Sashe 37
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
dinga tausaya mai ta dinga ba shi duk wata amanarta kamar yadda zai bata tashi amanar, matar da zasu rayu cikin farin ciki su dinga rayuwa mai cike da inganci wadda ke cike da girmama juna yake bu ata. Ya sha mafarkin yana tare da wata yarinya matsayin matarsa suna rayuwa cike da nisha i, ya dawo gida daga aiki ta rugo ta tarbe shi, ko da yaushe cikin fa a mai kyawawan kalamai take masu kwantar da zuciya, bai ta a ganin fuskarta ba amma Yau da ya ji muryar Jiddah sai ya tabbatar da cewa ita ce a mafarkinsa. "Ya Allah ka za a min mafi alheri kasa mu zama HA IN ALLAH Ni da Jiddah don girman zatinka." Haka Mustapha ya dinga tunani yana sa awa da kwancewa, ya rasa wa zai tambaya ya gaya mai tana da aure ko bata da aure, yana zaune yaga sun fito daga gidan dake jikin gidansa sun shiga gidansa. Wani sanyi ya ji daya ga ta shiga gidansa sai ya yi sauri ya bisu shima ya fa akinsa, ya bu e taga yana kallon tsakar gidan ko Allah zai sa ya dinga hango ko da wulgin yarinyar ne ya ji dama-dama. Zainab ta dubi Maryam tace "Kin ganta nan wai tafiya za tai gobe don Allah ba ta bari ba sai an yi arba'in ba sai ta tafi ba?" Jiddah tai murmushi tana kallon tsakar gidan kamar mai nazarin wani abu a ranta sai kuma tace, "Mama ta tafi da Haidar kada yai ta mata kuka ne." Maryam ta saka baki tace, "To ba ya saba da ita ba? Ai ba zai damu ba tunda yana ganinki ya amince ya bita." Ni dai ban wani jin da in zaman gidan saboda duk sai naji tamkar wani na kallona, haka ma dai tsarin zaman gidan bai min ba, don haka na tashi tsam nace ma Zainab zan koma gida sai na sake fitowa. Ta tashi ita ma ta biyoni tace mu je tare ba za ki tafi ki barni ba muna firar arzi Yana kallonsu suka fice daga gidan ya yi ajiyar zuciya yana jin wani nauyi na sauka daga cikin zuciyarsa yana asa sai ya ji wasai tamkar bai da damuwar komai a gidansa. Ko da muka koma gidan Zainab kasa natsuwa nai kawai sai na dinga tunano mafarkina da wannan bawan Allah wanda duk lokacin da zan mafarkinsa yana nuna min auna yana lallashina yana sunsunar jikina tamkar wasu indiyawa. Ganin Zainab ba zata barni nayi tunanin dake yawo a zuciyata ba na tashi nace mata zan je gida na dawo wanka zan yi, ba don ta so ba haka na fice ina cewa yanzu zan dawo na samu na kubce na fice. Yana inda na barshi azun bai tashi ba kenan? Haka na raya a raina na ra a ta gefensa na wuce ina jin sansanyar amshin turarensa, ina son amshi hakan yasa na jima zauren hajjo ina sha amshin turaren yana ratsa zuciyata sosai nake jin da in sa. Tunda suka fito ya sake fitowa yana addu'ar Allah Yasa ya sake ganinta shi dai birge shi kawai take yarinyar idan ya ganta yana samun natsuwa sosai a zuciyarsa. "Jiddah!!! Ya ja sunanta a cikin bakinsa yana jin farin ciki na ratsa shi kawai na ambatar sunan da ya yi. Jiddah kuwa abin duniya ya ishe ta, so take ta koma gidan mahaifinta kamar yadda Hajjo ta bata shawara, so take ta ga mahaifinta tai mai wasu tambayoyin da ke yawo a zuciyarta tun tana Lagos har yanzu ta kasa sanin amsar su haka ta kasa daina tunaninsu, don haka take son ta ganta idonta idonshi don kawai tai mai tambayar ko da ba zai bata amsa ba tana son yasan tasan tambayoyin kuma daga lokacin ne zata ba kanta amsa idan bai bata amsar tambayoyinta ba. Sai da akai arba'in sannan Mama ta zo muka shirya tare don komawa gida, sannan hutun semester ya are don haka Hajjo taban ku in da zan siyayyar makaranta, har mun ha a kaya nace bari na je nayi ma Zainab sallama. Bata gidanta tana gidan Maryam don haka can na iske ta na gaya mata yanzu za mu tafi sai wani karon idan Allah Ya nufa. Yana akinsa ya ji sallamarta don haka ya dawo saitin da zai dinga kallonta, yarinyar tamkar wata ar budurwa haka yake ganinta a idanunsa komai nata ya yi cif daidai ra'ayinsa. Waje ya fita ganin tana niyyar fita so yake ya ga tafiyarsu tunda ya ji tace tafiya za su yi yanzu. Haka kau akai ta fito da Zainab suka wuce ta gabansa yasan ba lallai bane idan ta ganshi suka fa a gidan Zainab basu jima ba suka fito tare suka shiga gidan Hajjo. Sai ya ji tamkar ya bita ya tambaye ta tana da aure ko bata da aure? Sai ya ji tamkar ya tambayi Zainab awar matarsa kuma ma wabciyarta idan yarinyar na da aure. Sai kuma ya fasa ba wai don gudun tsogumi ko wani abu ba sai don gudun kada ace mai tana da aure kawai ne ba zai tambayar ba. Yana cikin tunanin yaga sun fito sun tafi yasan ta tafi kenan sai bayan wani dogon lokacin kafin kuma su sake ganin juna. Wayarsa tai ara yana agawa ta fara halin nata kamar yadda ta saba na magana kai tsaye ba wani kulawa balle taushi a Muryar, abin da tace ne yasa ya ji tamkar zuciyarsa zata fito don fargaba da acin rai. "Na gaya ma kai gaggawar sakina kafin nayi maka abin da baka zata ba wallahi." Kashe wayar kawai ya yi ba tare da yace ko ala ba. Mu ha u a kashi na gaba. Taku a kullum Haupha [8/5, 9:13 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa