Sashe 43
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hauwa'u Salisu (Haupha)* *____________________________________* KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* '''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}''' https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Page 26 *Ku yi ha uri kwana biyu kun ji Ni shiru, ku sakani a dukkan addu'arku don haka.* Washegari tunda safe suka nufi gidan yarin cike da abubuwa da dama a ranau. Barista Alawiyya na tunanin su waye suke da ala a da mahaifiyarta akan wannan kisan? Me yasa mahaifiyarta ta makance ne? Tana da tarin tambayoyi da take da bu atar ace mahaifiyarta ta amsa mata su, sai dai matsalar guda ce ga alama mahaifiyarta ta riga ta gaji da duniyar duba ga yadda abubuwa suka faru da ita na rayuwa, tabbas ba zata ta a barin hukuncin kisa ya tabbata ga mahaifiyarta ba, ko da hakan na nufin abubuwa da dama ne zasu faru kuwa. Ya zama tilas ya zama lallai ta bibiyi masu bibiyar mahaifiyarta, dole ne ta nunawa duniya wannan karon shari'ar tata ce, da ita ake karawa ba karewa take ba, ya zama wajibi tai shari'ar da za ta finciko duk wani alhaki da ke mallakin mahaifiyarta ta mi a mata. Tsurama motar Daddynta ido tai, "Sai dai kai ha uri Daddy amma wannan karon hatta ahalinka sai na ana masu abin da suka ana mata na raba ta da mijinta suka barta da aramar yarinya ba ci ba sha na tsawon shekaru wanda hakan sun karya doka ta shafi na dubu aya da dari bakwai da tamanin da uku ne (1783). Dr Falsal ya kalleta, "Don Allah ki natsu ki kwantar da hankalinki, domin nasan cewa tunda Allah Yasa kika amshi wannan case to ya zama tarihi ba abin da zai shafi Mama da yardar Allah zata fice daga wannan yanayin. Kinga tunda muka taho baki yi maganar yara ba, bayan kin san suna makaranta muka taho muka barsu, har mun kwana... Wani banzan kallo ta maka mai wanda yasa ya rufe bakinsa ba tare da ya shirya ba. Tabbas Alawiyya nada ha uri da kauda kai, amma fa idan ranta ya aci tamkar bata san yadda kalmar mutunci take ba ko ha uri, lokacin da mutane ke gaya mai yana auren mace-namiji dariya suke ba shi, wai har tambayarsa ake anya bata dukansa? Saboda yadda take da zafi kan aikinta uwa uba ta sha kamo attin maza da kanta ta kai su gaban Shari'a musamman idan ta danganci fyade ko mijin dake wahal da matarsa. Duk jinsu yake domin shi ko cacar baki bata yi da shi, duk da yana mata fa a musamman kan yaransu amma sai dai ta ba shi ha uri tai tsit bata sake magana. Sau aya ne watarana suna tafiya a mota za su wuce daidai gadar Gaida road suka ga wani magidanci ya dage sai dukan matarsa yake ga ciki ga yara uku sai kuka suke suna ri e shi, amma har su kaima duka yake yana ara komawa kan mahaifiyar tasu. Duk ga mutane amma sai suka tsaya kallo wasu ma har auka suke a waya ba ruwansu da zuwa su raba fa an. Shima dai kamar kowa ne mai mota fakin ya yi kawai yana kallon yadda mijin ke dukan matar tana ta kare cikinta tana kuka. Kawai ganin Alawiyya ya yi gun bai san lokacin da ta bu e motar ta fice ba, sai hango ta ya yi ta auke mijin da mari hannu bibbiyu, kamar a Film ya ga ta dage iyar arfinta tana jibgar mutumin nan, ganin tana niyyar lahanta shi yasa ya fice da sauri ya nufi gun da zummar janye ta, lokacin ta dun ule hannu zata sauke shi kan cikin mutumin ta sauke mai shi a kumatu, sai da ha orinsa ya fice don azaba. Ganin mijinta ta daka yasa ta sake fusata amma sai ya yi ta maza ya sake karewa dole ta ha ura ta nufi mota nan take tai waya, ba a jima ba sai ga an sanda sun iso gun da motar asibiti, ta dube shi ba wasa ta ce ya je asibiti a duba shi ita kuma zata je office tare da matar da yaran yanzu, su yi waya idan an gama mai za ta je ta auko shi. Ta dubi mutanen dake gun ta daka masu tsawa tana cewa, "Wai ku nan mutane ne ko dabbobi masu afa biyu hannu biyu? Ko da yake nasan ko dabbobi idan suka ga an'uwansu dabbobi na cutar junansu shigar masu su ke amma ku sai abin ya zame maku abin nema da tutiya, to wallahi duk wanda ya sake ya ora wannan abin sai na kama shi na aure nasa an ci shi tarar manyan ku e. Kar ku manta sunana Barista Alawiyya Bello Gareji." Nan da nan mutanen kowa ya watse yana gogewa kar da ya jawa kansa bala'i da rana tsaka dan kowa yasan wacece Barista Alawiyya Bello Gareji a Kano da kewayen Kano da sauran Jahohi don babu inda ba a aukar ta aiki kuma indai ta je sai ta ci