← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 133

Sashe 62

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsaida shi tace, "Abubakar anya akwai zuciyar imani da tausayi a jikinka kuwa? Anya kuwa kana da adalci ka san shi ma kuwa? Yanzu idan akai iyar cikinka abin da kai min zaka ji haushin hakan kuwa? Abubakar me yasa wasu mazan ba ku da adalci ne? Me yasa kuke murna da karyawa mace zuciya ne? Tabbas zuciyarku kan mata bata da tausayi ko da yaushe cikin muradin sauraren kukan iya mace take. To a Yau a yanzun nake son mu kawo arshen ala ar tsakaninmu, domin na tsane ka na tsani soyayya ba zan ta a manta cin amanar da kai min ba Abubakar ka manta da Ni ka ri e matarka." Ta tafiyarta ta bar shi gun yana goge zufa. Wannan shi ne arshen soyayyar Jiddah da Abubakar. Tafiya kwana nesa sai ga Jiddah ta gama karatun ta, da kanta ta ga dacewar zuwa Kano gun Hajjo tai kwana biyu don kawai ta huta don haka ta shiryawa yaranta kayansu duka ta kaiwa Mama ta aje masu kayan abinci masu yawa tai bankwana da su ta wuce Kano tana jin ta wasai ba ta da wata damuwa ko takaici domin ta riga ta fahimci cewar soyayya da aure su neasu saka mace a damuwa to insha Allah ta yi nesa da su ba zata sake yin su ba har abada, zata kalli kowane namiji da kallon matsala a gareta zata kalli kowane namiji da kallon marar tausayi a gareta don haka zata zama cikin shirin korar soyayya ko ta halin a daga rayuwarta. Idan akwai abin da Jiddah ta tsana to kalmar ina sonki ce Jiddah. Ko taga namiji na mata kallon nan nasu na yaudara sai taji nan take ta tsane shi. KANO TA DABO TUMBIN GIWA... Tun da Jiddah ta iso Kano take jin ta cike da farin ciki da annashuwa, bata da wata damuwa ko tashin hankali ko da yaushe tana waya da Mama da yaranta don haka sai gogewa take tana ara waye wa, ganin zamanta haka nan ya yi yawa yasa ta shiga wata makarantar koyar da sana'a kala-kala don rage lokaci. Tun zuwan Jiddah Kano Mustapha ke cikin farin ciki ba kamar da ya fahimci cewar Jiddah zata jima a garin sai ya ji tamkar an yi mai bushara da gidan aljanna. Ita kuma angaren Jiddah a kwanakin nan tana yawan mafarkin Uncle Salim da wannan dogon mutumin da tun tana yarinya take mafarkinsa. Kamar Yau da take kwance tana barci tai mafarkin gata zaune ta yi tagumi, gefenta Uncle Salim na zaune ya tsira mata ido kamar mai nazarinta, ya ja ajiyar zuciya ya ce, "Jiddah kin san cewa hanyar da kike ba mai ullewa bace ba? Ki sani saka tsanar soyayya a ranki ba abun tutiya bane ba, shin ba ki son ace Yau gaki kin yi aure ba Deeni na kallonki yana ganin yadda kika cigaba ba kika cika burinki na auren soyayya ba ya ji nadama da takaicin abin da ya yi maki a baya ba? Ko kin auka har zuwa yanzu Deeni bai jin takaicin rabuwa da ke ne? To ki sani Ni dai idan zan baki shawara ki ji to ga wanda naga zai maye maki duk wani gurbin ba in cikinki da farin ciki Jiddah." Ya kama mutumin zai jiyo da fuskarsa kenan ta farka daga barcin ba tare da ta ga fuskar ko waye ba Uncle Salim ke ta mata maganarsa. Wanka tai ta shirya zata shiga gidan Bilkisu kenan sai ta kalli gidan Mustapha kawai sai ta ja ta tsaya ta fiddo wayarta daga aljihun rigarta ta nemo lambar ta kira shi, har ta katse bai auka ba, sai kawai ta sa a ranta idan ta sake kira bai auka ba zata goge lambar daga wayarta baki aya ta share shi tunda daman ba wani abu ke tsakaninsu ba ko da sai gaisuwa idan sun ure ma juna. Sai dai tana fara ringing ya auka ya ce, "Salamu alaikum." Ita ma ta amsa mai tai shiru, kamar daga sama taji ya ce, "Jiddah mutanen auye an shigo birni ne?" Dariya maganar ta bata wai mutanen auye watau ya koya daga Uncle Salim kenan shi ne ke ce mata hakan. Cikin sautin dariyarta tace, "Birni ko auye dai? Ai bai kamata ba kace na zo birni ba tunda kowa yasan daga birni nake don yadda Kano take State haka ma Barno take state don haka ka kashe wuta kawai duk kanwar ja ce." Shima cikin dariya mai cike da farin ciki ya ce, "Ba don na yarda ba fa, amma ki shirya na kai ki shan ice cream ki ga gari kuma nasan kin yarda da maganata." Kamar tace ya barshi sai kuma ta samu bakinta da amsa mai cewa sai ya fito Ta kashe wayar tana murmushi ta shige gidan Bilkisu, sun ta a fira ka an wayarta tai ara tana dubawa ta ga Mustapha ne don haka ta auka, cikin fara'a ya ce, "Ki fito mu je ina ofar gidan." Cikin sauri ta mi e ta nufi waje tana ma Bilkisu sai ta dawo. Tun daga zauren gidan Bilkisu take jin amshin turarensa wanda tunin duniya amshin ke matu ar birge ta sosai take son amshi musamman na turare sai kawai ta samu kanta da murmushi. Yana zaune kan mashin ya sha sabuwar shadda sai yalli take duk da cikin duhu ne, shi kan shi tun da ta fito yake kallonta yana jin nisha i a ranshi kamar har sun fara soyayya da ita ne irin za su fita yawon nan na sha atawa, har ta iso gun bai san ta isa ba, sai da ta maimaita sallamar sannan ya dawo daga duniyar tunani. Nan take amshin turarensu ya ha e da na juna sai wani sansanyan amshi ya bayyana gun mai da in sha Kamar su zauna ya tasa ta gaba yai ta kallo haka yake ji sai kuma ya goya ta suka nufi cikin garin domin ya gwada mata gari kamar yadda ya ce. Wajajen shan iska ya kaita sosai, duk inda suka je ban da tsokanarta babu abin da yake, ita kanta ta yi mamakin yadda bakinta ya bu e take maida mai martanin tsokanar da yake mata. Sai wajen tara da rabi suka dawo da leda cike da ice cream da kaza da sauran tarkace, ko da suka iso ofar gidan sun jima tana tsaye yana zaune kan mashin suna ara tsokanar juna kamar sun saba da juna sai da goma ta buga sannan su kai bankwana ya buga mashin insa ya kama hanyar fita unguwar ta kira shi a waya cikin mamaki tace, "Malam ya da koma wa yawo bayan dare ya yi?" Yana dariya ya ce, "Wa ? Ai sha biyun dare marecen Kura, ba yanzu muke dawowa ba mu." "To Allah Ya tsare Ya dawo da kai lafiya." Cike da jin da i ya amsa da "Amin Ya Allah na gode, idan na dawo zan kira ki." Ta amsa da to kawai ta shige gidan, har Hajjo tai barci ma lokacin don haka ita ta rufe gidan ta ware abubuwan da ta dawo da su ta aje don ta oshi tai wanka ta saka kayan barci ta kwanta. Yana shan kwanar gidan ya samu wani kwalbati ya kashe mashin in ya sauka ya zauna ya cigaba da tunano abin da ya faru da shi da Jiddah a yanzu. Muryarta kawai yake ji a kunnensa yana farin ciki ji yake nishadi nata ara arfi a zuciyarsa. Komai nata ya yi mai, yadda yake bu ata, gata kyakkyawar gaske ajin farko, ina ma Allah zai wanke mai ba in cikinsa ta hanyar mallaka mai ita matsayin sakayyar rayuwar aurensa? Tabbas da ya yi matu ar farin ciki kuma ya amince cewar bai yi ha urin banza ba. Sai wajen sha aya ya tashi ya je shagon da yake siyen fura ya siya ya koma gida, tuki yake amma ji yake kamar cikin sararin samaniya yake take don nisha Sai da ya gama komai kamar yadda ya saba bai iya kwanciya bai wanka ba ya saka doguwar rigar barcinsa ya jawo waya, sai kuma ya samu kansa da tunanin me ya kamata ya yi ne? Kiranta zai yi ko text zai tura mata? Sai kawai ya samu kanshi da tura mata text kamar haka. "Ban san haka ake farin ciki ba idan akai irin wannan fitar ba sai a Yau don haka gobe ma ina nemanki don mu sake fita ba mamaki farin cikin zai fi na Yau, ina maki ban gajiya sosai." Jiddah na kwance tana game a wayarta ta ji alamar shigowar sa o don haka ta duba sai ta ga na Mustapha ne, ita ma murmushi tai ta samu kanta da maida mai amsa kamar haka. "Tabbas akwai farin ciki kam, don ji nayi tamkar mu cigaba da tafiya a haka har abada. Gajiya kai za a tambaya kai da ka sake fita bayan mun dawo." Yana ta kallon sa on daya tura mata nata ya shigo ya bu e cike da nisha i ya karanta. Sai da ya yi tsalle ya fasa ihu don murna kana ya koma ya kwanta ya tura mata. "Kin ji ta kamar gaske, bayan na lura da yadda kika agara mu dawo gida kamar na sace ki shi ne za ki ce hakan." aramar dariya tai ba ganin abin da ya ce, don haka ita ma sai tace mai. "Ba dole ba na agara ka maido Ni gida ba kada ka saida Ni ka samu ku i ka ga kyakkyawar da babu irinta a auyenku." Sosai ya yi dariya da abin da tace , sai ya samu kanshi da ce mata. "Haba dai ai duk kyawun naki naga baki kai Jiddah ta ba ko? Nasan kina ganinta za ki ce dama na gaya maki hakan." Girgiza kanta tai tana murmushi tace mai. "Ikon Allah! Ai tunda ta ci sunana dole daman nasan za tai kyau don haka albarkar nawa ne ya shafe ta. Sai da safe ka kula da kanka barci zan." Tana tura mai ta kashe wayarta ta gyara kwanciyarta ta kwanta tana jin nisha i sosai a ranta. Mustapha kam kasa barci ya yi bayan ya tura mata sa on sai da safen shima. Ganin ya kasa
Chapter 62 · 0% Book details