← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 133

Sashe 28

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 20 Kasa rufe bakinsa ya yi, na tashi tsam na bar gun, har na tafi na dawo na amshi naman dake hannunsa na auki leda fara na kwashe mafi yawan naman dan saida ta cika dam, sannan na ulle na ba shi nace "Ga wannan ka kaima Safiya tana da rabo a wannan amma a nawa ko tayi tsafi da ba ar Jaba ba zata ci shi ba. Ga wani sa o mai da in fa a ma zuwa gareta , ka gaya mata duk ranar da ta sake zuwa gidana sai na yi mata abin da yafi wanda nayi mata kwanaki, idan kuma tana ganin arya ne to don Allah ina jiran zuwanta gidana ta sha mamaki." Duk da a raina ina jin tamkar zai rufe Ni da duka ne jin furucina amma sai naga ya auki naman ya saka aljihu yana cewa, "Masifaffar banza kawai ke dai kika sani kuma ai nan gidan za ki aje komai." Ya sa kai ya fice. Kawai sai naga ai bai kamata ba ma ace shike da wannan Uban naman don haka na auki sauran na ha e da nawa na rufe na kama harkar gabana ina jin zuciyata na tafasa kamar zata fito waje don ba in ciki. Bayan sati guda da suna na shirya tunda safe na shiga gun Abban Haidar nace "Zan je gidanmu na kaiwa Mama yaran ta gani Yau, amma zan dawo kafin sanwar ruwan zafi don nayi wankan yamma kan lokaci." Ya juyo ya kalleni sosai yace, "Wai da gaske wannan karon ba za ki ban komai ba na haihuwar? Ance min ana bada ku in karin angon jego fa amma naga ke baki da niyyar bani." an murmushi na dube shi nace, "Tabbas ana ba da ku in karin angon jego daga dubu ashirin zuwa sama amma fa ga angon jegon da ya tabuka abin kirki ya yi bajintar siyen kayan barka ga maijego to tilas a ba shi ku in karin angon jego don ya rage hidimar suna dake tafe kanshi. Amma kai nawa ka kashe min tun da na haihu? Me ka siya ka kawo min kace ga shi na barka ne? Ba Ni ba ko yaranka da suka zama dole kai ma sutura bakai masu ba, to nikam me zai sa na kwashi ku i na baka don ina tsoronka buge Ni ne ko kar ka kashe Ni?" Girgiza kanshi kawai ya yi ya maida kanshi ya kwanta, Ni kuma na fice ina jiran yarinyar Maman Khairat ta zo ta goyanin Afnan na goya Afnah mu tafi. Sai da na tabbatar dana oye nama na sosai sannan na tafi na bar shi kwance. Ina zuwa na iske Mama ba don kar taga hawayena ba tabbas da na fashe da kuka amma ya zan yi? Haka Allah Ya addara mana Ni da mahaifiyata zamu yi rayuwa irinta unci da takaicin a namiji. Tabbas ko dan mahaifiyata sai na jajirce kamar yadda Hajjo ta gayamin, dole na zama iya aya tamkar da dubu gun mahaifiyata, dole ne na sakata cikin farin ciki kamar yadda take arin sakani duk da bata da halin. Bayan mun gaisa na kawo dubu biyar cikin dubu goman da Hajjo ta ban na bata da atamfa guda hu u masu kyau nace ga rarar jikokin nan Mama. Tai ta godiya , na gyara zama nace "Hajjo tace zan fara saro kaya daga Kano to sai naga ya kamata ke ma ki fara naki sana'ar Mama saboda zaman haka bai da da i sam. Ina ga zan baki dubu talatin cikin ku in sai ki samu sana'ar da kikasan tana da riba kuma bata lalacewa ki kama, kamar irin ta saida robobi nasan za ki yi ciniki sosai Mama." Ta dube ni ta yi jim ka an sai kuma tace, "Kina ganin hakan ba komai ar nan? Da kin barni haka ke kin kama sana'ar sai yafi, tunda kin ga yanzu ba kowa gabana Ni." Na zum ura bakina nace, "Ai hakan ma kawai za ai, ke dai ki taya Ni da addu'ar Allah Ya shige mana gaba kan lamarin dai kawai." Haka muka Yuni Ni da yarana, gun mahaifiyata cike da aunar juna, motsi ka an tace me nake so, ko me zata ban. Ganin angama sallar la'asar yasa na shirya tsab na ebo abin da nake bu ata na abinci na tafi gidana ina jin tausayin mahaifiyata fiye da yadda nake tausayin kaina. Ina zuwa na hango gidan a rufe, don haka na le a gidan Binta naji ko ya kai mata makullin gidan kafin ya tafi, tace min bai kawo ba. Asalima bai jima da fita daga cikin gidan ba. Na fahimci don nace mai yanzu zan dawo shi yasa ya rufe gidan, ga shi naga alamar tsohuwar dake dafa mana ruwan wanka ta ora sanwar. Don haka na fiddo wayata na kira shi, amma kira kusan biyar ba wanda ya auka sai kawai naji har na fusata ban