← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 133

Sashe 10

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 9 Cikin ikon Allah muna zuwa gidansa, matarsa tai tsalle ta dire tace, "Wallahi ba zan ri e maka yarinya ba, komi zai faru ya faru, haka kawai ka kai yarinya Lagos ban san uwar data koyo ba, da rana tsaka ka kawo min ita wai na ha a ta da Yarona? To wallahi ban ha awa kai duk abin da kaga dama ina jiranka." Da farko ya biye mata suna ta cacar baki abin ba da in kallo balle saurare. Fa a take sosai iyakar arfinta ba zata ri e mai yarinya ba sai dai ya sake ta kan hakan ta amince. Ko da ya fahimci da gaske ba ri e nin zatai ba, sai yace mu tafi gun Mamarsa, ya kaini gunta, muna zuwa itama tace tunda can da nake yarinya arama bai bar mata ba sai yanzu da ta i ka an sai aure zai kwaso yarinya ya kawo mata? To ba za ta amsa ba yasan inda zai kai yarinyarsa tun wuri kafin dare ya yi ma shi... Sallamar wata dattijuwa ce ta tsaida fa an da take, anan na fahimci ashe ita ma Kakata ce ta wajen Uwa, bayan sun gaisa ta dubi Babana tace, "Gunka na zo, don Allah ka rufa min asiri ka sa a saki Hajjo da yaronta kafin sauran yaranta su ji abin da ke faruwa domin idan ta amar tsiya kake a cikin yaranta akwai kwamandan Sojoji, tana da yara masu kakin soja da mopal don haka ita fitina kwance take mai tada ta kuma kanshi take arewa." Mamar Babana tace "To wacece Hajjo kuma miye ha insa da ita?" Sai kawai kuka ya wace min, sai da nace ma Hajjo ta barni gunta ban san ganin kowa sai Mamana itama ba yanzu ba, amma ta matsa sai da ta kawo ni, to ga irin tukuicin da akai mata ai nan. Yana cika yana batsewa yace, "Su ne suka sace min yarinya ashe gunta na ganta don haka nace a rufe min ita sai naji dalilin sace min yarinya da su kai." Su duka suka auki Salati suna nanatawa Kakata ta mi e tsaye ta kakka e zaninta tace, "To ni dai na fita tunda na gayama gaskiya tunda baka ji kuma gaka ga zuri'ar Hajjo nan kai ne a asa wallahi don tana da masu wato mata ha inta, irin masu fushi da fushin .... Bata ida maganar ba aka ji ana a sallama ofar gida, ko da jin sallamar sai Babana ya kalli Mamarsa ya mi e ya fice kamar mu duka aka kira muka bi shi bayansa, muna fita muka ga motar sojoji ofar gidan ga Hajjo cikin aramar mota da Salim ga alama ranta a ace yake, wani soja ya ware hannu zai a wa Babana mari Hajjo tai hanzarin hana shi tace da muryar fa a, "Ka ban mamaki kuma ban ta a tunanin rashin arzi i da rashin darajar naka ya kai har haka ba sai yau. Ina son ka sani ni na wuce kasa a wula anta ni a gun an sanda da ace mu ma ananan mutane ne kamar kai Yau da sai na sa an tafi da kai Kano an koya ma ladabi da sanin girman manya an baka tarbiyya Yaro, amma ka ci darajar yaran dake tsakaninmu da kai bayansu da ka gane Barno Gabas take Yaro, ta. Yayarta ta isa inda take tana bata ha uri ni kuma na nufi gunta ina kukan zan bita, Uncle Salim ya jawo ni zai sani motar Hajjo tace, "Ko bayan raina ban ce ka ri e Jiddah ba Salim tunda ubanta bai da mutunci don haka ka bar mai iyarsa ya ji ata ya shanye ta." Ina ji ina gani Hajjo da Uncle Salim suka tafi suka barni ina kuka ina komai ba wanda ya tausaya min, Babana ya dubi Mamar mahaifiyata ce, "Don Allah Inna ku je da ita zan zo tunda ba wanda zai iya ri e min ita nan." Tabbas dangin Uwa daban ne, bata musa ba, haka ta kama hannuna muka wuce ina waigen mahaifina da mahaifiyarsa data kasa ri e ni. Tabbas zamana gun Inna na ji da i tamkar ina gaban Hajjo komai ana min kuma ina lokaci-lokaci ina gano mahaifiyata, sai a lokacin na goge zargin rashin son da nake tunanin tana min na fahimce ta tana da kawaici da kau da kai sosai akan sha'anin rayuwa bata da yawan magana haka bata cika kulani ba saboda ina iyar fari gunta. Sai a lokacin naga anina shima ya girma Masha Allah ba laifi, ina sonsa don wani lokacin da shi nake tafiya gida. Kwanci tashi aka sakani makarantar boko data islamiyya ina zuwa ban rasa ci ba ban rasa sha ba, sai dai tun daga ranar da Babana ya bada ni yace zai zo bai zo ba haka bai ta a aiko da komai ba yace a ban ko sallah ta zo bai min inki Inna ke min komai. Watarana na je gidan Mamana na iske ta tana goge hawaye na tambayeta