fatima sai ta mutu." Kallon Dr. Faisal tayi ba tare da tace komai ba, amma shi da yake yasan halin an kayansa sai ya bata labarin abin da take son ji kawai. "Sun tabbatar min da cewa zan rasa ki kamar yadda zan rasa yarana tare da Ni kaina a banza idan ban sa kin janye daga shari'ar nan ba." Fatima ta sake fashewa da kuka tace, "Kinga abin da nake gaya maki ko? Tabbas ba za su bar ku ba, basu da imani sun yi aurin suna wajen tarwatsa rayuwar mutanen da basu ji ba, haka basu gani ba, don haka don Allah ku yi ha uri ku manta da Ni tunda daman mun manta da Ni ku saka a ranku cewar ban duniyar baki aya daman, don Allah ku yi min alfarmar barina a nan ku je." "Wallahi ba zai yiyu ba, sam hakan ba zai faru ba ko a mafarki ba zan iya juya maki baya ba Fatima balle a ido biyu, kin san iyakar shekarun da na auka ina jiran wannan damar ta sake ganinki? Shi ne don na cika marar rabo wanda bai san darajar soyayya ba sai na yale ki? To tabbas ki saka a ranki idan mutuwa za ki yi to tare da Ni za ki mutu Fatima." Cewar Daddy kenan yana zubar da hawaye. "Tabbas ka cika miji na gari abin koyi ga dukkan maza, ina bayanka nima zan bi dare, rana, don tabbatar da cewa mahaifiyata tana cikin natsuwa ta manta komai ta koma cikin farin ciki na wanke ta daga duk wani ba in fenti da akai mata a idon duniya, nasa duniya ta karramata ta bata KAMBUN YABO." "Ashsha! Anya kuwa kin san su waye Hajiya Turai da Hajiya Tani ar nan?" To su in manyan tantirai ne masu ta ama da ku i da tsafi." A Yau bari na baku labarin asalin abin da ke faruwa ko kun yadda da maganata, ku yi ma kanku karatun ta natsu ku cire hannu daga lamarina, saboda na riga na shiga tarkon matan zamani masu gadara da ku i masu ta ama da shirka wa anda basu auki aikata zunubi wani abin tur ba. LABARIN FATIMA "Lokacin da Bello ya zo neman aurena, ban amince ba, saboda ban son nayi nesa da yarinyata da Inna, saboda nasan duk duniya su ka aine dangina ahalina kuma, sannan har ga Allah ina tare da son mijina Baban Alawiyya duk da ina ji a jikina danginsa ba zasu ta a amincewa ya aure Ni ba haka ba zasu yadda da amsar Alawiyya ba matsayin jininsu ba yasa na yanke shawarar zama ba aure na fi amincema na zame ma Alawiyya Uwa kuma Uba ban san a wayi gari tai kukan rashin Uba don haka na i amincewa da maganar aure ga duk wanda zai zo guna da sunan neman aurena. Sai dai zuwan Aliyu yasa mutane fara gulmace-gulmace ana cewa na aje soja cikin gidanmu na i aure, wasu marassa tsoron Allah ma suka fara cewa ita ma Alawiyya a haka na same ta, wannan maganganun ne suka saka Inna tai min magana kan na yi ha uri na fitar da wanda nake so kawai yafi mutunci kuma hakan zai dakushe wancan ba in suna da ake son dinga kiranki da shi na marar Uba. Hakan yasa na amince da Aliyu domin ya yi min al awarin zai aje nan nan garin ba inda zai kai ni, ya tabbatar min da cewa bai da kowa sai Ni, don haka na ji na amince da shi domin ban san na sake yin na aurena da Babanki , rana guda danginsa suka zo suka rabamu har ma suka aukar iyarsa suka ce basu auke ta matsayin danginsu. Cikin lokaci ka an akai aurena da Aliyu Soja ya kama mana haya a Tabkin fili muka tare, ya ce na tafi da yarinyata amma nace a'a saboda har ga Allah ban san iyata tai agolanci wani gida nasan Babanta ba zai murna da hakan ba. Cikin ikon Allah Aliyu na kulawa da Ni yadda ya kamata, sai dai har zuwa lokacin ina danne zuciyata ne kawai amma Babanki ya i barin zuciyata. Kwatsam! Bayan wata shida da aurenmu wata rana Aliyu ya fita ya dawo da alamar damuwa, nai tambayar duniyar nan amma sai ya ce min ba komai kawai. A haka muka tafi da shi har kwana uku sai a na hu u ne ya kira ni bayan ya dawo da rana, ya dube ni ya ce, "Fatima don Allah ki yi ha uri ki yafe min duk abin da ya faru, wallahi ba laifina bane ba, na riga nayi bincike sosai kanki na fahimci cewar idan na gaya maki gaskiyar koni wanene to ba za ki aure ni ba, Ni kuma har ga Allah kece irin macen da nake mafarkin aure, hakan yasa nayi maki aryar cewa Ni an nan garin ne amma ba haka bane ba, Ni an asalin garin Kaduna ne a unguwar tabkin Malamai nake zaune sannan Ni in babba ne a cikin aikina domin saura shekara biyu nayi ritaya, ina da matan aure biyu Hajiya Turai da Hajiya Tani, duk a gidana suka je Makkah insha Allah ke ma zan biya maki sai mu je tare daman ina son na sake zuwa. Shekaru da dama nayi aure amma Allah bai ta a ban haihuwa ba na nema har na gaji na fawwala Allah lamarinsa nasan dai shi ne mai badawa haka kuma shi ne mai hanawa. Don Allah ki yi min alfarma ki yi ha uri ki bini Kaduna na amince ki tafi da Inna da Alawiyya tunda dama na gaya maki ban ta a haihuwa ba Ni kinga sai Alawiyya ta ebe min kewar yara a gidana don Allah Fatima." Jikina baki aya ya yi sanyi, tabbas da ya gaya min cewar yana da mata kuma yana da tarin dukiya ba zan aure shi ba, gwara na auri daidai Ni talaka, ina Ni ina zama cikin manyan Hajiyoyi?" "Fatima don Allah karda ki tada hankalinki kan wannan maganar wallahi na rantse da Allah zan kula da ke yadda ya kamata ba zan ta a barinki ki yi kuka ba a rayuwarki insha Allah ki ban amanarki zan ri e maki ita da hannu biyu insha Allah." Ya zan yi? Aure ya wuce komai sannan ya wuce ai wasa da shi don haka na shirya na je na gayama Inna komai. Ita ma jikinta ya yi sanyi kan lamarin amma haka tai ta ban warin gwiwa, haka na sake bata amanarki na taho cike da tashin hankali lokacin kina makaranta haka na je ta can na tsaya ina hangen ki ke da awarki Jiddah iyar Iyami mai abinci. Ba aramin kuka nayi ba da zamu tafi amma haka na dangana muka tafi ta kan jirgi, duk da cewar Ni ma asalina ba matsiyaciya bace haka nake Makkah sai da na zama kamar wata auye saboda an kwana biyu ba a gamu ba. Lokacin da muka sauka filin jirgin Kaduna, nayi mamakin manyan motocin da suka zo tarbar mu,kai tsaye wani babban gida muka nufa wanda ya tuna mun asalin gidanmu da asarmu, har hawaye suka zubo min, na share ina hasko fuskar iyayena da Yayyena. Sashe uku ne cikin gidan, kai tsaye duk inda ya taka afarsa nan nake aje tawa, cikin wani babban falo naga mun shiga ga an aiki nan cike da gun sai kai kawowa suke, kujera ya nuna min na zauna cikin natsuwa da fargaba cike da zuciyata, damuwa shimfi e a kan fuskata. Nan da nan aka cika min gabana da kayan ciye-ciye, Ni dai kaina asa na kasa ko aga kaina balle na samu sukunin cin abin da ke gabana. Ya jima zuwa can sai naga ya fito ta wata ofa wadda ba ta ita ce ya shiga ba, bai jima da fitowa ba ya zauna sai ga wata dakekiyar mata ta fito ta wata ofa ta ci uwar kwalliya sai taunar cingam take tana hura hanci, ko ban tambaya ba nasan cewa ranta a ace yake yadda ta watsa min wani mummunan kallo ta hakimce kan kujera ta turo kallabinta gaban goshi. Ina cikin satar kallonta ne wata ofar ta bu e sai ga wata Hajiyar ita ma, ba arya ta ci kwalliya sosai kamar ta so tafi ta farkonma. Su duka suka tsare ni da idanu wanda ba alamar fara'a a kan fuskarsu. Maigidan ne ya fara magana bayan ya yi gyaran murya. "Alhamdulillah! Na ji da i da na dawo na iske ku lafiya kamar yadda na barku lafiya. To cikin ikon Allah kamar yadda ba kira kowace daga cikinku na gaya mata zan ara aure kafin na ara in, da na ara kuma na kira kowacce na gaya mata na ara aure, to Yau ga matar da na auro daga Lagos mai suna Fatima... "Ahayye warrr." Abin da suka ha a baki suka ambata kenan. "To wallahi bari ka ji Alh. Baka isa ba ka kwaso mana rainon Lagos,zaman asan gada ba a cikin gidanmu ba." Cewar wadda ta fara shigowa kenan. "Ai Hajiya ke kika tanka ma har aka ji ta bakinki, Ni kam ai sai dai a gani a aikace." Cewar wadda ta zo daga baya kenan. Ya girgiza kai ya ce, "Ban san abin da kuke gaskiya, ya kamata ace kun ara hankali kan wanda gare ku, saboda ku ba yara bane ba, na gaji da yadda kullum gidan nan ba zaman lafiya, sai kace na ha a musulma da kafura haba! "Warrrrr! Ahayyye Warrr." Tare suka sake ha a baki