← Book details Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 133

Sashe 79

Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

akin ban san abin da ke hannunsa ba. Gidan aninsa na nufa wanda na fara sauka gidansa, ban oye masa komai ba na gaya mai, ya jajanta shi ma ya ara min wasu ku in ya ce maza na bar garin kuma insha Allah zan ga iyayena da yardar Allah. Ya ara da cewa nasan waye Yayana zai iya maida kisan da ya yi kanki bayan ya wula anta maki rayuwa don haka ki bar jahar nan baki aya Alawiyya Allah Ya shige maki gaba kan dukkan lamurranki." Haka na bi dare na tafi na kwana tasha motar asuba na bar Sokoto na shiga motar Katsina ina jin tashin hankali sosai a raina. Bayan na isa Katsina ne na sauka a hanyar shiga wani auye gab da Katsina, ban san kowa ba auyen kuma naji a raina nafi son zama auye fiye da cikin gari, domin na lura zama cikin garin yafi ko'ina tashin hankali, na karanci mutanen gari ba su da amana basu da taimako basu iya tausaya ma mutum haka ba su yin abu don Allah. Na jima zaune a wani aramin waje dana lura kamar kasuwar su gun. Na ji yunwa na je na siyi abinci na ci na koma inda nake zaune na sake zama, har dare ya yi ban gusa daga gun ba idan ba sallah da cin abinci na tashi yi ba. Wani matashin saurayi dake kula da Ni tunda na sauka mota ya iso inda nake zaune ya yi min sallama na amsa ya tambaye ni gidan wa nake nema ne. Na ce mai ba gidan kowa, ban san kowa ba na zo neman iyayena ne kawai ko zan dace cikinsu wani na garin. Ya dubeni sosai ya ce, "Kina nufin b tare suke da juna ba iyayen naki ba? To taya suka rabu da juna idan haka ne?" Haka kawai naji na yarda da shi don haka na ba shi labarina kaf tun daga farko har arshe. Jinjina kai ya yi, ya ce min, "Ki zo mu je na kai ki gidanmu wajen Mamana, ita ka ai ce sai Ni a gidan mahaifina ya rasu shekara biyu kenan da rasuwarsa." Na bi shi har gidansu ya yi ma Mamarsa bayani kamar yadda nayi mai, ta amince za ta zauna da Ni gidanta amma ta gayamin tana zuwa cikin garin Katsina gun aikatau a wani gida idan ba damuwa na dinga bin ta muna zuwa tare muna dawowa tare. Ban ja ba nace ma amince. Sunanta Zainab sunan yaronta Awwal sosai naji da in zama da su saboda ba tsangwama sun gaya ma jama'ar auyen daga garin an'uwanta na zo zan kwana biyu nan. Ranar da muka fara zuwa aikatau gidan sai da na razana ganin gidan mai kyan gaske ga shi babban gida, amma kuma Baba Zainab ta gayamin maigidan bai da iyali shi ka ai ne gidan, kuma abincin da ake a gidan sadaka yake ba da shi. Wata na guda ina zuwa aiki gidan rannan dai Baba Zainab ta kwanta bata lafiya sosai, muka kaita asibiti Ni da Nura aka ce mana musayar oda za ai mata, ga shi ba mu da ku in da aka nema na aikin. Hakan yasa na nufi gidan aikinmu da takardar asibitin aikin da za ai ma Baba Zainab da nufin neman taimako gun maigidan tunda halinsa ne bada taimakon. Ina zuwa cikin sa'ar gaske na iske motar gidan ban sha wahalar samun iso gunsa ba, da yake mun saba da sauran ma'aikatan gidan. Ina shiga da sallamata falon maigidan inda ban ta a shiga ba tunda nake zuwa gidan aiki sai Yau, yana zaune ya sadda kansa asa tamkar mai tunani na sake yin sallama a karo na biyu. ago kanshi ya kalle Ni da nufin amsa sallamar sai kuma ya tashi zumbur ya nufoni ya kama Ni ya dinga girgiza Ni yana cewa, "Da gaske ke ce a gabana Alawiyya! Alawiyya dama kina raye? Alawiyya ke ce gabana! Ya fashe da kuka ya rungume Ni sosai a jikinsa, maganarsa ta arshe tasa na gane mahaifina ne shi da naji ya ce, "Ina Fatima ina tsohuwa Alawiyya?" Kuka mai arfi ya wace min nima na rungume mahaifina sosai ina kukan farin cikin ganin mahaifina. Sai da mutane suka shigo jin kukana ya yi yawa duk suka ja birki ganina rungume jikin Alhaji muna kuka sosai. yar ya sake Ni ya zaunar da Ni ya dube su yana matu ar murna ya ce masu, "Yau Allah Ya amsa addu'a ta Ya bayyana min jinina iyata wadda na fito nema shekaru masu dama da suka wuce. Wannan ita ce Alawiyya iyar Fatima da nake baku labarin ta ace a garin Lagos." Nan da nan wajen aka auki murna ana hamdala ga Allah. Sai daga baya na dawo hayyacina na tuna da marar lafiya ta dake kwance asibiti, na ba Daddy takardar na ara da yi mai bayanin halin da take ciki. Ina zaune nayi ya yi waya nan take aka tura