Sashe 131
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 46 Maryam na zaune tana kallo ta gyara akinta tsab ta yi wanka ko'ina ba laifi Hafsat ta fa a gidan tana masifa tana kuka. Da farko Maryam bata auki muryar Hafsat ba sai da ta fa o falon sannan ta kalle ta sau guda ta maida kanta ga kallon don a tunaninta ita da mijinta ne ke masifar, ita kam yanzu ta gaji da zaman hauka na kishin auye zata yi koyi da halayen Jiddah ta zauna lafiya da mijinta da danginsa, saboda ta ga hatta yaranta bayan Jiddah suke to waye ba zai koma bayan ta ba? Maryam ta kalli akin sosai ta sake fashewa da kuka tace, "Maryam don Allah haka kike zaune da wannan yarinyar har kika samu sararin zama da yin kallo ba komai a ranki? Duk ina zafin kishin da nasan ki da shi akan mijinki? Anya kuwa haka nan Jiddah ta bar ki kema bata gama da ke gun Malamanta ba? Ai nasan ba zan ce Malami guda ba sai dai tarin Malamai wallahi, to idan ke ta gama da ke Wallahi Ni ba zan yadda ba sai naga abin da ya ture wa blBuzu na i wallahi." Maryam ta kalle ta murmushi ya su uce mata yanzu kam ta fahimci komai, fa an na Jiddah ne bana maigidan ba kenan, sai ta samu kanta da sakin dariya sosai kafin ta kalli Hafsat tace mata cikin rashin damuwa. "Zauna na baki labarin abin da ya faru bayan baki nan wanda ya zame min ishara a rayuwar aurena. Ta ja ajiyar zuciya tace. "Bayan kin bar gidan nan ban san cewa kina can kina tsula tsiyarki ba kin hana maigidan nan ko da cin amarcinsa ba Ni kuma na rufe ido na dinga zabga mai rashin mutuncin safe daban na rana daban, duk abin nan bai ta a nuna min ba laifinsa bane balle na amaryarsa ba har dai ta kaini da yin yaji duk ban san wainar da kike toyawa ba sai a bakin wata mata a ma wabtanmu take gayamin ai kin yi asiri kin raba Mustapha da amaryarsa kin hana shi zama lafiya shike kai ki ko'ina hatta gidan awayenki don ki nunawa duniya ke kin isa. Matar ta cigaba da gayamin a ranar ma kun ha u gidan wani sunan kina ta bada labarin yadda kika maida Mustapha talasuru, matar ce taban shawara na koma gidana nayi ha uri amarya ma ta shanye wannan takaicin balle Ni dana kwana biyu da Mustapha? Hakan yasa na ji na amince a ranar ban kwana ko'ina ba sai gidan nan. Kin san abin mamaki? Na iske ba yarana ko guda a gidan nan na zagaya gun awata naga ko su na can tace min su na gidan Jiddah naji matu ar takaici da haushi amma na daure na koma gidana nasa waya na kira Mustapha a lokacin yana gabanki don naji muryarki kina cewa kar da ya wuce minti uku yana magana da Ni. Sai kawai na kashe wayar dama kiransa nayi nace ya maido min yarana. Da dai naga ban da mafita sai na sake shiga gun awata nace tai min kwatancen gidan Jiddah ta kuwa yi min na kwasa rai ace na tafi gidan a matu ar fusace ina tunanin irin cin mutuncin da zan ma Jiddah da wula anci idan na isa gidan. Ina zuwa na iske gidan a bu e nasa kai na shiga naga ashe mai ruwa aka bu e ma ofa yana zuba ruwa a tanki, na shige ba ko sallama kawai naji ana magana dole na ja na tsaya don kin san Ni da la e daman ko a gidan nan. Kan kunnena naji Jiddah na koyawa yarana karatun Alkur'ani don ga alama lokacin da naje sun gama, naji ta ora da gaya masu muhimmancin iyaye musamman Uwa ta ara gaya masu hatta Annabi da kansa ya ce Uwa kafin ya ce Uba. Kin san dai yadda yarana suka raina Ni ba su jin maganata sam don ko tsorona ba su yi amma naji Jiddah na cewa su yi mata al awarin babu wanda zai sake ata ma Mamarsa rai ko ya yi mata rashin kunya, jin kunnena suka amsa da cewar sun daina ai tun da tai masu magana ma. Sai na tuna da cewa a lokacin baya fa sadda su na zuwa gidan tabbas sun fara sauyawa ba mai yi min musun magana kuma basu barina nayi aiki balle maganar girki nayi mamaki warai da naga sun iya girki mai kyau suka ce min Aunty ce ta koya masu ta kuma ce su daina bari na ina aikin gida, haka zalika duk bayan lokaci take aiko da ku in Napep tace su je ina masifar ina zagin haka za su tsallake Ni su wuce gidanta ita ke masu kitso da unshi ta kuma ba su turaren wuta da humrar jiki mai amshi tace su kawo min duk da cewar ubansu ba ta ita yake ba amma ta danne komai take ma yaransa hidima har da matarsa. Jikina ya yi sanyi alau sai na kasa shiga ciki na juyo kamar munafuka na koma gida ranar a sukuku na yini har sai da Mustapha ya bar wajen ki sannan ya Kirani kamar kar na amsa kiran sai kuma na amsa nace mai ina gida ya maido min yarana. Ban jima da mai wayar ba sai ga su sun dawo sai kumburi suke basu so dawowa sam, amma duk da haka sai da su kai min sannu da zuwa suka nuna min iyayen kayan da Jiddah ta basu duk sabbi ne masu tsadar gaske Nima da nawa kayan kamar kowane lokaci a ranar ne kawai na amshi kayan nace na gode a fili naga yadda yaran su kai murna da hakan har ma suka ora min da bayanin Aunty Jiddah fa bata lafiya kuma Babansu bai kwana gidan, su na yawan kama Aunty Jiddah na kuka idan ta gansu ta nuna ba kuka take ba. Sai naji ta ban tausayi naji a raina ina sonta duk da kishiya ce a gareni amma tabbas ita in alheri ce a guna don haka sai jikina ya yi sanyi sosai na rasa ya zan yi na magance wannan matsalar kawai na shiga gidan Hajjo na amshi lambar awarta Barista Alawiyya na kira ta ban gaya mata koni wacece ba na dai gaya mata Jiddah na cikin matsala a gidan aurenta. Tai min godiya ta kashe wayar sannan na ji na samu natsuwa don nasan labarin Alawiyya sosai bata da sau i akan lamarin Jiddah. Bayan kwana biyu da hakan sai ga kiran Alawiyya a wayata kamar kar na auka sai kuma na auka tashin farko ta kama sunana arau a bakinta sai da gabana ya fa i sannan muka gaisa tace min "Nasan za ki yi mamakin jin yadda na kama sunanki ko? To kar ki mamaki domin kin san aikinmu ya bamu damar bincikar duk wanda ba mu yadda da shi ba ke harma da wanda muka yadda da shi bincike muke don mu ara mai matsayi a zukatanmu. Tabbas Hafsat tai wauta amma ina tabbatar maki da cewar kanta zata are wautar don a cikin datsin nan na warware duk wata tufka da tai na warware ta tsab don haka zata fara girbar abin da ta shuka da kanta, kuma zamanta na gidan Mustapha ya are daman nayi tunanin zaman Jiddah cikin koshiyoyi har biyu ba zai yi mata armashi ba har a raina nasa zan fitar da guda a cikinku don Jiddah da maigidan su samu sau in ba in kishinku da haukanku, to madalla da ke kika gane gaskiya amma fa ki sani ina ankare da komai da kowa indai akan Jiddah ne don tun kafin ki Kirani daman na je gidan na fahimci akwai damuwa don haka na kyale ta don nabi ta asa nayi maganin damuwar hakan yasa na fasa zuwa inda zan je kai tsaye na nufi inda nasan za a taimaka kan matsalar sai ga shi kuwa komai ya zama daidai an kwance aurin da Hafsat tai ma Mustapha da taimakon mahaifiyarta. Maryam ina son ki sani Jiddah bata da damuwa sam kuma bata da jin zafi balle yashi don wallahi mijina naso ya auri Jiddah ba mijinki ba, saboda Jiddah alheri ce a duk inda take sai dai Allah bai nufa ba dole ina ji ina gani Jiddah ta auri Mustapha madadin mijina, don haka ki san me kike ki rabu da munafukai da mazuga ku zauna lafiya don Allah." Ta kashe wayar ba tare da ta ban damar furta ko da kalma guda ba sam. Tun lokacin naji kishin Jiddah yabar zuciyata sai haushinki da jin zafin abin da ki kai mana na rabamu da mijinmu don mugunta da son kai. Sai na fara daidaita kaina da mijina na daina zaginsa da tada mai hankali na daina tuna Jiddah matsayin kishiya sai a ar'uwata duk da har zuwa lokacin na kasa bayyana mata cewar ina sonta ba kishi nake da ita ba. Muna a haka wata rana cikin dare Mustapha na nan gidan da kwana sai naji wayata na ara ina dubawa naga sunan Aunty kamar yadda yara sukai saving a wayar don su na yawan yin waya ba kamar idan za su yi wani abun basu san ya ake ba su na kiranta ta kira ta gata masu ta wayar. Kamar kada na auka sai kuma naga dare ne don haka raina yaban ba lafiya ba don haka gabana na fa uwa na aga wayar, sai na ji muryar Jiddah a galabaice tana ce min bata lafiya sosai. Nai hanzarin kashe wayar na nufi akin maigidan na tada shi na gaya mai Jiddah ta kira wayata bata lafiya ina gani ya duba wayarsa bai ga alamar ta kira shi ba sam kenan dai Ni kawai ta kira saboda tasan ranar girkina ce nice ke da iko da shi sai na sake girmama kawaici da halaccinta sosai naji dama zan iya koyar duka halayenta dana koya ko don na zama abar koyi ga wasu kamar yadda