← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 133

Sashe 88

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne? Shin Deeni wane lambar yabo ka samu na wula anta matarka da yaranka da kai? Ina so ka sani baka wula anta banza ba, domin Jiddah na da Ni zan iya ha uri idan Ni kai mawa amma ba zan iya ha uri ba idan ita zakai mawa ba. Ka sani dole ne na nuna maka cewar Jiddah tafi kowace macen da kake tarayya da ita anci da gaya ta yadda ko mai irin sunanta ka ji sai ka girmama sunan balle ka ganta. Nasan kana son jin ko Ni wacece ko? To tabbas nasan indai da gaske kai ne Deeni mijin Jiddah ba zaka rasa sanin wacece Alawiyya a gun Jiddah ba wadda su kai rayuwa a Lagos tare ba. Don haka na zo ne don na aukar wa awata kuma ar'uwata fansar abin da kai mata wanda ba zan iya yafe maka ba ko da kuwa hakan zai sa na samu arin matsayi ko tarin dukiya Deeni. Ko da yake kaga yadda Allah Ya maida Jiddah ita da yaranta suna cikin aminci da kiyayewar Ubangiji yadda ya kamata, to bari na yi maka wani albishir in ma, Jiddah yanzu ta zama cikakkiyar Lauya mai zaman kanta wadda ke aiki a cikin babban gari kamar Kaduna, tana baibaye da tarin masoya manyan gaske masu aji da matsayi wa anda suna iya rasa komai nasu indai za su mallake ta. Kamar wasa ta ta a hannunta sai ga wasu majiya arfi sun shigo su kai waje da shi suka saka a bayan mota, tun yana gane tafiya ake har ya daina gane komai saboda yunwa da ishirwa da suka dame shi. Ya yi barci yafi sau tari har barcin ya gagare shi yi ma sannan ya ji motar ta tsaya lokacin da ko hannu bai iya agawa. Sai dai suka auke shi a wula ance suka shiga da shi wani babban gini suka watsa wani aki mai tarin mutane duk maza suka juya. Ashe bisa wani suka jefa shi, suna juyawa ya jefar da shi ya rufe shi da duka yana zaginsa ta Uwa ta Uba, maimakon mutanen akin su raba su ko su shiga tsakaninsu sai ma suka kama ki i da robobin dake hannunsu masu kama dana aljamirai. Sai da mutumin nan ya yi mai lilis sannan ya yale shi ya koma gefe yana ajiyar zuciya. Tun daga lokacin ya fahimci cewar gidan maza ne aka kai shi, kuma wani babban alubale da yake fuskanta ne yadda yadda kowa yafi wani arfi a akin dukan wanda yafi arfi yake, idan aka basu abinci kafin ya gama ci ake amshewa ai ta mai dariya bai da yadda zai yi. Babu irin azabar da bai sha a cikin akin saboda duk akin shi ne raggo bai iya fa a ba cikin tarin an daba aka kai shi masu zaluncin gaske ba tausayi ba imani a ransu ko alama. Ko yanzu da yake zaune yana wannan tunanin ji yake tamkar ya nutse don kunya da nadamar abubuwan daya aikawa Jiddah ganinta yake tamkar bata isa ba, kallon marar galihu yake mata wadda bata da mai tsaya mata a dukkan lamurranta ashe ba haka bane shi ne babban marar galihun da bai da mai tsaya mai kan komai na rayuwarsa. Ko da yaushe cikin tunanin yaushe zai bar gun nan yake ya je ya nemi inda Jiddah take ya bata ha uri, amma bai san lokacin da zai bar wajen ba ga alama dai nan zai mutu ba tare da ya nemi inda yafiyar Jiddah ba. Kuka yake sosai yana arawa cike da jin haushin kansa. Baban Jiddah Tun da yake zaune a cikin gidan yarin nan bai ta a jin kewar yaransa ba sai Yau ga shi ciwo ya yi mai sallama bai lafiya bai da mai kula da shi duk ya kori yaransa bai nuna masu tausayi ba, bai basu kulawa ba haka ya fifita yaran tasha fiye da yaransa. Har ya manta yaushe rabon daya saka ko da yaro guda ne a idonsa, su duka bai san inda suke ba, ba kamar Jiddah ita ce wadda ko mijinta bai ta a sani ba balle gidan aurenta. Jama'a da dama sun sha iske shi su ba shi shawara kan ya nemawa yarinyarsa ancinta a gidan mijinta amma yai biris ya nuna ba abin da ya dame shi sam. Shi a takaice ma ko kalar yaran da ta haifa bai sani ba, hana rantsuwa ranar da ta ta a zuwa daga asibiti ta iske shi da yaranta an biyu data haifa ya ji tace nan zata zauna ya kore ta tun daga ranar bai sake ganinta ba har Yau. Mutane suna yawan ba shi shawara kan yarinyar na cikin matsala amma ko a jikinsa ji yake ita in matsala ce damuwa ce a gunsa wadda ba wata aruwa da zata kawo mai sai dai ta nema gareshi tunda ba cikin ku i take ba, talaka ne mijinta kuma ba ta ita yake ba ma mijin nata. Hakan yasa baki aya ya manta da ita a shafin rayuwarsa. Yau ga shi yana ta ganin inda yara ke da rana, yana ganin yadda yara ke tsayawa kan damuwar iyayensu saboda suma iyayen sun tsaya ma yaran a kan damuwarsu lokacin da suke yara. Kullum akai masu wa'azi sai ya zubar da hawayen nadamar abin da ya aikata ma yaransa, tabbas ya cutar da yaransa iyakar cuta wadda bai san inda zai gansu ba su yafe mai ba, ko da yake ba mamaki ma ba ar wahala ta kashe mai yaran yanzu. Kuka yake sosai kamar ranshi zai fita. Wata tsohuwa da duk lokacin da taga Baban Jiddah na zaune yana kuka ko tunani sai taga kamar ta san shi amma ta rasa inda ta san shi, Yau dai kukan da yake ya yi yawa yasa ta ji tausan shi sosai don haka ta matsa a hankali ta isa inda yake ta zauna kusa da shi tana ba shi ha uri da Hausar da har zuwa yanzu bata gama kame bakinta ba, da jin Hausar ba Bahausa bace ba ita. Ya kalle ta yana kukan ya ce, "Tsohuwa ki bar Ni nayi kuka don na aikata abin kukan ne wanda ko ke kika ji shi sai kin ce na cigaba da kukana domin Ni kuka ya kama ba kowa ba." Tsohuwar ita ma ta rasa ido guda da hannu guda tace, "Ni kam a gani na nice ya dace nayi kuka Ni da na rasa ido guda da hannu guda kuma aka kawo nin gidan yari ake ta ajiya ta, ban da kowa a cikin garin nan, Ni da kake gani nan da can baya a nan nake zaune ina sana'ar saida abinci, ba laifi ina samun ciniki yadda ya kamata saboda ba laifi ina gyara abincina yadda ya kamata. A haka ne Allah Ya ha a Ni da wani bawan Allah wanda ya auki yarinyarsa ya ban amana, na amsar mai yarinya da sunan zan ri e ta amana amma na kasa cika al awarin dana auka na dinga azabtar da yarinyar nan ban duba ga yarintar ta ba, haka na dinga jibga mata aikin wahala ga ban bata abinci ga duka da zagi na safe daban na rana daban, yarinyar nan babu irin wahalar da bata sha ba a guna ba, komai ita ce ke min, hakan bai sa ba na raga mata ba, idan ubanta ya zo na ha a mata sharri ko ganinsa ban bari tayi, daga arshe nasa a raina zan gudu da ita na kaita garinmu can Jahar Yobe inda zan fitar da ita daga addininsu na maida ta cikin addini na na ha a ta aure da yaron anina, yin wannan tunanin yasa na dinga cin ku in yaron na aika da wasi a nace zan kawo wata yarinya ar addinin Musulunci zuwa namu addinin. Hakan yasa aka dinga aiko min da manyan ku e suna cewa nayi aikin lada, sai dai ina cikin hakan ne wata tsohuwa ta kawo min ajiyar jikarta da al awarin zata dawo nan da wani lokaci ka an amma bata ba labarinta don haka da naga ku in da taban na ajiyar yarinyar sun are sai na auki karan tsana na orawa yarinyar tare da wadda aka ban ri o ko da yaushe cikin azabtar da su nake ba ji ba gani. Muna a cikin yanayin ne aka aiko min da cewa mijina zai ara aure a can gida don haka na yanke shawarar tattarawa Ni da yarinyar mu tafi mu bar wadda aka ban ajiya nan tunda wadda ta ban ajiyar ta i dawowa, sai dai a daren ranar yaran nan suka ha e kai suka gudu bayan sun ibar min ku i masu dama, ina cikin tashin hankalin ne kuma sai ga Baban yarinyar da aka ban ajiya ya zo har da Yayansa, muna tsaye kuma sai ga wanda yaban ajiyar yarinya shima ya zo ganin yarinyarsa, in takaice maka labari rasa madafa yasa na yi ma wa ancan arya shi kuma na saka mai maganin barci a lemu nabi dare na gudu na bar Lagos don daman ba wanda yasan daga inda na zo Lagos Ina komawa gida sai kuma fastocin garinmu suka matsamin da tambayar ina yarinyar da nace zan kawo a maidata addininmu? Nace ta gudu suka ce arya nake basu yadda ba, kawai nayi masu damfara ne na amshe masu ku e kuma sai na biya su, daga arshe dai suka wace duk wata kadara ta suka tsiyata Ni sosai kuma suka ce mijina ya ara aurensa. Kasancewar ina kishin gaske yasa muka kasa zaman lafiya a gidan mijina ko da yaushe cikin fa a da dambe muke. Muna cikin wannan rayuwar ne wata rana mukai fa a cikin dare da kishiyata ta ci nasarar caka min tsinken kitso a idona guda ta kuma caka min a tsintsiyar hannuna ni kuma na auki wu a na da a mata a cikinta ta fa i ba rai Ni kuma na gudu cikin daren. Rashin gata yasa nai ta yawo auyuka ina bara har na tara ku in mota na taho Lagos don in cigaba da Bara ta, sai dai lokacin idona ya tsiyaye hannuna ya ru e da taimakon wani bawan Allah ne akai min
Chapter 88 · 0% Book details