komai na aikin. Ni kuma na ba shi labarin abin da ya faru dani bayan rabuwarmu da tsohuwa. Tun daga nan ne ya saka Ni makaranta na cigaba da karatuna cikin kwanciyar hankali sai da na gama karatuna kaf sannan ya ce na shirya mu je garinsu wajen danginsa dama al awari ya yi ba zai koma ba sai ya gano iyarsa. Haka kuwa akai ya basu Awwal gida mai kyau ya ba shi jari mai kyau muka nufi garinsu Daddy na yi matu ar mamaki dana ga Kano muka nufa ban sake tsinkewa da lamarin ba sai da naga mun shiga cikin gidansu Inna Saude na kalli Daddy na zaro ido waje nace "Me za mu yi nan kuma Daddy? Nan ne gidan dana baka labarin an ri e Ni an azabtar dani sosai fa." Baice komai ba muka shiga cikin gidan duk ya sake lalacewa gidan ya koma kamar kango. Jikina a sanyaye muka shiga gidan kamar yadda na lura da jikin Babana ma a sanyaye yake. Tana zaune tsakar gida afarta tayi wani uban kumburi ba kyan gani duk ta rame ta fice hayyacinta kamar ba Inna Saude ba, Daddy ya yi sallama nikam biye nake da shi kawai na kasa ko bu e bakina. Ta zabura tai kamar ta mi e tsaye amma ba dama, saboda afarta da ba lafiya. Kuka ta saki da arfin gaske tana ambatar "Bello kai ne a gabana ashe kana raye dama?" Nan da nan sai ga jama'ar gidan sun cika gidan, kowa na ambatar Auta ya dawo ga Autan Inna Saude! Mamar Faisal kawai ta kula da Ni ta kuwa jawo ni tana cewa, "Kar dai ince Alawiyya ce ta dawo? Allah na gode maka da ka dawo wa yaron can da farin cikinsa." Sannan kallo ya dawo waje na kuma, Inna Saude ta dube ni tana kuka tace, "Da gaske Alawiyya ce ko wasa? Idan ita ce ina ta gano Auta na? Kai wannan yarinya ba dai zata rabu da jinina ba ashe? Na tsaneki na tsane ki amma kin li e min, kamar kaska. Sai a lokacin Daddy ya kama hannuna ya ri e ya dube su duka ya ce, "Ina Baba yake?" Aka auki kuka ana cewa Allah Ya yi mai rasuwa ai. Ya girgiza kan shi yana jin ciwon rashin mahaifinsa sosai har sai da ya kai da goge hawaye. yar ya ce, "Wannan ita ce iyata da na fita nema ta wajen Fatima dana haifa a Lagos." Sai kallo ya koma sama, nan da nan fuskar Maman Faisal ta sake washe wa ta ce, "Allah abin godiya, tabbas Alawiyya tai kama da kai amma ba damar fa a saboda Inna bata son ta." Na dube ta nace, "Mama ina Yaya Faisal ?" Tai murmushi tace, "Yana asibitin da yake aiki, kullum sai ya yi maganarki ko da yaushe bakinsa na kanki ba don na i amince mai ba da tuni ya bi duniya nemanki . Naji sanyi a raina domin duk tsawon rayuwar da nake da gaba in da nake ina ma ale da son Faisal a raina , kawai na oye abin ne saboda ban da ancin hakan, ban da gata da galihun da zan ce ina son shi balle har na saka a raina zan aure shi. Ko ba komai nasan cewa Kakarsa ta tsane Ni fiye da yadda ta tsani kowa a rayuwarta. Muna a haka ne ya dawo da gudu ya shigo yana ambatar sunana, cikin farin ciki muka dubi juna murna fal a zukatan mu. Da dare sai ga Yaya Mansur ya zo, ya yi murna sosai daya ganni, lokacin da ya ji labarin nice iyar Oga Bello ba aramin farin ciki ya sake shiga ba. Nan ne yake ban ha uri kan abin da ya dinga min, ya ce, ashe Inna Saude ce ta zuga matarsa har ta kai ta gun Malami akai min asiri aka saka min tsanarki a raina don haka ne duk sanda na ganki nake jin kamar na kashe kaina ko na kashe ki." Matar ma ta zo cike da kunya tai ta ban ha uri nace ba komai ya wuce ai. A lokacin ne Yaya Mansur ya dubi Daddy na ya ce, "Oga kaga ku en da nake turo ma kuwa na gareji ko? Ai Masha Allah ana samun alheri sosai bayan tafiyarka." Sai a lokacin ne ma Daddy ya tuna da wani account na shi na da ya manta da shi ma shi sam. Ya ce "Ai kuwa ban san kana turawa ba, domin hatta layina karya shi nayi ban sake bi takan wani account in banki ba balle na cire ku i kona saka wasu ba." Washegari kuwa aka sake bincikar account in sai ga ma udan ku e a ciki masu yawan gaske. Daddy ya fitar da su kaf ya ban ya ce, na nemi sana'a mai kyau, don haka na yanke shawarar zan gina asibiti mai kyau inda za a dinga taimakon marassa arfi tunda Yaya Faisal likita ne. Kwana biyu da zuwanmu Daddy ya zuba ku i ta hanyar abokin aikinsa aka fitar da Inna Saude asar waje akai mata aikin afarta sai dai dole sai da kujera take amfani bata iya tashi tsaye ta taka afarta kamar kowa. Bayan mun dawo ne
Chapter 79 · 0% Book details