sake bi takan wayar ba na samu aton dutse nasa na alle makullin gidan na shige daman nasan ofar akin bu e take don ba makullin rufe ta sai dai a sakaya kawai. Ina zama tsohuwar na zuwa ta cigaba da iza wutar ruwan wankan har ta tafasa, ta kwashe min na barta tana yi ma su Afnan, tana da kirki sosai matar domin duk sanda ta gama yi masu wanka sai ta wanke min kayansu ta wanke har da na Haidar, hakan yasa nima nake yawan yi mata kyauta iyakar arfina. Ba Deeni bane ya dawo gidan sai bayan magrib irin gab sallar ishsha'i sannan ya dawo. Da yake ofar akina na aje kwa on don ma ba sai ya sha wahalar nemansa ko tambaya ba. Ina jinsa yana cewa "Wane isasshen ne ya lalata min kwa on gida? Ai ko Allah sai kin biyani ku on nan inga ta aryar rashin mutunci." Har tuntubar nake wajen fitowa ofar akin nace, "Magana kake ne?" Ni ma zuwa yanzu na fahimci yadda nake bala'in ha e fuska duk idan zan mai magana sai naji tamkar zan kashe kaina don mugun haushinsa da nake ji. Ko ganin irin muguwar hararar da nake watsa ma shi ce tasa ya shige aki yana jan tsaki. Nima ban san ya akai ba na ja nawa uban tsakin wanda ya fi nashi ara da sauti. Har ya shige ya sake fitowa, 'Ke wai Ni kike yi wa tsakin?" Fuskata ba alamar tsoro nace, "Kai da kake min kanwa na kasa ne da ba zan rama ba?" Na wuce shi fuuu na fa a kan kujera na zauna ina cika ina batsewa. Tunda Deeni ya fahimci ban cikin matsalar komai Ni da yarana kullum sai nayi girki haka mutane na yawan shigowa muna gaisawa ana fira sai na samu kaina da rashin damuwa da lamarin Deeni kwata-kwata bai gabana. Abinci duk lokacin da na dafa ina zuba mai yawan gaske tunda yanzu a cikin mazan unguwa yake zuwa cin abinci. Duk da ina jin shi wani lokacin idan ban gama da wuri ba idan ya aiko nace yanzu zan kawo yai ta masifa har sai sun dinga ba shi ha uri kamar irin shi ne ya siyo ya kawo min na kasa girkawa da wuri. Ni dai ko tankawa ban yi idan nice na kai abincin yake yin fa an gabana. Muna a haka na shirya tsab na nufi Kano don saro kayan da zan cigaba da saidawa. Zuwa yanzu daman Deeni babu ruwanshi da Ni ko harkata balle ta yarana, sai ya ga dama yake aukar su ko da yake yana yawan aukar Afnan don ita ce mai sunan budurwarsa in ji shi nasan duk dan in ji haushi ne amma ko a jikina , kuma shi ka ai ke kiran yaran da sunansu amma kowa Afnan da Afnah yake kiransu. Har na fice ya kira Ni ta waya, wai na samu yaro na aika mai da ko dubu guda ce bai da ku i. Kamar ince babu sai kuma na ce to, na aiki yaron Binta nace ya kai mai. KANO Tun a mota na kira Uncle Salim na gaya mai ina hanyar zuwa Kano. Ina sauka tashar mota na iske Uncle Salim na jirana, don haka ban sha wahala ba muka isa gidan Hajjo. Hajjo na ga ni na ta rumgume ne tana ta jin da in yadda ta ganni babu muguwar kama kamar lokacin da nake goyon Haidar. Abinci mai rai da lafiya na iske an aje min, na ci iyakar ci na, mu kai ta labari da Hajjo da Uncle Salim. Uncle Salim ya mi e tsaye ya ce, "Jiddah bari na fita Mustapha na jira na waje za mu je wani waje sai na dawo." Ni da Hajjo muka bi shi da adawo lafiya. Hajjo ta dube ni "Ya kamata ki shiga wajen awarki Zainab ko da yaushe tana yawan maganarki idan ta shigo gidan nan." (Zainab awata ce nan makwabta tun zamanin zama na gun Hajjo tamu ta zo aya da ita) na mi e na auki Afnan sai kuma naga barci take don haka na aje ta na wuce ina ce ma Hajjo sai na dawo. Kamar wal iya haka yaga wul inta ta wuce idan ba gizo idansa ke ma shi ba gidanshi ta shige. Shi kam yarinyar na birge shi sosai yake jin tana ba shi sha'awa tana da kyau haka tana da jiki mai kyau da tsayawa a zuciya. Tun shekarun baya ya so nuna mata so sai ya wayi gari bai san yadda tai ba, ya yi nauyin bakin tambayar abokinsa Salim labarin yarinyar har ta kai lokacin da Salim ke gaya mai ta yi aure, hakan yasa ya cire ta daga ranshi amma yanzu yana ganinta sai da ya ji ina ma ace matarsa ce?" Ko da yake shi yanzu ba ta mata yake ba domin ya yi masu ku in goro duk kanwar jace basu da amana haka basu da kirki sam basu san darajar na tare da su, amma yana ji a jikinsa duk da tabon
Chapter 28 · 0% Book details