Sashe 56
Hadin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
dake zube asa kallo da mamaki kwance kan fuskarta. Samun kanshi ya yi kiran sunanta kawai. Cikin sanyin muryarta ta gaida shi ta are da tambayar ko Bilkisu ta shigo?" Yasan daman sai dai hakan, haka kawai ba zata zo gidan ba don babu wadda suke magana sosai da ita a gidan. Ya dube ta cike da murmushi ya ce, "Bata shigo ba, amma dai shiga ki tambayi masu gidan." Ta yi an jim sai kuma tai murmushi ta juya tace, "Bar ta ma kawai daman a waya ta kira Ni na je gidanta kuma bata nan to nasan wani time nan gidan nake iske ta." Magana take amma sai wani annuri ke fita daga fuskarta, da gani ba ruwanta da wata damuwa domin fuskarta ma ta nuna bata cikin damuwa kwata-kwata. Ya bi bayanta da kallo yana cewa, "Allah ka mallaka min wannan yarinyar don na samu cikar burina da kwanciyar hankali kamar kowane magidanci." Ganin har ta kai ofar fita baki aya daga gidan sai kawai ya samu bakinsa da kwa a mata kira da arfi "JIDDAHH ! Cak ta ja ta tsaya ba tare data juyo ba, shi kuma sai ya sake kiran sunan nata cikin murya mai cike da damuwa, "JIDDAHH! Karaf sai a kunnen matansa, don haka kowacce ta zabura domin fitowa taga wacece maigidan ke kira haka ba ko shakkar cewa a cikin gidansa yake? To masu karatu me Mustapha zai ce ma Jiddah? Dama wasu abubuwan duk za ku ji su a page na gaba. Taku a kullum Haupha [8/22, 9:13 PM] Hauwa'u Salisu (Haupha): *HA IN ALLAH* Labari da rubutawa