lafiya tai shiru sai da mijinta ya shigo yake bata ha uri anan na fahimci mahaifina ne ya zo ya amshe ansa wai zai kai shi makarantar allo. Ni kuma kukan na saka domin nasan yadda wahalar almajirci take, bai kamata ba ace ya kai yaronsa almajirci ba, haka dole muka dangana ni da mahaifiyata muka ha ura da batun anina. Duk garin ban da awa sai wata Safiyya ita ma daga kitso da take min muka ha u shike nan jininmu ya ha u da ita, ina matu ar tausayawa rayuwarta domin tsoho take aure tana yarinya duk da ba fahimtar yadda zaman aure yake nai ba ni dai ina jin tausayin Safiyya don haka komi aka dafa gidanmu sai na kai mata kasancewar mijinta ku in abinci yake bata bai kawo anyen abinci yace ta dafa, to Ni kuma sai na dinga kawo mata safe da rana wani lokacin har dare ina cewa ta dinga adana ku in tana siyen sabulun wanki da wanka, duk da suma idan naga Inna cikin ku i ina matsa mata taban in siyo ma Safiyya sabulu tai wanki, to hakan yasa duk arshen wata idan yaran Inna sun kawo mata sabulu da kayan abinci nake matsa mata tana ban ina kaiwa Safiyya. Mutane da dama sun sha kawo zugar cewa Inna ta raba ni da Safiyya wayau kawai take min, sai Inna tace ba ruwanta tasan ba mai iya shiga tsakanina da Safiyya don haka sai kowa ya yi shiru. Watarana na dawo makaranta naga Inna da Mamarmu da sauran Yayyenta a gidanmu duk cikin damuwa ba mai fara'a sai naga idon Inna kamar kuka take ma, nan da nan hankalina ya tashi na shiga tambayar abin da ke faruwa. Yayan Mamana yace "Jiddah ki yi ha uri komai yake faruwa dake da sanin Ubangiji, kuma insha Allah ba za ki ta e ba, ki ara ha uri kan wanda ki kai a baya, insha Allah za ki yi farin ciki kuma kowa sai ya yi alfahari dake a rayuwa. Jiddah Mahaifiyar mahaifinki ta zo Yau tace angama komai gobe za su aurar dake don haka ki koma gidansu a Yau don gobe akin mijinki za ki kwana, saboda sun gaji da zamanki a nan kuma su basu bada yaransu agolanci tunda an samu mai sonki za su aurar dake ko mahaifinki bai san da auren ba tunda ya tafi yawonsa na Dawa." Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un!!! Ita ce kalmar data fito daga bakina, sai kuma nace "Kawu wane irin aure kuma? Ni wa na sani ma da zan aura?" Sai kawai sauran matan suka saka kuka ina ganin Mamana na share hawaye ta mi e ta auki hijabinta ta fice bata ce min komai ba. Haka ina ji ina gani Inna ta kwa a lalle tai min duka afa tai min ga hannuwa ta ji a magani kala-kala ta ban tace na shanye, wani kuma tace idan lallan ya kama nayi wanka. arshe dai da dare Inna ta ha a min kayana Ni da ita da Safiyya muka doshi gidansu mahaifina, kowa zuciyarsa ba da Muna zuwa muka iske dangi cike da gidan ana ta hidimar buki da gaske, wanda ba wanda yasan Amarya sai a lokacin akai ta nuna ni ga dangina ana cewa nice amarya. Inna ta baroni ina kuka tana kuka tace gobe iyayenki za su zo ayi komai da su ki yi ha uri Jiddah haka taki rayuwar take ke kuma watarana sai labari." Ni da Safiya har dare ya tsala kowa na harkar gabansa ba a ce ga inda zamu kwanta ba don haka muka ra a gefen wata tabarma muka kwanta har safe. Tunda safe sai ga dangin Mamana sun zo da iyayen kaya bayin Allah duk da basu da shi amma sai da suka kawo duk wani abu da Uwa ke yi sun kawo min. Kayan kawai aka amsa aka watsar da su nan tsakar gida kamar dai yadda aka watsar da ni amarya da awata Safiya kalaci ma Yayar Mamata ta bada ku i aka siyo mana mu kai, har zuwa rana duk muna tsakar gida ni da dangin Mamata cikin ikon Allah sai ga abinci daga gidan Inna an kawo wanda shi ne wanda dangina suka ci na mahaifiyata duk da ana ta cin abincin amma ba wanda yace gana amarya ko na iyayenta. Sai zuwa la'asar aka ban sabbin kaya aka ce nayi wanka na saka lokacin za a aura aure, sai a lokacin naji ance an aura aurena da amaraddeni wanda ake kira da Dini kan sadaki Naira dubu talatin cif. Da dare aka auki amarya ina tare da awata da Yayar Mamata duk da sai da aka so yin fa a gun kai amarya an yi komai dangin Mamana basu tanka ba sai gun kai amarya suka ce dole a je da ko mutum guda ne a cikinsu. Wannan shi ne asalin aurena da Deni, buki da kwana biyu Mamana ta kawo min cincin da dubulan har da alkaki,
Chapter 10 · 0% Book details