nasara. Cikin matu ar tausayawa ta kama matar ta shiga motarta, suma yaran suka shiga kai tsaye babban asibitin ta dake unguwar Bachirawa ta nufa da ita don a duba lafiyarta data abin da ke cikinta. A takaice sai data sa mijin yin gidan yari ta kuma tsaya tsayin daka kotu ta raba auren ta kuma mallaka ma matar gidansa, kyauta har da tarar wasu iyayen ku i da zai ba da don kula da yaransa da cikin dake jikinta, wanda sai dai danginsa su kai karo-karo suka ha a ku en tilas aka ba matar. Haka bai manta ba da shari'ar da ta gwabza da an gidan ministan harkokin waje na garin Abuja wanda yawon shan iska ke kawo shi Kano ya yi wa iyar wata almajira fyade har ta mutu, cikin jarida ta tsinci labarin amma sai da t upai ruwa tai tsaki matsayinta Na babbar Lauyar dake zaman kanta ta shiga case in ta dinga gogawa da lauyan asar waje da Uban yaron ya auko kan a kare mai yaro, amma arshe sai da ta kai Yaron gidan yari, kuma ta sa Uban ya biyya diyya tunda yana tarin dukiyar da yake ba yaran na abin da ya ga dama. Ganin hakan Uban ya dinga turo mata an daba kala-kala amma sai dai ta tura mai su asibiti kawai ya rasa yadda akai ma take masu wannan laga-laga. Don kuwa shigowar an fashi gidansu har bai iya irga yawansu, sai dai ya ga ta ci riga da wando kamar wata ar China ta kama artabu da su sai ta kama su. Shi ya rasa inda ta koyo wannan shegen fa an ma wallahi. Shafa inda ta cire mai ha ori ya yi ya sauke ajiyar zuciya ya sadda kansa tabbas yana da bu atar ya kama bakinsa idan ba haka ba kuma yana da kyau ya tattara ya koma gida gun yaransa ya jira ta, idan ta gama ta dawo gunsu. Daram! Gabansa ya fa i ya ji jiya tana cewa idan an isa a fara kama shi da Daddy sannan a kira ta a waya! Tabbas Alawiyya tafi aljani iya shai ana gata bata da tsoro ko da wasa, yanzu ta ya zai iya nufar Kano bayan neman a auke shi ake?" Jin alamar an tsaya da motar yasa ya dawo hankalinsa ba tare daya ba kanshi amsar tambayar da ya yi ba. Tare suka shiga ciki, fuskar Alawiyya sam ba annuri hatta Daddyn ya lura da yadda ta tsare gida take auke kai. Bayan sun nemi a fito masu da Fatimar suka zauna kan babban kafet in da Dr Falsal ya shimfi a masu kowa da abin dake damunsa. Daddyn Alawiyya na cike da tsoron kar dai ace da gaske ya sake rasa Fatima duk tsawon shekarun daya auka yana jiranta. Hawaye suka zubo min bai damu daya goge ba. Barista Alawiyya na tunanin yanzu a nan mahaifiyarta ta kwana, cikin fitsari da kashi da cinnaku da sauran abubuwan yama?" Hawaye suka zuba mata bata damu data goge ba ita ma. Dr Falsal na tunanin yanzu kenan rayuwarsa na cikin tashin hankali saboda matarsa? Kenan wannan karon zata iya bijire mai idan yace ga wani abun kan mahaifiyarta? Tabbas akwai damuwa mai tarin gaske, a Yau ji yake yana jin wani abu mai kama da nadama tare da danasanin barin Alawiyya ta zama yadda ta zama na amsa sunan babbar Lauya. Shigowar Fatima gun yasa kowa tashi tsaye yana kallonta, Alawiyya ta tashi da sauri ta tarbo ta cikin sauri ta kai ta gun da zata zauna. Cikin lalube ta zauna tana ri e da hannun Alawiyya, ta zauna bakinta auke da "Allah Ya yi maki albarka." Bayan kowa ya zauna, Barista Alawiyya ta gaida Fatima ta amsa shima Faisal ya gaida ta, ita kuma ta gaida Daddyn Alawiyya. Barista Alawiyya ta dubeta cike da tausayi ta ce, "Mama na gani a labarai an ce ku uku ne gun maidiganku amma ban ga maganar su a cikin case in kisan kan ba, sannan kuma na gani an ce kin yanka shi ne sannan ki ka caka mai wu a a ciki... "E tabbas haka ne duk na aikata! Hawaye suka zubo ma Daddy, yayin da Alawiyya tai murmushin ya e ta dubi Mamarta tace, "Naga an saka cewa ke ce amarya kuma ke ce kawai kika ta a haihuwa da shi a gidan don haka kika kashe shi don ki samu gado... "E haka ne nice na kashe shi! Kallonta kowa yake ban da Alawiyya data sadda kanta asa hawaye na son zubo mata amma ta i basu damar zubowa. "Tabbas Mama ba ke ce ki kai kisan kan nan ba." Cewar Alawiyya. "Na rantse da Allah nice na kashe Alhaji Alawiyya! Don Allah kar da ki saka kanki a halaka domin Ni daman can rayu cikin farin ciki ba, don haka kada ki hanani komawa gun mahaliccina domin ina kyautata zaton insha Allah zan kasance a cikin farin ciki a can. Alawiyya bari ki ji dama ina cike da nadamar tafiyata ban ganki ba, banga mahaifinki ba naga wane irin yanayi kuke to alhamdulillah tunda ga dukkan alama baki da damuwa har