Sashe 54
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 30 JIDDAH Tun da ta dawo daga Kano gun rasuwar Uncle Salim sai ta sake komawa miskilar gaske, bata damu da kowa ba, bata magana, ranar da ta dawo ta sauka gun Mamarta sai dai da kanta taga dacewar ta matsa daga gun Mamar saboda yadda ita ma Mamar take zaune ba da i hakan yasa ta yanke shawarar barma Mama Haidar tun da bata da yaro arami gabanta, ita kuma ta tattara kayanta ta nufi gidan mahaifinta, sai dai gidan a rufe yake ga alama kuma ya jima da rufewa don haka ta nufi asalin gidansu mahaifinta kanta tsaye duk da tana jin fa uwar gaba amma sai ta dake ta nufi can, tana zuwa da sallamarta ba kowa tsakar gidan don haka ta nufi akin Kakarta. Tana zaune ga alama sallah ta gama, Jiddah ta gaidata ta amsa ba yabo ba fallasa bata damu ba tasan daman hakan zai faru don haka ta share ta kai kayanta ta ajiye ta dawo ta kalli Kakar tace, "Kaka naje gidan Babana naga ba kowa ko sun tashi daga gidan ne?" Kamar ta kai mata duka haka ta watsa mata kallo sannan ta ce, "Ban sani ba, nace ban sani ba, kema shegiyar gulmar ce ta taso ki daga gidanki kika zo ki ka tasani gaba da tambaya? To ya saida abin shi ya ara gaba inda babu jin zafi sai wace uwar tsiyar kuma?" "Kaka ina matarsa to?" Cewar Jiddah. "Ban sani ba, wai ke Ni abiyar ki ce Ni da za ki zo ki tasani gaba da tambayoyi? To ya sake ta ai shi tun da Allah Yasa ya auri uwarki da farko shi ke nan komai ya ta are mai ya kasa samun macen kirki da arzi i har yanzu. Shi yasa ake son ka auri mace ta gari da farko sai ka ga kana ta dace dana kirki daga baya." Cewar Kaka tana maka ma Jiddah harara. Jiddah tai murmushi tace, "To dama Deeni ne ya sake Ni don haka na nufi can tun da bai nan zama nan ya kamani kenan." Kakar ta zaburo tace, "Gidan Uban wa za ki zauna in? To tun wuri ma ki san inda dare ya yi maki ba inda za ki zauna a nan atoh na gaya maki ma, haka kawai ki zo gaki ga yara to waye zai auki nauyinku? To ban iyawa tun kafin ma dare ya yi ki sake mafaka wannan ba tai ba." Jiddah ta dubi Kakarta fuska cike da hawaye tace, "Ban ce wani ya auki nauyina ko nauyin yarana ba, kawai wajen kwana za a ban shike nan amma Ni zan ci da kaina da yarana insha Allah Kaka." "To wannan fa, yanzu ki kai magana indan wajen kwana ne akwai akuna sai ki fita ki za i guda ki share ki zauna ban hana ba." Duk da taji ciwon abin amma ta ji da in yadda Kakar ta bata damar zama a gidan, don haka tai godiya ta mi e ta je ta duba akunan ta za i wanda ya yi mata ta share shi tsab ta auko kayanta ta saka ta fice ta je ta fitar da ku i ta sai leda da katifa da labule ta dawo ta saka a akin. Fahimtar su Afnah sun fara jin yunwa yasa ta sake fita ta siyo masu abinci ta dawo suka ci tare ta bar su a akin ta sake fita ta siyo duk abin da tasan tana da bu ata ta ha o da kayan tea da sauran kayan abinci ta siyo kwa o ta dawo. Nan da nan ta kammala akinta tsab ta ebi ruwa tai masu wanka ita ma tai wankan ta tura akin su kai ta wasa da dariya da yaranta tana jin damuwarta na raguwa. Mama ta kira ta gaya mata duk abin da ya faru, tace Allah Ya kyauta kawai don bata da abin cewa kan lamarin. Cikin sati guda Jiddah ta saba da zama gidan Kakarta duk da cewa zaman aki yafi mata da i kan zama kusa da mutanen gidan don yanzu sun fara gaya mata magana wadda za tai mata ciwo. arin jin da in ta yadda su Afnah basu bata ciwon kai sam, har ta kai su makarantar boko dake ha e da islamiyya suna zuwa kullum hankalinta kwance, kawai ko da yaushe takan tanadar masu abinci ne da sun dawo su ci su yi ta wasa cikin aki. Kwatsam! Hutun semester ya are don haka ta tarkata su ka maida ma Mama su da kayan abincinsu ta harha a ta koma makaranta cike da burin yin karatu. Da ta dawo sai ta sauka ta can ta auki yaranta su wuto gida. Maza da dama na damunta da maganar aure amma ita ko a Film taga aure bai burgeta balle a gaske, ita ba abin da ke burgeta irin karatunta sai kuwa kasuwancin da ta fara na saida kayan aki da sauran tarkacen mata na sawa, kuma masha Allah tana samun ciniki sosai a makarantar yadda ya kamata. Hutun aji biyu ta samu don haka ta shirya ta nufi Kano don ko da yaushe Hajjo cikin orafin rashin zuwanta take duk da tana gaya mata karatu take. Ta so warai ta tafi da yaranta amma sai makaranta ta hana don haka ta barsu gun Mama ta shirya ta nufi Kano. Tun da ta shiga motar wani ke kallonta ita ma taga kamar ta san shi amma ta rasa ina ne ta san shi don haka ta share ta fito da wayarta ta fara karanta littafi kawai don hankalinta ya auke daga kallon da mutumin ke mata. "Amma sai naga kamar na sanki ko?" Cewar mutumin dake kallonta. Tai banza da shi tamkar bata ji me yake cewa ba, amma saboda kunya tai mai ka an sai ya janye wayarta daga fuskarta ya sake maimaita tambayarsa. Yamutsa fuska tai kafin tace, "Ban iya ganewa nima." Murmushi ya yi tabbas ya gane yarinyar wadda yake gani ce a school in su, don haka ya ce, "Wace makaranta ki ke ne pls?" Cike da gatse tace "Wadda kake." "Tabbas nasan ke ce daman, ko a school ina arin yi maki magana amma sai ki share ki yi kamar baki san da mutum ba, don Allah ki daina girman kai babu kyau." Kamar ta ja tsaki sai kuma taga rashin dacewar hakan don haka ta kauda kanta kawai, don har zuwa yanzu wayarta na hannunsa ya i bata. Tana ganinsa ya saka lambarsa ya kira a wayarta bata dai tanka mai ba, haka bata nuna ta gane me yake ba, duk tana kula da yadda ya yi saving number da sunansa ta ta e baki ta kauda kanta. Har suka isa Kano yana ta zuba kamar Kanyar da babu da i, tai banza ta yale shi kowa na jin shi yana ta magana ita kuma tai banza da shi kamar bata gun. Suna isa ya bada ku in motar shi da nata ya tsaida mata mai keke napep ya biya shi ku in ya ce ya kaita inda zata je. Yana zaune abin duniya ya dame shi, tabbas yana cikin matsala mai girman gaske bai kamata ba ace cikin mace uku ba bai samu wadda zatai mai abin da yake so ba, ko dai shi ne ke da matsala ba matan ba? Yana son kulawa amma bai samun mai kulawa da shi, kowace kanta da yaranta kawai ta sani shi kam babu mai bu atar ko jin damuwarsa a cikin matan nashi ko da yaushe nadama yake ta auren shi ji yake dama bai da aure tabbas da ba zai yi shi ba... Mai keke napep ya tsaya daidai saitin da yake zaune, kamar kar ya kalla don yaga mace ce zaune a cikin napep in, amma kamar fisgo shi akai kawai yaga Jiddah na niyyar fitowa daga cikin napep in, wani sanyin da i ya ji ya ziyarci zuciyarsa kamar ba shi ne zaune cikin damuwa ba. Hankalinta na kan ta shiga cikin gidan don haka bata ga Mustapha ba da ke ta muimui da baki yana son ya yi mata magana amma ya kasa bu e baki yadda zata ji shi, har ta shige gidan yana bin bayanta da kallo. "Jiddah nada kyau." Ita ce kalmar da ya fa a yana bin bayanta da kallo. Hajjo na zaune tana jiranta don sun yi waya ta iso Kano tun azun, ga kulolin abinci nan gabanta ga alama na tarbar Jiddah ne. Da gudu Jiddah ta fa a jikin Hajjo tana murna kuma sai ta saka kuka, domin ta tuna da Uncle Salim. Hajjo tai ta yi mata dariya tana cewa, "Ba dai a san ar fari da shagwa a ba amma ga wata da rana tsaka an samu Yau." Wayarta tai ara tana dubawa taga awarta ce Bilkisu don haka ta aje wayar don tasan ita ma jiranta take don tasan Yau zata zo Kanon. Abinci ta zuba ta fara ci suna fira da Hajjo tana bata labarin rayuwarta da yadda take zaune gidansu Babanta bata oye mata komai ba. Hajjo ta girgiza kanta tace, "Ki yi ha uri Jiddah wata rana sai labari ko ban da rai sai kin tuna na baki wannan labarin za ki yi farin ciki kuma za ki ba mutane mamaki kowa da kowa zai so ki za ki zama abar kwatance a ko'ina Jiddah insha Allah." Murmushi tai, zatai magana kenan Mustapha ya shigo gidan da sallamarsa. Hajjo ta kalle shi tace, "Idonka kenan ko Mustapha? Sam baka zuwa gidan nan yanzu sai dai naji amshin turarenka kawai ka wuce ko? To ai akwai ha in ma wabtaka idan ka aje na zumuntar." Yana an murmushi yana shafa eya ya zauna ya ce, "Ba haka bane ba Hajjo ina son shigowa kawai dai abubuwa ne ke mun yawa a kwanakin nan." Hajjo ta dube shi ta yamutsa fuska tace, "Ai daman nasan abin da zaka ce kenan idan nayi magana, ai shike nan." Jiddah tai mai kallo guda ta kauda kanta ta bu e baki kenan