Sashe 105
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ci da uwar haka nan a wahale ko gun kwana mai kyau ba su da shi haka suke kara zube a zauren gidan karuwan." Jiddah ta fashe da kuka jin abin da Alawiyyar tace mata, tabbas zata je da kanta ta ceci rayuwar yarinyar ko da ita ne Safiya ta tsira. Haka ita ta jima da yafe ma duk wanda ya cuce ta ranta fari tas ne kan kowa yanzu haka. Alawiyya ta dubi Jiddah tace, "Amma ina kika samo hujjar da kika bada a kotu kan A'isha?" Jiddah tai murmushi tace, "Yau kwana hu u kenan muna chat da Matashi sai naga ya yi status in wani pic wanda ya auki hankalina har nayi mai magana nace suwaye a jikin hoton daya ora a status insa? Shi ne yake gayamin abokinsa ne ke birthday party, to a jikin hotunan mata biyu ne rak don haka sai na sake tambayarsa matan fa suma duk abokanka ne Matashi? Sai ya ce min a'a aya yarinyar abokinsa mai birthday in ce gudar kuwa abokin wani ne daga abokan ya zo da ita gun bai san ta ba sai a hoton don bai je gun ba. Sai zuciyata ta dinga hasko min fuskar matar Abubakar duk da sau uku zance na ta a ganin hotonta amma don kauda kokonto sai na kira Abubakar nace ya turomin hoton matarsa, shi ne ya turomin a take na gane ita ce a jikin wancan hoton na abokin Matashi don haka sai na sake tambayarsa yana da kyakkyawar ala a da wanda ya zo da ita ne gun? Ya yi dariya ya ce ga alama dai tana cikin komarki don haka zan nemo maki labari kanta sosai amma dai ina fatan ba wani case bane mai girma ba kanta? Nai dariya nace ko ka an kawai sunanta dana abokin nake son ji ya wadatar ma da Ni. Ba a jima ba ya kira Ni ya ce min sunan ta A'isha shi kuma Abdul abokin kasuwancinta ne amma ban san wane kasuwanci bane suke. Nayi mai godiya na aje waya sai ga sa on number Abdul ya turomin kamar yasan abin da nake tunani kenan. Ban ata lokaci ba na auki lambar na saka a layina na aiki na kira shi ta jima tana ara bai auka ba sai kuma ya auka yana tambayar waye. Na gyara muryata sosai nace mai awar A'isha ce na kira ne na gaya mai gaskiya kanta idan ba damuwa. Ya yi jim sai kuma ya ce ina jinki amma ke ya sunanki? Ban oye mai sunana ba nace Jiddah sunana , ya ce min "Ina jinki to meke faruwa ne?" Nace ko kasan da cewar ta kashe ar aikinta ta ora wa mijinta laifin kuma yanzu haka tana shirin fallasa ala arka da ita a kotu saboda wani oyayyen dalili nata? Ya yi wani uban ashar ya ce, " arya take wallahi bari na kira Oganmu ki turomin account inki zan saka maki na kati na gode sosai da taimako." To sai na dasa alamar tambaya a gun, me yasa ya ru e don nace Aisha zata tona ala arsu? Waye Ogansu da zai kira? Me yasa ya ce zai min kyautar ku i don na taimake su? Nan da nan sai walwata ta fara nazari tana sa awa tana tacewa sai kawai na ora su a mazaunin masu laifi su duka don haka yanzu ina tare da masu laifi uku ne aya nasan laifinta kisan kai ne, su kuma biyun ne ban da tabbas kan nasu laifin amma ina da tabbacin masu laifi ne. Don haka sai na kira A'isha a waya nace mata, "Ina magana da A'isha matar Abubakar ce? Sai ban amsa da e ita ce lafiya nake nemanta? Ina na samu lambarta ? Nace mata na kira ki ne daga cibiyar bincike ta asa bisa jagorancin abokin har aklarki guda dana kama mai suna Abdul M Adam ina fatan kin san sunan koma ince mai sunan? Ta ja gwauran numfashi tace min tabbas tasan sunan tana jina. Na cigaba da ce mata, ki kwantar da hankalinki ba kece abar harina ba kamar yadda ba Abdul bane abin harinmu ba, idan kikai min yadda Abdul ya yi min tabbas ba zan sake kiranki ba, haka ba zan bari sunanki ya fita a jerin sunayen abokan cinikayyar ki ba. A'isha ina jiranki ki yi min bayanin irin har allar da kika san kuna yi sai ki ban sunan mutum guda cikin manyan dilolinku tare da bayani ka an to Ni kuma zan cire ki a list in wa anda za a kama. Cikin ikon Allah tai min bayanin wayoyi ne suke safara amma ita iyakarta fitar masu da ita asashen waje kawai saboda tana tare da babban mutum mai madafan iko wanda jirgin kansa garesa daga shi sai ita ke tafiya cikin jirgin sai mai tu in jirgin don haka suke amfani da damar suna bata wayar tana kaiwa duk asar da suka je ita da an majalisar. Ta ban sunan dilansu da arin bayanin inda take zuwa tana amsar wayar duk na na e a wayata. Bayan mun gama wayar na shirya kai tsaye na isa inda tai min kwatance na yi sa'a ba kowa gun sai masu gadi su biyu ban sha wahala ba gun shiga saboda guda ya sanni sosai ta silar wata shari'a da nayi mai kan wani yaro da aka sace mai nabi mai ha insa don haka cikin natsuwa suka bu e min ko'ina na shiga nayi bincike na samo sunayen duk masu hannu a cikin lamarin. Sannan a cikin ofishin dai naga hoton A'isha da shi an majalisar na auki hoton na tafi da shi kai tsaye gidan shi na sha atawa yana ciki kuwa na iske shi na zauna na fito da hoton A'isha da sauran gan in su na an kwangilar waya na fara da kora mai bayanin laifinsu da ara mai da cewar shi ne babban mai laifi wanda ke taimakawa ana fitar da wayar daga asar nan zuwa asashen waje don haka sunansa ne a farko kafin nasu, sannan na nuna mai hoton A'isha da Abubakar da hoton yaronsu na gaya mai yana bin matar aure matsayinsa na babban an siyasa a asar nan wanda idan wannan maganar ta fita zai rasa abubuwa da dama, irinsu siyasarsa, mutuncinsa, ba mamaki har da iyalansa ma. Hakan yasa ya ru e yake ce min wallahi bai sani ba, ya auka bata da aure sai a satin nan ne yake ganin abin da ke faruwa tana Shari'a da mijinta wai ya kashe mata ar aikinta bayan ya yi mata ciki, to da yake kin san mu an siyasa bamu da yadda tun ha uwarmu bada jimawa ba na sai mata wata sar ar zinari mai tsadar gaske na saka mata Camera a cikinta na saka mata nace kada ta sake ta cire ta sai zan sake mata wata, tunawa da hakan yasa na kunna Camerar don ganin meke faruwa a nan ne naga wannan abin da ya tada min hankali watau kisan da tai ma ar aikinta da kiran da taima mahaifiyarta. Ya ban aukar na kalla, na ri e na yi mai godiya nace sai mun ha u a kotu, duk da ya so na cire shi a lamarin nace ba zai yiyu ba saboda ya jima cikin manyan siyasar dake gur ata asar nan. To kin ji yadda akai na samu shaidun dana gabatar a wajen Al ali Yau." Abubakar ya sake yin godiya ya tafi cike da jin nauyin abin da yai ma Jiddah a baya Yau ga shi ita ce ta cece shi ta watar mai ha insa a lokacin da kowa ya yale shi ya juya mai baya. Prince ya dubi Princess insa ya ce, "Zan je gun Baba mu yi maganar zuwa kai ku in aurenmu don wallahi na gaji da wannan ja min ran da kike ko da yaushe so nake na ganki kusa da Ni ga Ni gaki." Alawiyya ta goya mai baya tace zata kira Baffa ta gaya mai yanzu kuwa gwara ayi hidimar a wuce gun haka nan. Da dare Jiddah ta gayama Hajjo ita ma ta kira Maman Jiddah ta gaya mata, tai ta addu'a tana arawa domin ta gane yaron da akace yana son Jiddah tabbas bai da kwaramniya da gani yana da hankali yasan me yake yi kuma don ba laifi yafi Deeni shekaru. Alawiyya ma ta kira Baffa ya ce sai ya ji daga bakin Jiddah sannan zai yadda don ba auren dole zai mata ba kuma ya zatai da karatun da take yi? Ya kira ta ya tambayeta ta amsa mai da cewa Mustapha ya amince ta cigaba da karatunta ba zai dakatar da ita ba ko bayan sun yi aure hakan yasa Baffan jin da i ya amince kuma sai dai ya ce ya tura can Jalingo shima zai je can su ha u da yayyen mahaifinta su amshi ku in auren. Ba haka ta so ba, so tai shi ya amsa ya zama waliyinta kawai a yale su tunda ba wanda yasan da zaman ta a duniyar daga su har mahaifin nata amma tunda ya ce haka sai ta amince sai dai umarnin arshe ne ya sosa mata rai da ya ce ta shirya ita da Alawiyya suje Jalingo ta gaida iyayenta kafin ai auren don ba lokaci za a saka ba mai tsawo. Ba yadda zatai haka ta amsa da to duk ba da i a asan zuciyarta. Ta shaidawa Prince da Hajjo da Alawiyya yadda su kai da Baffa su duka sun goyi bayan hakan don haka ita ka ai ce abin baima da i ba suka saka ranar tafiya Jalingo nan da kwanaki biyar. Sai kuma wata sabuwar fitina ta fita na yadda mata da dama ke sallama har gida suna gaya mata cewar karda ta sake ta auri Mustapha yadda take haka idan ta aure shi ta ci baya kuma sai tayi nadama tayi danasanin aurensa kowace mace tana kafa mata hujja da tarin auren da yayi a baya da yadda yanzu gidansa yake ba zaman lafiya wai bai kula da mata kashe mace yake komin diri da kyanta idan ya aureta aryar daga waje ne kawai tana shiga gidan ta