Sashe 5
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
su yake mata bata ara awa guda take fa awa. Inna Kande ta kiramu ni da Alawiyya tace, "Zan tafi garinmu amma zan gaya maku labarin yadda nake da ke Alawiyya (ta nuna Alawiyya da yatsa) ba don komai ba sai don yanayin rayuwa, ban san abin da gaba za tai ba. Alawiyya ki sani nice mazaunin Kakarki tabbas amma ba nice Kakarki ba sam! Ba Alawiyya ba hatta ni sai da na kalli Inna Kande, domin duk da arantata nasan lokacin da Innar Alawiyya ke zaune a gidansu kuma Inna take kiran Inna Kande, haka a gabansu tai aure ta auri wani soja suka tafi tare ta bar Alawiyya hannun Inna Kanden. Amma yau ga shi tana maganar wai ba ita ce Kakar ta ba... Inna Kande ta ci-gaba da cewa, "Mahaifiyarki na santa ne a motar da muka shigo na zuwa nan garin daga Gombe duk cikin motar ita ka ai ce budurwa domin duk mun manyanta mu tunda da niyyar bara muka fito daga gidajenmu zuwa Lagos tunda mun ji ance ana samun ku i da bara a Lagos. Tunda muka shigo motar da yake tafiyar dare ce na lura da yarinyar kuka take sam bata cikin hayyacinta sai ta jima tana kuka sai kuma ta koma tunani, duk inda aka tsaya don a ci abinci ita bata cin komai kuma bata siyen komai, sallah kawai take yi ta koma kurerarta tai ta kuka. Hakan yasa da aka tsaya cin abinci na ga kowa ya fice daga motar ban da ita na je nayi mata magana nace, "Baiwar Allah lafiya kike tafiya cikin uncin rayuwa ne? Shin me yasa ke tunda muka taso baki ci abinci ba kuka kawai kike da tunani?" Sai da ta goge hawayenta sannan tace min, "Ni in daga asar Chadi nake sunana Hajiya Fatima iyayena suna da arzi i dai-dai gwargwado don mu duka ba wanda bai ke aikin hajji ba a gidanmu ni ka ai ce mace a gidanmu sai Yayyena maza su hu u, muna rayuwa cikin kwanciyar hankali da wadata kwatsam aka fara rigimar boko haram a garin Chadi hakan yasa muka koma cikin Niger da zama mu duka, sai dai mun yi asarar dukiya mai yawan gaske wadda tasa muka dinga rayuwa a cikin talauci a Niger, a hakan watarana kwatsam mu ka ji mutane nata gudu suna ihun an kawo hari Niger in ma, mu ma muka bi ayarin an gudun hijira mu kabar Niger a jigace, sai dai lokacin da muka isa Nigeria kai tsaye Jigawa muka nufa, Allah da nashi ikon hatsari ya gitta mana a nan ne na rasa halina ban san inda suke ba, don ni dai na tsinci kaina a gadon asibiti ance mun kuma rarraba mutanen cikin motocin da sukai hatsarin akai, na yi iyakar nema na amma ban ga ko da mutum guda ba na ahalina shi ne akai min hanyar zuwa Lagos don zuwa nayi bara na samu abin ci da kaina." Ko da naji labarin Fatima sai tausayi ya yi masifar kama ni don haka nace ta kwantar da hankalinta idan mun sauka ni zan ri e ta kar ta saka damuwa a ranta, insha Allah watarana zata ha u da mutanen gidansu. Tun da muka iso Lagos na kama mana hayar gidan da muke ciki na fara fita bara sai ta hanani tace gwara mu nemi sana'a sai ya fi zuwa barar nan mutunci, na yarda da shawarar ta muka fara sarin biredi da lemu muna saidawa cikin ikon Allah kasuwar ta amshe mu kamar wasa a haka wani saurayi mai suna Bello yace yana son Fatima ta nuna bata amince ba da farko sai daga baya ta amince da shi domin ni kaina na yaba da halayensa yana sana'ar wankin mota ne a nan Lagos yace shi an asalin Kano ne neman ku i ya kawo shi nan Lagos. Cikin mutunci akai aure suka tare gidan hayar daya kama masu zamansu gwanin ban sha'awa, sai da Fatima ta shekara uku bata samu ciki ba sai a ta hu u ta samu cikinki, ta sha matu ar wahalar kwaikwan cikinki kamar ba za ta tashi ba har dai aka haife ki, kina da shekara guda dangin Bello suka bayyana basu yi wata-wata ba suka auke shi suka ce basu yarda da auren da ya yi ba don haka ko ar basu so, yana kuka yana komai ya saki Fatima saki guda ya ban amanar ki yace duk daren da ewa zai dawo ya tafi dake. Bayan tafiyar Bello Fatima ta shiga gararin rayuwa na kewa da soyayyar mijinta sosai domin Bello mutum ne har da rabin mutum, ya san yadda ake fita ha in iyali yadda ya kamata. Sai ga wani soja ya bayyana da arfinsa yana son Fatima ita kuma tace ta gama aure zata zauna ta kula da yarinyarta har abin da Allah Ya addara. Sojan nan yai ta naci yai ta wa amma Fatima ta kafe kan bakanta hakan yasa hankalin sojan tashi ya dinga yini gidanmu yana mata magiya yana neman na saka baki ta amince ya aureta arshe dai da naga mutane sun fara gulma na saka baki Fatima ta auri sojan nan mai suna Aliyu nan da nan aka saka biki wata guda yace kuma a nan zasu zauna sai bayan bukin da wata shida Fatima ta zo tana kuka take gaya min an sauya mai wajen aiki zuwa Taraba kuma yace da ita zai tafi. Babu yadda muka iya ni da ita dole muna ji muna gani na bar Fatima ta bi mijinta ke kuma aka bar min ke nan. Abin da yasa ba zan je da ke garinmu ba ban so ne ai maki wani kallo wanda bai kamata ba, ba shakka sai nafi kowa kukan mugun sunan da za a dinga jifanki da shi,sannan ina ji a jikina duk inda Babanki yake yana tafe gareki gwara ki zauna a nan kar ya zo baki nan, insha Allah ba zan jima ba zan dawo gareki Alawiyya." aramin kuka muka sha ba jin labarin mahaifiyar Alawiyya ba, amma duk da haka sai naji gwara ita tunda ko banza tasan asalinta ni fa? Ban san nawa asalin ba ko sunan iyayena ban sani ba. A ranar Inna Kande ta wuce garinsu ta bar Alawiyya gidanmu gun Iyami. Cikin sati guda Iyami ta fito da sabon salon azaba da musgunawa garemu wanda ya ninka wanda take min a baya. Ga shi Inna Kande shiru bata dawo ba har ta share wata uku ba ta ba labarinta . Watarana muna makaranta Sule ya zo cike da farin ciki yake shaida min ga Babana can ya zo. Ni da Alawiyya muka fice da gudu cike da farin cikin murnar Yau zan saka mahaifina a cikin idanuwana. Shin da gaske Jiddah zata ha u da mahaifinta kuwa? Me yasa Inna Kande bata dawo ba? Ina labarin mahaifin Alawiyya da mahaifiyarta? Da su da wasu amsar duk zaku ji su daga taku a kullum Haupha [7/3, 8:57 AM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa